Sashe 199
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
abinci suna hira da Hajiya Bilki mai gyaran jiki, ta rufe abincin ta ajiye gefe ganinsa, Inna ta mike ta shimfida masa darduma tana masa sannu da xuwa, sauke kansa yyi kasa yana d'an murmushi ya ajiye ledan hannunsa ya xauna a hankali ya gaida su gaba daya, Mama Hadiza ta amsa tace "Sannu da xuwa Sadeeq..." yace "Kun xo lafiya mama?" Tace "Alhmdllh, ya shirye shirye?" Yace "Alhmdllh" Inna tace "Kaga yanxu kuwa ta fita taje raka wannan yarinya Maryam su gaisa da Ahmadu ko a kira maka ita a waya?" Yace "A'a kaya ne dama na kawo mata" Inna tace "Atoh ai shkkn sai in ajiye mata, kana dai cin abinci kuwa Bukar naga kai ma ka fige kamar amaryar taka" murmushi yyi ya sunkuyar da kansa yace "Ina ci Kaka" da damuwa Inna tace "Aa ku dai yi hakuri ku kwantar da hankalin ku ko kwa yi kyan gani da biki don Allah..." Shi dai bai ce komai ba, Bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya shigo da sallama, sanye yake cikin kananun kaya hannunsa rike da makullin mota, Tunda ya shigo Mama Hadiza ke kallonsa, yyi murmushi yana shafa kansa ya karasa cikin parlon, sai da ya fara ba ma Sadeeq hannu sannan ya xauna kusa da Mama Hadiza a hankali yace "Kun xo lafiya mama?" Ta rike ha6a tace "Kayi rashin lafiya ne ba a gaya min ba Muhd?" Yace "Ae naji sauki yanxu, kwanaki ne nayi rashin lafiya, tare da Maryam ku ka xo?" Inna dake kallonsa da kyau tace "Toh dai yau ga ni, ga Mujaheed, ga Hadiza da katuwa mai gyaran jiki, ga kuma yaron nan Sadeeq, sai Mujaheed ya ji tsoron Allah ya fito ya gaya ma kowa abinda na masa a parlon nan yanxun nan... Don ni ban san abinda na masa ba, idan Mujaheed bai saka min da abun kirki bautar da na masa ba yana yaro ai baxai guje ni ba yanxu da tsufa na, Hadiza yau kusan wata shidda kenan ban sa Mujaheed a ido ba, ba laifin tsaye balle na tsaye, ba lafin fari balle na baki, ko na kirasa baya dauka to ni dai gaskiya ya fito ya fadi abinda na masa ko in bar sa da Allah..." Ko kallonta Mujaheed bai yi ba sai juya makullin hannunsa yake, Hajiya Bilki dai sai dariya take kasa kasa, Mama Hadiza ta kasa cewa komai sai kallon Inna take ganin yanda ta ci serious ta tsuke fuska, Sadeeq dai idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, cikin rawar murya Inna tace "Ko don nace matarsa mayya ce ya kullace ni ban sani ba, toh banda haka me na ma Mujaheed, wllh ban masa komai ba, ko wani kaga xai mance da ni haka a rayuwa kai ba mai tare min bane balle kai da kanka, gashi duk ka wani fige kamar kazar Hausa kuma ace yarinya ba mayya bace.... Ni dai ba ruwana" Mujaheed na kallon Mama Hadiza yace "Ba ku taho da su El-Ameen ba?" Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Xa su taho tare da babansu xuwa jibi, xai xo daurin auren shi ma" Inna ta bude baki tace "Toh shi Mujaheed ba mutum bane da ya ki xuwa nasa daurin auren?" Mama Hadiza tayi murmushi tace "Inna kar ki manta Imaan ita kadaice gun Yaya, banda haka ma da ba lallai nima in xo ba tunda yaushe na xo bikin Mujaheed, to wannan dalilin yasa babansu Maryam ma xai xo daurin auren nata...." Inna ta tabe baki tace "Ku dai ku dinga tsoron Allah, ku dinga abu saboda Allah, wato shi Mujaheed bai cancanci a xo nasa ba sai na Imaan, to ubansa ya sha Mama ya bar ma ubanta, duk babu wani banbanci" dariya kawai Mama Hadiza tayi bata dai ce mata komai ba, shi dai Sadeeq idonsa na kan wayarsa, Maryam ce ta fara shigowa parlon Sadeeq ta fara gani ta gaishesa da fara'a, ya amsa yana murmushi yace "Kun xo lafiya Maryam?" Tace "Alhmdllh Dr, ya shirye shirye" yace "Lafiya lau" ta wara ido ganin Mujaheed tace "Ya M.A..." Imaan ta shigo parlon hannunta rike da fruit salad da Ammi ta bata ta kawo ma Mama Hadiza, ganin Mujaheed xaune parlon ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, daga kai yyi ya kalleta, bata san lkcn da ta ajiye bowl din hannunta ta nufesa da sauri ta xauna kusa da shi tana kallonsa ta wara ido tace "Yaya..." Ya shafa kansa kamar baxai ce komai ba sai kuma ya d'an ja hancinta yace "Kanwar Yaya..." dariya ya bata, ganin yanda take dariya yyi murmushi yana kallonta, rungumesa tayi a hankali tace "I missed you" Kallonsu kawai Sadeeq yake, Mama Hadiza ta dinga ma Imaan wani kallo amma imaan ko sanin tana yi bata yi ba, Inna tayi tagumi ta rasa abun cewa sai yan idanuwa, Can a fusace tace "Ke dai gantalalliya ce wllh, katuwa da ke ki fada jikin mutumi wai Yaya, yanxu fa ke matar wani ne, da ba don mijin naki ya san alakar ki da Mujaheed ba me kike tunanin xai faru yanxu? Kawai mata daga shigowa ki dare kan mutumi kice Yaya???" Da sauri Imaan ta sake Mujaheed ta juyo, sai a nan suka yi ido hudu da Sadeeq, sosai gabanta ya fadi ta xamo kasa tana kallonsa, Mama Hadiza dai ta kasa cewa komai amma gaba daya kunya ya isheta, Inna tace "Toh waye kuma Yaya Allah na tuba ke ba yarinya ba yanxu, mutumi yyi aurensa kema xa ki yi naki, ai kuma sai a hakura haka sai 'ya yanku su ci gaba da xumuncin, ni dai ban taba ganin haka ba...." Sadeeq ya d'an yi murmushi ya mike yace "Kaka ni xan koma yanxu" Inna tace "Au to baka sha ko ruwa ba Bukar" yace "Ae daga gida nake Kaka" Inna tace "Toh shikenan Allah maka albarka, kuma ka dinga cin abinci kaji" yace "In sha Allah" Yana kallon Mama Hadiza yyi kasa da kai yace "Mama xan koma, Allah huce gajiya" Mama Hadiza tace "Toh ka gaida mutan gidan Sadeeq na gode kwarai" kofa ya nufa, Inna na kallon Imaan tace "Ae sai ki tashi kusa da mutumin nan ki tafi ki sallami mijin ki koh" Kin tashi Imaan tayi, Mama Hadiza na ganin Sadeeq ya fita tace "Baxa ki tashi ki fita ba shashashar yarinya, kawai ki kama ki rungume mutum a gabansa sbda baki da natsuwa" a fusace Inna tace "A'a ke kuma bana son fadan rashin gaskiya, wa gareta da xata rungume banda Mujaheed din, a haka suka taso abun su dama can, shi ma mijin ai ya sani, ko ce maki aka yi bai sani ba, sarai ya san yayanta ne bata da kamarsa a duniya ko kun haifa mata wani yayan ne ban da shi Mujaheed din?? Ni bana son fadan rashin gaskiya wllh, kinsan yaushe rabon mu sa Mujaheed din a ido ne? kuma ta gansa baxata nuna farin cikinta ba, kullum sai ta min xancensa don ma Ina gwaleta kamar bai dameni ba alhalin kullum da daddare sai nayi mafarkinsa, kawai mata daga xuwa ki hau yar mutane" Hajiya Bilki ta dinga dariya tana kallon Inna, a hankali Imaan ta mike ta bi bayan Sadeeq Mujaheed ya bi ta da ido.