← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 207

Sashe 110

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Imaan isn't free....* it's 300 Via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via 07087865788 to be included in the payment group....

Mujaheed na dawowa ya tadda Ammi xaune parlor, Ammi ta amsa sallamansa yace "Ta ci abinci ai" Ammi tace "Ta sha shayi daxu" yace "Tana ciki har ynxu?" mikewa Ammi tayi tace "Ehh tana ciki" bedroom din Imaan ta nufa, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, Ammi ta cire duvet din jikinta xuwa kafanta tace "Imaan" tashi xaune imaan tayi ganin Mujaheed ta daure fuska ta ja duvet din xuwa waist dinta, a hankali tace "Ammi na ma fara jin sauki" Ammi ta kallesa tace "Magunguna ka siyo mata?" Mujaheed ya girgixa kai yace "A'a injections ne, sai na shafa..." Ammi tace "Ta sha drugs a bar injections din anjima" kallonta yake sannan yace "Amma na yanxu ne alluran..." Imaan tace "Toh na ji sauki ai yaya" Bai kuma cewa komai ba sai kallonta da yyi ta gefen ido babu yabo bbu fallasa, Ammi tace "Ina lotion din tube din?" Mika mata ledan yayi ta amsa ta cire man xafi dake ciki, Mujaheed ya kara kallon Imaan da ta ki kallonsa, Juyawa yayi ya nufi kofa kamar baxai ce komai ba bayan ya bude kofar yace "Sai anjima" ba tare da Ammi ta juya ba tace "Allah ya kai mu" da kanta ta shiga shafa mata man xafin a kafafuwanta da bayanta, Tana yarfe hannu tace "Toh Ammi alluran fa, ni dai bana son Yaya ya min, Kuma har yanxu Ina jin joint pain din" Ammi tace "Anjima Dr Habib xai xo..." Ammi na gama shafa mata ta fita dakin imaan ta koma ta kwanta ta lumshe ido. Da yamma Imaan na xaune parlor pepper soup din naman ragon da Aunty ta kawo mata na gabanta ta kasa ci don gaba daya bata da appetite, har wani rama tayi kamar warce tayi sati ba lafiya, xuwa lkcn dai ta ji sauki sai rashin kwarin jiki don Dr Habib ya xo ya mata injections din da Mujaheed ya siyo daxu, Ammi ce ta fito parlon ta iso kusa da ita tace "Idan baxa ki ci ba ki kai kitchen ki rufe Imaan, ai ba dole bane" Imaan bata ce komai ba ta amshi wayar da Ammi ke mika mata, Sadeeq ne ke kira a wayar, ta kalli Ammi da ta juya xata koma daki sannan ta daga wayar ta kai kunne hade da masa sallama murya can kasa, daga daya bangaren ya amsa yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai tace "Sure Ina yini?" Yace "No, you sound sick ki gaya min baki da lafiya ne?" Cikin sanyin murya tace "Ae na ji sauki" Yace "Subhanallah, me ya sameki?" Ta girgixa kai tace "Kawai xaxxabi amma naji sauki sosai" ya d'an yi shiru sannan yace "Toh Allah ya kara lafiya, anjima xan xo in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen, I will call you idan na iso" tace "Toh" katse wayar tayi ta ajiye tana shan pepper soup din naman a hankali, Bude kofar parlorn aka yi Inna ta shigo ta tsaya tana kallonta tace "Ikon Allah, yanxu don kaddara ta fada ma wayar ki sai ki kwanta ciwo imaan?? anya kuwa xa ki yi tawakalli irin nawa? Kinsan irin asaran da nayi a rayuwar nan kuwa tun tasowata har ixuwa yanxu? To 6arin ciki hudu nayi a gidan mijina, na haifi 'yan biyu suka mutu rana daya, dakina ya ta6a konewa kurmus bbu abinda aka fitar da sai mafici, kishiyata ta ta6a turo min yan fashi suka kwace min jakata a titi Allah ya so bbu komai ciki sai naira daya, 'ya yana uku kacal a duniya, da ubanki, sai na Mujaheed sai kanwarsu Hadiza dake kasashen turai, to ban gode ma Allah ba? Me ya sameni, ke don kawai an dauke wayar da bai fi dubu hamsin ba idan ma ya kai sai ki sa ma kanki damuwa kiyi ta ciwo kamar wayar jaraba, in dai waya ce ni baxan bari ki sani a bakin duniya ba xan ba Ahmadu dubu goma ya cika ya siyo maki wata ba ruwana" Imaan dai bata ko kalleta ba balle ta tanka ta, Ammi ta fito ta gaida Inna, Inna ta amsa tace "Aisha yanxu baki nuna ma yarinyar nan karatun tawakali??" Ammi tace "Ciwonta ne fa ya tashi Inna" Inna tayi shiru tana kallonta, can tace "Dama imaan na da wani ciwo ne da ban sani ba?" Ammi tace "Ciwon nata kuma Inna kika manta?" Inna ta rike ha6a baki Bude tana kallon Ammi, can tace "Ni dai ba ruwana, ku je kuna fadan haka wani ya ji, dama banda rashin lafiya da kowa ke yi Imaan na da wani ciwo na daban ne ban sani ba?" Ammi tace "Toh ko jiya ma Abbanta yace wannan yaron da ke nemanta ya kamata a sanar masa laluranta tun yanxu" Gwalo ido Inna tayi ta saki salati tana tafe hannu ta xauna ta rike kai tace "Naga abinda ya isheni ni patuuu, wayyoo Allah duniya ta lalace" dagowa tayi tana kallon Ammi tace "Aisha da hankalin ku ke da Bukar kuwa? Dama Imaan na da wani ciwo ne ni da ban sani ba, ku dai ku dinga fadin gaskiya ku ji tsoron Allah, yaushe rabon da in ji Imaan bata da lafiya a gidan nan, Ni dai kada wanda ya laka ma jikata ciwo lafiyarta lau, waye baya xaxxabin maleria da thypho, to kada ma ku kuskura wani yaji wannan mugun xancen, ku dai ba kwa fadan alkhairi a gidan nan, Ni dai ba ruwana, yaushe rabon da tayi ciwo?? Ai yafi shekara biyar ba ma banda sharri irin naku...." Mikewa Inna tayi ta nufi kofa rai bace tana cewa "Mutane dai ba tsoron Allah, meye kuma wai a gaya ma yaron da ke nemanta laluranta kamar mai cutar AIDS... Ni dai ba ruwana" a bude tabar masu kofar bayan ta fita ta kara gaba, Ammi na kallon Imaan tace "You make sure you tell him everything about ur health condition, kar ki boye masa komai" Imaan ta sauke idonta kasa a hankali tace "Toh Ammi" Ammi ta xauna kan kujera a ranta tana jinjina halin inna, imaan ta kalleta tace "Ya ce xai xo anjima" Ammi tace "Toh sai ki gaya masa" biyar da few minutes Sadeeq ya kira Imaan ta wayar Ammi ya sanar mata yana waje, bayan ta gaya ma Ammi, Ammi tace "Toh kar ki dade dai a waje" "Toh" kawai imaan tace ta sa hijab dinta ta fita, tana isowa gun motar ya bude mata back seat yana kallonta yace "Shiga ki xauna" girgixa kai tayi tace "A'a..." Yace "No pls ki shiga kinga you are sick, you look so weak, bana son musu get in plss" shiru tayi bata ce komai ba, komawa gefe yyi ta shiga motar a hankali, yana kallonta yace "Kun je clinic kuwa?" Tace "A'a Dr dina ya xo ya min allura" ido ya kafeta da shi, hakan yasa ta sunkuyar da kanta yace "What's wrong with you?" Ba tare da ta dago ba tace "I woke up with headache, backache and joint pain... pains everywhere...." Ya d'an bude ido da mamaki ya cire glasses din idonsa yace "Yana maki haka ne dama?" Ta kallesa ta gyada masa kai gently, kasa daina kallonta yayi, murya can kasa yace "Are you... A sickler?" Girgixa masa kai tayi tana murmushin karfin hali tace "I am a carrier, I am carrying the trait" jin yyi shiru ta daga kai ta kallesa, tausayi taga karara a kwayar idanuwansa yana kallonta, underneath his breath yace "Ya Salam, a very rare case, Subhanallah" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, jingina yyi da motar ya rungume hannunsa yana kallon gate din shiga gidan looking so disturbed.

Umma ta share xufar da ke keto mata bayan ta gama sauraran bayanin mutumin gabanta, Hajiya Saude sai jinjina kai take, da kyar Umma na gyara xama tace "Toh malam yanxu meye abun yi.... A taimaka don Allah, wllh ji nake kamar xuciyata xata fashe, ko kuma in hadiye xuciyar, duk duniya bani da makiya da ya wuce yarinyar nan da uwarta, uwarta ta xalunce ni a rayuwa ta cuce ni, a dalilin uwarta na shiga gararin rayuwa malam ka taimakeni ko nawa ne ni xan biyaka wllh, Malam ka dubeni..." Mutumin dake xaune gabanta ya girgixa kai yace "Auren nan fa na gaya maki idan ba wani Ikon Allah ba sai an yi sa, mijinta ne d'an gidan attajirin babu tantama, sai dai kuma wani Ikon Allah, gashi nan na gani, gashi nagani har ranan bikin..." Hawaye ya kawo idon Umma tace "A dai duba malam a taimaka" Malam yace "Toh ga takarda sai ki rubuta abinda kike son ayi a ciki, amma fa banda kisa... don yarinyar na da tsawon rai haka ma Yaron sai dai kuma wani Ikon Allah, sannan kuma baxa a iya raba su ba.... yar ki kuma da kike son yaron ya fara nema kuma ba mijinta bane baxai taba yiwuwa ba, ba mijin yar ki bane yaron attajirin.... Sannan ina maki tuni surkarki a tsaye take kan yarinyar.... Tasirin aikinmu a kanta kamar ko da yaushe dai kalilan ne kema kin sani, Ki rubuta komai amma banda abubuwan da na lissafo maki a baya" Umma ta gyara xama tana share hawayen idonta ta amshi takardan da biro ta ajiye kasa ta fara rubutu.....

*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter 110 · 0% Book details