← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 207

Sashe 127

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788Inna na kallon Imaan da ta xauna kusa da ita cike da damuwa tace "Toh ba gashi kin fito sak mutum ba yau kin sa gyale, amma da kullum da hijabi xulum xulum kamar matar ladani..." Ta rasulu dake ta bin jama'ah da kallo tace "Toh wai ni abinda na kasa ganewa a nan shine... uwar amaryar da danginta basu san kin xo nan bane ban ga an xo gaishe ki ba har yanxu, dubi fa yanda muke xaune kamar gantalallu marasu makabuli babu wanda ya bi ta kan mu, an san ke kika raini Mujaheed tun yana tsumma kuwa, Kai duniya dai ta lalace ni ta rasulu" Inna ta tabe baki tace "Shine nake ta kallon ikon Allah, sai yawo suke mana da gwalagwalai kamar barayi babu wanda ya xo ya durkusa nan yace Sannu Inna... ya taro? To Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana na 'yan baya, shi kuma Mujaheed din dubi yanda ya wani yi tsamo tsamo da shi kusa da amaryar babu walwala kamar dai wanda aka tilasta ya xo casun..." Imaan tayi murmushi ta kalli Mujaheed sannan ta kalli Inna tace "Toh ke ina ruwanki..." Inna tace "A'a da ruwana mana, ni ba karamin aikina bane in tashi inje samesa yanxu in ji ko lafiya..." Ta rasulu tace "Maxa je ki, nima naga rashin walwalan yayi yawa sai yake kawai yake, kamar wanda aka ma dole, anya ma auren soyayya xai yi kuwa" Inna ta tabe baki ta mike tace "Toh wani ya rainan min shi da baxan sani ba idan yana cikin damuwa ko akasin haka, sarai nasan sa ciki da bai, da abinda ke damunsa a xuciyarsa xaman da yayi a nan" Kutsawa ta dinga yi cikin mutane wanda yaki matsawa dama hankadesa take tana cewa "Yau naga bala'i mutane an xo cin shinkafa da yar kaza kamar mayu, an ki bani hanya..." Kallonta aka dinga yi ana bata hanya tace "Banda jaraba ko wacce ta fiddo kayanta na karkashin akwati ta saka ta xo mana nan tana jiran shinkafa da salaq da kaza, ohh yunwa ta yi yawa a duniya" A haka har ta isa inda amarya da ango ke xaune, wata kawar amarya ce tsaye tana bada history din amarya sai wani yauki take tana jujjuya idanuwanta, cool music sai tashi yake mutane na mata tafi... sake baki Inna tayi tana kallon yarinyar, can dai ta karasa inda take tsaye ta d'an ta6o ta a kafada, gaba daya wa enda suka san Inna suka xaro ido suna kallon ikon Allah, juyowa budurwar tayi tana kallon inna murmushi dauke fuskarta, Inna ta matsa kusa da ita sosai murya can kasa tace "Wani tsinannan telan kika ba kayan ki ya lalata maki haka saboda rashin tsoron Allah, duk duwaiwuka a waje?" Ba karamin tsorata da girgixa Inna tayi ba tana xare ido jin muryarta ya kauraye makeken hall din gaba daya ta cikin speakers, Hall ya rikice da dariya, Mujaheed ya sunkuyar da kansa, Umma ta kasa motsi inda take tsaye sai hadiye abu take da kyar, Imaan ta hade kai da table tana dariya kasa kasa, su Maimoon ma suna ta dariya daga inda suke xaune, Aunty da Ammi da Mama Hadiza dama tagumi suka yi suna kallon Inna da tayi tsamo tsamo a gaban hall sai kallon jama'ah dake dariya take, gaba daya yan uwan amarya wani kallo suka dinga yi ma inna, ita kuwa mai bada history ta ji kamar ta nutse gashi an ki daina dariya a hall, Safeenah ta wani hade rai tana kallon Mujaheed tace "Haba Mujaheed dama gate pass din wa enda suka kamata da wanda basu kamata ba ku ka dinga raba ma suka shigo mana nan, dubi wannan tsohuwar me ya kawota nan ta ina ta samu pass din shigowa har xata kunyata aminiyata cikin mutane, kasan Yar gidan wacece ita kuwa??" Gently Mujaheed yace "Watch ur words..." A fusace tace "Don't tell me that Mujaheed, how dare the old woman insult my friend that way, yar gidan governor ce fa tsaye a wajen..." Calmly yace "Ko yar gidan uban wacece, ke kawarki ce, to ni kuma grandmum dita ce a kusa da ita, so you dare not look into my face and say nonsense about her" Wani kallo Safeenah ta dinga ma Inna da ta tabe baki cikin sanyin murya tace "Ba lafiya, dama ba a sirri a nan, daga magana kuma sai sipikoki su dauka su min terere...." Juyawa tayi ta kalli yarinyar da ta kasa cewa komai har sannan tace "Ki dai maida masa ya gyara maki ai kudi kika biya ya cuce ki ya maki wannan dinkin" daga haka ta bar wajen ta tafi gun Mujaheed, har sannan Safeenah bata daina bin ta da wani irin kallo ba har ta iso inda suke tana kallon Mujaheed tana washe baki tace "Wannan ce amaryar Mujaheed" Safeenah ta dauke kai fuska daure, Inna ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Toh Allah ya bada xaman lafiya, ta dai sha gwalagwalai maa sha Allah" Hajiyan Marafa ce tsaye kan Umma tana bala'i a mugun fusace tana cewa "Haba Rukayya ke baki ga irin manyan mutanen da muke ba gate pass bane xa ku ba wannan tsohuwa mai wanke wanke ta shigo mana hall tana shirme tana kunyata mutane, kin san yar gidan wacece tsaye a wajen take magana kuwa?? reputation dina da na 'ya ta kuke son 6atawa ko meye hakan?" Umma dai sai hakuri take bata a rikice tana cewa "Wllh ban san wanda ya bata pass din ba, don Allah kiyi hakuri Hajiya, wllh ban san daga inda ta taho ba...." A mugun fusace Hajiyan Marafa tace "Toh maxa ki sa a fitar da ita daga hall din nan tun wuri kada ayi mummunan abu a nan, maxa a fita da ita kada in sa masu gadi su fitar min da ita ta tsiya" Umma sai cewa take kiyi hakuri Hajiya xa ta tafi yanxun nan kuwa, ae ba ku kadai ta kunyata ba har mu wllh, ban san wanda ya bata pass ta shigo ba ni ban ma santa ba, haka irin tsoffin nan suke idan suka ga ana taro su shigo cikin jama'ah" Hajiyan Marafa ta juya fuu ta wuce tana cewa "Maxa ta bar nan kada in sa masu gadi su ja ta su fitar..." Inna na kallon Mujaheed tace "Toh naga duk baka da walwala lafiya kuwa, ko baka ci abinci bne?" Ya girgixa kai yace "Ba komai, ki koma kiyi xaman ki" Inna tace "Toh madallah sai dai har yanxu mu dai babu abinci babu labarinsa, ga ta rasulu can ma sai hamma take" Tana magana ta dau tsadadden drink dake gabansu tace "Ko in dau wannan" yace "Dauka" dauka tayi tace "Toh shikenan, Allah dai yasa ba mai halin uwarka xaka auro mana ba dai" daga haka tayi wucewarta, Safeenah ta bi ta da wani harara tana kyabe baki, Umma ta rasa yanda xata yi ta fitar da Inna a hall din cikin lumana, duk ta rikice taje can taje nan, Inna na dawowa xuwa seat dinta ta dinga cewa mutane "To dai duk wanda ya ci abu yyi hakuri ya saka gwangwani ko kwalin a jakarsa kada mu bata masu waje da kazanta mu cuce su...." A haka har ta koma gunta, ta ajiye ma ta rasulu drink din daya ta ajiye daya gabanta tace "Ma rage xafi..." Ta dau drink din ta fara budewa, Inna ta xauna tace "Naje na samesa amma kinsan ko gaisheni amaryar bata yi ba, ni dai ban kulata ba, ba ruwana kada in kunyata kai na cikin jama'ah ga ni babba, taro yayi taro in je inyi magana in kunyata Mujaheed din ma gaba daya, bakina a leko na juyo na dawo ai ana tare...." Ta rasulu tace "Gwara da baki kulata ba kam, ki bari sai an kaita dakin nata ki shirya kije ki mata tatas ki gaya mata yanda kike da Mujaheed" Inna tace "Ehh dama ai dole in sanar mata wahalan da nayi da shi don ta gane matsayina a wajensa, ana kai ta da washegari dama Imaan xan ce ta rakani inje in karanta mata yanda muke da shi" Umma ce ta taho gun Inna da sauri tana haki tace "Inna yanxu aka kirani wai ruwa ya cika parlon ki sai kwararowa waje yake ga kofar a rufe, ko dai kin bar pampon bayan gidan ki a bude baki sani ba?" Inna ta mike ta rafka uban salati a rude tace "Hadiza ta cuce ni ita ta shiga bandakin karshe tayi fitsari, shikenan ruwa ya shanye min gida na shiga uku na lalace ni patuu, ga dukiyoyi irinsu kujeru, tv, gado carpet, fridge duk a ciki" ta rasulu dake xabga salatin ita ma ta mike tace "Na shiga uku ni ta rasulu, jakata na dakin nima har da kudi dubu biyu, yanxu me xan ce ma 'ya yana daga xuwa biki ambaliya ya rutsa da ni??" Umma tace "Toh bari in sa driver ya maxa ya maida ku gidan gaskiya, don ruwa aka ce duk ya cika tsakar gida" Ko sauraranta Inna bata yi ba ta fice da gudu tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una ambaliyan ruwa a gidana a kira min yan kwana kwana, ga gudunmawar dubu hamsin da Bulasawa ya bani a dakin...." ta rasulu na biye da ita a baya ita ma da gudu tana salati, Mama Hadiza da su Aunty na ganin Inna ta fita da gudu suka taho gun Umma dake tsaye suna tambayarta me ya faru, Umma tayi wani dariya tace "Wai fa kudin da xata yi liki ta mance a gida shine wannan saurin wai driver xai maida ta gida" Kasa cewa komai Mama Hadiza da su Aunty suka yi, Umma tace "Allah dai ya kyauta, lamarin Inna ae sai ita" daga haka ta wuce ta bar su wajen a tsaye, Imaan dai na xaune an barta da jakunkuna irin na tsofaffi, Maryam ce ta taho gun Imaan da sauri tace "Ke maimakon mu bi su Inna mu je mu yi abinda xa mu yi kika bari suka wuce" Imaan ta xaro ido tace "Ae kuwa, toh kawai mu yi kamar xa mu bi su da jakar su sai mu wuce" Maryam tace "Toh dauko mu tafi" Imaan ta dau jakar Inna ta mika ma Maryam na ta rasulu, kallon Mujaheed tayi taga idonsa na kansu, ta dauke kai tana xaro ido tace "Maryam kin san Yaya kallonmu yake" Maryam ta kallesa taga still kallonsu yake duk da liki da mutane suka taru wajen suke masa da Safeenah, Maryam ta koma ta xauna tace "He is suspecting us Seriously, kin san me xai faru?" Imaan ta girgixa kai, Safeenah ta bude jakarta ta ciro new note din naira dari dari tace "Gashi ki tafi kiyi masu spraying, kafin ki dawo na fita gun mota sai ki sameni da sauri, but before then Bari in canxa seat" Imaan ta nufi can gaban hall din hannunta rike da tulin kudin, su Maimoon, Ummi, Rahma da wasu kawayen Safeenah da yan uwanta da suka sha gold sai cashewa wa suke da wakar jarumar mata da ya cike hall din Lol.... Safeenah ma na tsaye tana rawa gently tana kallon Mujaheed with love, shi ko yana tsaye kamar statue yana jujjuya wayar hannunsa, dance floor din kuwa banda dubu dubu babu abinda xaka gani a kasa sae few five hundred notes, Imaan ta isa kusa da su ta ki yarda ta kallesa tana kallon Safeenah dake rawa ta fara mata likin a hankali, kallon cikin ido Safeenah ke mata haka kawai Imaan taji gabanta na faduwa bata sake yarda sun hada ido ba tana ci gaba da yi mata likin kudin, Bandir din dubu daddaya Mujaheed ya ciro ya nufi gun kanninsa da suka dage sai cashewa suke barin Maimoon, Ya fara manna masu da daddaya da daddaya, Safeenah ta bi sa da wani harara ganin kanninsa kawai yake lika ma, Imaan na lura da abinda tayi haka yasa taki lika mata kudin hannunta gaba daya ta koma gun su Maimoon ta fara masu likin, Mama Hadiza ta xo ita ma tana ma su Maimoon da Imaan likin kamar su kadai ne a wajen tana murmushi, facing din Imaan Mujaheed yyi yana kallonta ya fara xuba mata one thousand naira note din a hankali, kasa kallonsa ta yi kanta a kasa, can kuma a hankali ta fara lika masa na hannunta, Mama Hadiza ta juyo ta dinga xuba masu na hannunta ita ma, Aunty ma haka, da abokansa gaba daya da suka cika wajen lkci daya, Safeenah ta ji kmr ta nutse don ba kowa wajenta sae flowing gown din jikinta, duk aka koma ana ma Mujaheed da Imaan liki, Umma sai xare ido take tana kallon ikon Allah, kowa ya xo sai ya fara ma Imaan da Mujaheed liki kamar ita ce amaryar, don wasu ko noticing Safeenar ma basu yi ba balle su san ba ita suke ma likin ba, Imaan dai ta dawo amarya a wajen duk kunya ya isheta.... Sai da Mujaheed ya manna ma Imaan gaba daya note din hannunsa yana kallonta, ita dai sai kokarin barin wajen take amma saboda yanda aka kewayesu ta rasa hanyar fita, da kyar dai ta samu ta lallaba ta fita taron xuciyarta na bugawa, tana kallon inda Maryam ke xaune taga har ta fita, da sauri ta nufi door din fita hall din ta fice fittt, Maryam na ganinta ta dallo mata fitilar motar ya Yusuf, xata tafi gun motar taji an fixgota, ihu tayi a tsorace ta juya xuciyarta na bugawa.....
Chapter 127 · 0% Book details