← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 207

Sashe 121

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganeta baxan ce mata ban gane ta ba, tun daxu nake durkushe a nan nake aiki babu mai taimakona, baki ji bayana ba kamar ya balle in huta...." Maryam ta hade rai ta shige parlonta, Imaan tace "Maryam ce fa Inna" Inna tace "Waye kuma Maryam" Dariya kawai Imaan take tana kallon Inna, Inna tace "ita ce ta xama kamar zal6e?" Imaan ta xauna a balcony din tana dariya, Inna ta tabe baki tace "Ku dai baku son gaskiya a gidan nan, yanxu da ba don wannan yar albarkan Maimoon ta gaya min a boye ba daxu da baxan ma san Hadiza xata xo gidan nan ba, Toh kuma kya taho min da yarinya tsigi tsigi kice Maryam, Yar da aka haifa hannuna ce aka ce maki baxan gane ba, ni fa na mata wankan farko kuma a gabana aka yayeta..." Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" Fitowa Maryam tayi daga parlon ta yi wucewarta, Inna ta bi ta da kallo ta kyabe baki tace "Ubansu dai ya cuce su ya hallaka su, ya kwashe su ya tafi kasar tsinannu yayi kaka gida, toh tana ma jin hausar kuwa" Imaan dai ta kasa cewa komai sai dariya take, Inna ta gama dauraye bakin tap din ta mike ta shige cikin parlonta tana cewa "Bukar dai ya haifi jaraba, ba don naka naka bane ai ni bana bari a cuci Bulasawa a lika masa ke ba, to banda haka ni sa'ar uwarki ce xaki xauna bakin kofa kina babbaka min dariya kamar mahaukaciya?? ita ma Hadizar dama kada ta kuskura ta xo min nan xan koreta tunda bata maida ni bakin komai ba, banda haka ta kamo hanya rai kwakwai mutu kwakwai baxata gaya min ba in mata addu'a, wannan ba shawarar kowa bace illa wannan mutumi Bukar don shi ne me irin wannan tunanin na marasu nutsuwa, Amadu baya haka" mikewa Imaan tayi ta bar wajen ta koma part din su... Bayan magrib tare Abba suka tafi gun Inna da Maryam, Inna na xaune parlon tare da Mama Hadiza da Mujaheed, Inna na ganin Maryam ta washe baki tace "Yanxu nake rokon Mujaheed ya tashi ya nemo min ke don tun saukan ku bamu hadu ba kin xo daxu ina gurje bakin pampo ke kuma baki jira in gama ba kika yi wucewar ki" Maryam ta xauna ta gaisheta babu walwala, Inna ta amsa da fara'a tace "Kun sha hanya, sai kawai naga kin kusa kamo imaan a tsayi..." Maryam dai bata tanka ta ba, Mama Hadiza sai murmushi take, Abba ya gaida Inna ta amsa tace "Ae gwara da ba a gaya min suna hanya ba Ahmadu da baccin kirki ma ni baxan yi ba, amma da na gansu kamar daga sama ai yafi ko" Abba na murmushi yace "Gaskiya ne" Mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon Maryam ta bi bayansa, a jere suke tafiya tace "Ya M.A kaga abinda Inna ta min daxu kamar bata taba ganina ba" Dariya Mujaheed yyi yace "Xata maki fiye da haka ma, so take it off ur mind plss haka nan take, ya karatu?" tace "Alhmdllh...." Ya kalleta yace "Hope baki kula samari sai kin gama karatun" tayi dariya tace "Kai ya M.A, bayan ga Imaan ma tana da saurayi, ta ma ce min xai yi birthday soon and his frnds will be celebrating it for him, wai in bata shawarar abinda xata basa" Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, can yace "When tace maki birthday din?" Ta wara ido tace "I didn't ask her, mun ma gaisa da shi a waya yace xai xo gobe ya gaisheni, his voice is cute..." Tana murmushi ta kare maganar, Shiru yyi bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya a hankali tana biye da shi, Xaro ido tayi tace "Wait... Am I even suppose to tell you this??" Yar dariya yyi yace "Me yasa kika ce haka?" Tace "Naga irin kamar you are surprise.... Kila ma baka san tana da saurayin ba ni ce na maka revealing koh?" yace "Yes.. boye mana take, Amma kar fa ki ce mata kin gaya min she won't be happy" Maryam ta marairaice tace "Toh nima kar ka mata magana about it she won't be happy with me...." Yace "Sure I won't" suna isa part din su Imaan tace "Am spending the night here, ka ce ma su Maimoon, Ummi da Rahma su xo muyi hira plss" yace "Ohk xan gaya masu" daga haka ya wuce, tafiya yake amma gaba daya abinda Maryam ta gaya masa ne ke yawo a ransa... Wani murmushi yyi ya shiga sashin su.Washegari da safe Imaan na kumbure kumbure ta gama shirin islamiyya bayan Ammi tace baxata xauna mata a gida ba, Maryam ta sami Ammi a kitchen a hankali tace "Ammi don Allah ki barta kar ta je yau, I don't have anybody to gist with idan ta tafi fa" Ammi tace "Ga kakarki can ki je ku yi hiran mana" da sauri Maryam tace "A'a ni bana son hirarta kawai tayi ta xagin mutane, nima ta fara xagina" Ammi tayi murmushi tace "She is ur grandma dai" Maryam tace "Sure, pls Ammi kin yarda kar taje?" Ammi tace "Karfe sha biyu xa su tashi ai, kuma sauka xa su yi soon Maryam, imaan ko shakkar fashi bata yi shi sa nayi forcing dinta ta wuce" Maryam tace "Ohk then, Allah ya kai mu 12 din" daga haka ta fita kitchen din, Imaan ta fito daki bayan ta dauko jakarta ta nufi kitchen ta tsaya bakin kofa kamar xata yi kuka tace "Ammi na tafi" Ammi tace "Breakfast din fa?" Ta girgixa kai tace "Ni sai na dawo" Ammi tace "Oho cikin ki" Juyawa imaan tayi ta fita, Maryam ta rakata xuwa parking space, dai dai fitowar Mujaheed da makullin mota a hannunsa, Maryam tayi masa murmushi tace "Good morning ya M.A" ba tare da ya kalleta ba yace "Morning Maryam kin tashi lafiya?" Tace "Sure.. Alhmdllh" Imaan dai tuni ta dauke kai, Maryam tace "Aiki xaka fita ya M.A" yace "Noo, sai da yamma nake fita aiki during weekends" Tace "That's nyc... Do you need my company?" Ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Sure... if that will suit you" ta kalli Imaan tace "Alryt sweetheart xan raka Ya M.A, ayi karatu da kyau a islamiyya" imaan ta kalleta tace "Ohk bye" tana fadin haka ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, da sauri ta dauke kai, Ya bude motarsa ya shiga ya tada, Maryam ta xaga ta shiga gaba. Ko da Imaan ta dawo daga Islamiyya karfe sha biyu Maryam bata dawo ba, Imaan na kallon Ammi tace "Ammi wai tun da safe har yanxu Maryam bata dawo ba?" Ammi tace "Ehh wai sun fita tare da Mujaheed koh?" Imaan ta tabe baki ta mike ta wuce dakinta. Bayan azahar tana gama cin lunch ta tafi bangaren Inna, Inna na xaune parlor tare da Mama Hadiza, Imaan ta gaida small mum din nata sannan ta gaida Inna da ta tsuke fuska, Inna ta amsa tace "Ke kiji Hadiza da wani mummunan xance Imaan, wai duk abinda xa ayi na bikin Mujaheed mai kyau ko mara kyau in saka ido kar in yi magana, Saboda ita bata da tsoron Allah, bata son gaskiya xuciyarta ta kekashe, to me mutum xai min wanda Allah bai min ba" Mama Hadiza tace "Ni dai ki fahimce ni Inna, idan ba mu fada maki gaskiya ba kina da mai gaya maki ne, ba girman ki bane komai kika gani ki tanka a tafi da ke a baki, Haba inna" Inna tayi mitsi mitsi da ido tace "An dade ba a tafi da ni bakin ba, ni da bikin jikana ki dinga gaya min maganan banxa, ke kinsan wahalan da nayi da Mujaheed kuwa, wllh wllh ko Rukayya bata da iko da shi a yanxu, mutumin da yasa na dinga fada da jama'ah a anguwa yau ya kwale d'an wancan gobe ya danne d'an wancan, da ma Allah ya rufa min asiri bai sa an min duka a anguwar ba har Allah ya raba ni da anguwar? ke kinsan sau nawa na shirya na tafi makarantar su Mujaheed fada da malamai kuwa... Kishiyoyina kuwa duk min dambatu da su a kan Mujaheed, Sannan ace wai in xama kurma a bikinsa kamar uwata tace min je ki kya gani? To wllh karya ake...." Mama Hadiza tace "Ba ace ki xama kurma ba amma ba komai xa ki tanka ba, ba komai xaki shishshige ma ba, Allah na tuba Rukayyar da ma in don ta nata ne bata son a shiga lamarin bikin, ji fa tasan don bikin takanas na xo kasar nan amma tun sannu da xuwan da ta min jiya a bangarensu ban sake ganinta ba, ace kuma tayi farin ciki da xuwana...." Inna ta kunduma ma Umma xagi tace "Ai ba ita ke aurar da d'a ba nice nan mai aurar da Mujaheed kar ki ji komai, mu xuba kuma a gani, Allah dai ya kai mu ranan da rai da lafiya, sai dai mu kwashi yan kallo da ita a bikin nan idan kuma bata yi hankali ba dama baxata kwana gidan nan ba ranan bikin" Mama Hadiza ta tabe baki bata dai ce komai ba, Inna tace "Haka kawai, inyi wahala da shi a dinga gaya min maganan banxa" Imaan dai murmushi kawai take tana danna wayar hannunta, sallama aka yi bakin kofar parlon, Imaan ta juya da sauri jin muryan Sadeeq, Inna ta mike daga xaunen da take da sauri tana washe baki tace "A'ahhh sannu da xuwa Bukar, kai ne da ranan nan... Bisimillah shigo abun ka... Ba kowa daga ni sai Hadiza da Imaan" da gudu imaan ta shige dakin Inna, Sadeeq ya shigo parlon kansa a kasa, Inna na washe hakora ta kalli Mama Hadiza dake xaune kan kujera tace "Ke tashi ki basa waje ya xauna mana, sirkin ku ne" Sadeeq ya bude ido yace "A'a kaka ga waje ai" Bai jira cewarta ba ya xauna saman carpet dake shimfide, Inna ta nufi fridge ta bude ta kwaso ruwa uku da malt uku ta taho, Mama Hadiza dai sai bin ta take da kallo cike da takaici, Sadeeq na kallonta a hankali
Chapter 121 · 0% Book details