Sashe 30
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Good evening" Tace "Same" yace "Kin gane ni kuwa?" Kallonsa tayi bata ce komai ba tayi saurin sunkuyar da kanta ta shiga jera kayan basket din hannunta, yyi murmushi yana kallonta yace "Dama saboda kina tare da yayanki ne kika kafe ni da ido jiya a airport, yanxu kuma gashi kin kasa" juyawa tayi xata wuce yace "Wait" juyowa ta kuma yi, ya duka ya dau pads din da ta ajiye ya sa mata cikin basket din, still tayi a tsaye, ya wuce shi kuma gun counter, turo baki tayi ta bi sa da kallo ta gefen ido, bayan wasu sakwanni ta bi bayansa, bata yadda ta tsaya gun da xai biya nasa kudin wines din da ya siya ba a mall din, duk da mutanen da suka fi yawa a next counter din can ta tafi ta tsaya, ana xuwa kanta ta bude jaka xata fiddo atm card dinta taga ya mika masu nasa, juyawa tayi tana kallonsa ya saka masu pin dinsa a pos din, imaan dai ta kasa cewa komai, suka cire kudinsu suka mayar masa card dinsa ya nufi kofar fita, ledan kayanta ta amsa bayan an mata packaging, gabanta ya dinga faduwa har ta fita bata fatan ganinsa a waje, ai ko tsaye ta gansa jikin ride dinsa, da sauri ta dauke kai ta nufi bakin titi, ya bi bayanta har ya isa Inda take yace "In ji yau yaya bai ce ki taho shopping da kafa ba" bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yyi murmushi yace "Toh muje in ajiye ki a gida?" Kamar jira take tace "Nooo" daga haka ta tsayar da adaidaita fuskarta daure ta shiga, mai napep na tambayarta inda xata je tace "Mu je gaba" bin su yyi da kallo yana murmushi, sai bayan da suka yi nisa Imaan ta fada ma mai adaidaitan anguwar da xa ta. Suna isa ta kasa gane gidan, mai napep din yace "Toh kiyi tambaya mana" a hankali tace "To wa enda ban sani ba xan tambaya? Kamar fa wancan layin ne" ya juya yana kallonta yace "Duk fa kin sa na xagaye anguwar nan" Shiru tayi tana kallon layin da suke tsaye ciki banda haushin karnuka baka jin komai ko ina silent" mai napep din yace "Duk na kona mai na" yana fadin haka ya sakko don samun wanda xai ma tambaya duk da ba kowa silent layin sai mota daya dake tahowa, kana ganin layin kasan na manyan mutane ne sosai, ya kalleta yace "Ya kika ce sunan layin?" Fada masa tayi, mai motar na isowa inda suke ya tsaya ta dalilin tsaida shi da mai adai daitan yayi, Ya sauke glass mai adai daitan ya kalleta yace "Ya layin ma?" Ta hade rai don ta gaji da gaya masa sunan layin ta sakko daga napep din tana sake nanata masa, shiru tayi tana kallon mai motan kamar yanda shi ma ke kallonta, ya d'an yi murmushi yace "Ashe anguwar mu xa ki xo dama" bata ce komai ba ta wani hade rai, yace "Gidansu wa kike nema?" Ta sauke kanta kasa tace "Mariya Ahmad" Yace "I think wancan gidan ne" ya nuna mata gate din gidan, sae a sannan ta gane wajen, ta kallesa da kyar tace "Nagode" daga haka ta ciro dubu daya ta mika ma mai adai daitan ya bata dari biyar ta wuce xuwa gate din. Sosai Mariya taji ddin ganin Imaan ta rungumeta tace "Imaan a gidanmu, lallai yau za ayi ruwa da kankara, taya kika gane nan" imaan tayi murmushi tace "i just came to check on ur health daga shopping mall nake" Mariya tace "wllh naji sauki sosai, gobe in sha Allah xan je schl" Imaan tace "Toh Allah ya kara lafiya" Mariya zata dauko mata drinks a fridge tace "Aa ni fa baxan sha ba bana shan abu mai sanyi" Mariya tace "Ehh akwai mara sanyi ai" murmushi kawai imaan tayi Mariya ta tafi dauko mata mara sanyi, sosai Mariya ke son Imaan sai dai Imaan bata da saurin sabo kuma bata sakewa da mutane duk da kowa yasan mahaifin Mariya mai kudi ne sosai kuma sananne, har kawance ake son yi da ita, yawanci Mariyar ce ke xuwa gidansu Imaan dubata idan ta kwana biyu bata je schl ba, ita ko Imaan tun da suka je gidansu Mariyan duba yayarta da aka ma aiki tare da classmates dinsu bata sake komawa gidan ba sai yanxu, bayan boko islamiyyarsu ma daya kuma Mariya ma na da haxaka both schl da islamiyya tamkar Imaan din, Duk yanda imaan ta so tafiya Mariya ta ki yarda wai sai mamarta ta dawo sun gaisa, mahaifiyarta na dawowa kuwa ta kai Imaan har parlonta, Imaan ta duka kasa ta gaisheta da fara, matar mai kirki ta tarbe ta tana tambayarta mamarta, Imaan tayi murmushi tace "Tana gida" Aunty tace "Ya karatun fa" imaan tace "Alhmdllh" Aunty tace "Maa sha Allah sai ku yi ta dagewa, Allah ya bada sa'a kin ji" bude kofar dakin aka yi duk suka kalli kofar, xaro ido Imaan tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya mata kallo daya kafin yace komai Aunty tace "Har ka dawo Sadeeq" yace "Ehh na dawo, ina yini" tace "Lafiya lau" Mariya tace "ina yini ya Sadeeq" yace "Lafiya lau" Imaan ta sunkuyar da kanta, yana kallon Mariya yace "Bakuwa kika yi" Mariya tace "Eh yaya, classmate dita ce Imaan" Yace "Oh I see, sannu da xuwa bakuwa...." Imaan ta kasa dago kanta tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Daga haka ya juya ya fita, Imaan na kallon Mariya tace "Xan tafi Mariya" Turaren Humra mai yawa Aunty ta dibar ma Imaan da smart collections, Mariya ta amsar mata tana godiya, Imaan tayi mata godiya ta mike suka fita tare da Mariya Aunty na cewa ta gaida ummanta, Bedroom din Mariya Imaan ta shiga daukan jakarta da ledan shopping dinta, bayan ta dauka tana facing Mariya tace "Waye wannan da ya shigo Mariya?" Mariya tace "Wai ya Sadeeq? Yayana ne shi" Imaan ta xaro ido da sauri tace "Da gaske?" Mariya tace "Kin san sa ne?" Da sauri Imaan ta girgixa kai tace "A'a tambaya kawai nake" Mariya tace "He is my stepbrother, ga bangarensu can, kina shigowa compound part dinsu xa ki fara gani" Imaan tace "Ayya, ni dai xan wuce kar Ammi ta fara kirana" daga haka ta fita Mariya na biye da ita, a parlor suka tadda Aunty da Sadeeq, da fillanci Mama ke ce ma Sadeeq tunda fita xai yi ya daure ya ajiye Imaan ko bai kai ta har gida ba, Imaan tayi murmushi tace "Aunty ya bar shi xan hau napep" Mariya ta fashe da dariya, Aunty tayi murmushi tace "Ashe dai kina ji, kin bar kawar ki a baya, ba abinda ta iya sai shashanci" Imaan ta kalli Mariya da ta cinno baki tana murmushi, Sadeeq ya mike yace "Toh bari in ajiye ta" Imaan ta d'an xaro ido, Babu yanda ta iya, bata kuma yi ma mahaifiyar Mariya musu ba, suka fita tare da Mariya dake rike da ledan ta bayan Sadeeq ya fita parlorn, Aunty ta bi su har bakin kofa tana ce mata ta gaida ummanta, cikin motar suka tadda Sadeeq, Mariya ta bude mata front seat Imaan ta sunkuyar da kanta ta shiga ba don ta so ba, Mariya tace "Byee Friend sai mun hadu schl gobe, nagode sosai" murmushin karfin hali Imaan ta mata bata ce komai ba, Mariya na kallon Sadeeq da ya tada mota tace "Ya Siddiq drive my friend carefully fa" wani kallo yyi mata bai dai ce komai ba yyi horn, Mariya ta koma ciki tana dariya, har suka hau saman titi babu wanda yace komai cikinsu, bayan wani lkci yace "Wani anguwar xa ki?" Tana wasa da fingers din ta tace "Malali" bai ce komai ba, sai da suka kusa bayan kusan minti sha biyar sannan yace "Wani layin?" Ta gaya masa, daga nan kuma ta dinga nuna masa Inda xai bi har suka shigo gate din layinsu, dai dai gidan ta nuna masa yayi parking ya juya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba tana daukan ledanta dake kan kafarta tace "Nagode" yace "Welcm" daga haka ta bude motar ta fita ta rufe masa motarsa ya bi ta da kallo, Tsaye taga Mujaheed bakin gate da alamar fita xai yi don makullin motarsa na hannunsa, ya kalleta ya kalli motar ya sake kallonta da wani expression, ta wani daure fuska duk da faduwan da gabanta ke yi abinda yayi ma Maimoon ranan don an ajiye ta a mota ya fado mata a rai, turo baki tayi ganin ya ki matsawa daga gate din sai kallonta yake, ta raba ta gefen sa har tana bugesa ta shige gidan da sauri, juyowa yyi yana ci gaba da kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje xuwa part dinsu, sai da ta isa entrance din parlonsu ta tsaya ta juya tana kallonsa, har sannan kallonta yake, ta turo baki ta bude kofa ta shige ta kulle.🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟