Sashe 64
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo nan, to har kun shirya ne inna?" Inna tace "Haba dai sai kace wata yarinya, to me yyi min da baxa mu shirya ba, wai na ce ma Rukayya mahaukaciya, ke ki ji fa? to me ta min xan xageta banda abunsa ma dai, kawai daga ina mata gyara? Ni fa na yarje ma Ahmadu ya aureta wllh, baki ganta ba a lkcn yar siririya yanda kika ganki, kamar iska xai hure 'yar banxa ta fadi, gashi iyayenta basu da komai basu kuma ba wani ajiya ba, wani d'an akurkin gida fa gare ubanta a lkcn, to ni ban masu bakin ciki ba don xuciya ta fess mai kyau ne na yarda Ahmadu ya auro mana ita a haka, ke kinga wahalar da nayi da ita kuwa? Wllh kare baxai ci ba, gashi ba abinda ta iya a lkcn, har girki ni ke sa ta kan hanya ina koya mata, kishiyoyina su yi ta jin haushi yanda nake ji da ita bana son ko k'uda ya ta6ata har dai ta samu cikin wannan yaro Mujaheed, sai kin ga wahalar da nayi mata sbda laulayin da ta dinga yi ba kakkautawa, to ni duk ba wannan ba don nasan sakayya ta dai na gun Allah, to don kuma yanxu Rukayya ta xama abinda ta xama sai me xai dameni ni patuu? ga dai Amina na bina sau da kafa ga Aisha, ni dai abinda na sani shine Mujaheed ai xai yi auren, to nan xata d'an dana ko da dadi ko babu, abinda duk abinda ka shuka shi xa ka girba, tsaf xan karance ma yarinyar xaman da xata yi da ita, muna nan da ku sai an dinga xuwa daukata shari'a a mota...." Imaan har wani kwanciya tayi kan kujera tana dariya amma ba mai sauti ba, Umma da ta makale jikin kofa ta fita ta sa takalmanta, inna ta tabe baki tace "Wllh Mujaheed da gwiwowinsa bibbiyu ya durkusa ya dinga ban hakuri tun ban kai ga gaya ma ubansa ba, to tunda naga yyi nadama kawai sai na yafe masa don ba halinsa bane gaskiya bai taba juye ni a tsakiyar titi ba tunda mu ke" Imaan ta fashe da dariya tace "Jiya dai ya juye ki ai"