← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 207

Sashe 45

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... 😃😃Gidan wani cin abinci Mujaheed yyi parking, yace "Ki jira in fito..." da sauri tace "Nima ba abinda na ci wllh" ya kashe wayarsa kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "meat pie daya ya ishe ki" kafin tace komai ya bude motar xai fita, da sauri tace "Yaya amma fa ban sa takalmi ba" da sauri ya kalli kafarta, yace "Good kinga sai ki jira ni in ci abinci in fito" Ta fashe da kuka tace "Wllh haka xan fito, ni fa ba abinda na ci tun da rana sai furan nan da ka tsammin" ya hade rai yace "Ki fito ki ja min kallo cikin mutane" ta marairaice tace "Yaya to mu je ka siya min ko bathroom slippers ne" yace "Ki dai jira yanxu xan gama cin abincin in fito" Bude motar tayi ta fito, ya xaro ido yana kallonta, Xata xagayo inda yake ya mata tsawa yace "Tsaya nan kar ki xo min nan" ta turo baki tana kallon sa yace "Dama ki tsaya sai na shiga sannan ki shigo, kuma ki nemi can nesa da ni ki xauna xan sa a kai maki abincin can" a hankali tace "Toh" Daga haka ya shiga yana waigota don tabbatar da ta bar distance sosai tsakanin su, Yana xaunawa sai ga ta ta shigo, ya wani hade rai ya dauke kai, tabe baki tayi ta nemi nesa da shi ta xauna ba tare da ta damu da kallon da ake mata cikin eatry din ba, jollof rice da half chicken yasa aka kawo masa da five alive drink sai bottle water, yana kallon waitress din yace "Ae kuna da meat pie koh?" Tace "Ehh har da burger da pizza with sausage roll duk akwai" yace "Good kinga wancan matar dake xaune at that far end?" Waitress din ta kalli inda yake nunawa ganin imaan tace "Ehh na ganta" yace "Ki kai mata meat pie daya da table water, ni xan biya bill din" tace "Ohk" daga haka ta wuce ta dau meat pie din da table water ta nufi gun Imaan tana ajiye mata a gabanta imaan ta kalli Mujaheed da ya dauke kai yana cin abincin gabansa, waitress din ta juya ta wuce, satan kallonta Mujaheed yyi suna hada ido ya juya kujerar sa yayi backing dinta yana murmushi yana cin abincin sa, Imaan ta dinga kallon sa amma ya ki juyowa, bayan kusan minti uku ya sake juyawa a hankali, kawai ganinta yayi a gabansa tana kallon sa kamar xata yi kuka, da sauri ya fara kalle kallen eatry din ya ga kallonsu kawai ake, ya xaro ido kafin yace komai ta ajiye masa meat pie da ruwan a gabansa ta jawo plate din abincin da drink ta dauka ta koma inda take ta xauna ta fara ci, Mujaheed bai ce komai ba ya dauke kansa, bayan kusan minti goma ya mike ya tafi ya biya kudin abincin da snack sannan ya dawo ya dau meat pie din da ruwa yana satan kallonta ita ma kallonsa take, mamaki ya cika sa ganin har ta kusan cinye shinkafar nama kuwa ta ma gama da shi, ya dauke kai ya nufi kofar fita, imaan ta mike da sauri ta dau sauran five alive din ta bi bayansa, a tare suka iso gun motar, ya bude driver seat ya shiga ita ma ta shiga gaba yace "Fita ki koma ki cinye abincin" tayi yar dariya tace "Dama fa nasan wucewa xaka yi ka bar ni shi sa nake ta kallon ka" ya hade rai yace "Fita nace" tace "Ai na koshi baka ga na cinye naman ba" tada motar yayi ya bar eatry din, bayan sun hau saman titi yace "Xan maida ki gida yanxu, wllh kika kuskura kika ce nasan komai a kan furan inna Allah xan sa ki kuka" da mamaki tace "Kai ina xa ka yanxu?" Yace "Gidana" ta fashe da kuka tace "Toh shine ni xaka maida ni gida, wllh kar ma ka kai ni don baxan fita daga motar nan ba" ya buda ido yace "Toh ina xan kai ki?" Ta turo baki tace "Mu tafi gidan ka tare" ya gyada kai yace "Tunda ke mahaukaciya ce ni ba mahaukaci bane" ta kallesa tace "Toh da ba ina xuwa ba" ya jefa mata wani kallo yace "Da ba yanxu bane" Shiru tayi ganin ya dau hanyar gida ta kamo sa tace "Don Allah yaya kar ka maida ni gida yanxu, wllh Ammi xata iya dukana don dama tace kar in dauko mata magana" yace "Toh ina xan kai ki?" Hawaye ta fara yi, yayi murmushi yace "Gobe baxa ki dauke ma tsohuwa furanta ba, ni dama ba ruwana" ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, bayan few minutes yace "Abinda xai faru yanxu ina maida ki gida sai ki shige dakin Anty da sauri, ki kwana a can" ta dago tana goge hawayen idonta tace "Don Abba ya gani ko, kasan Ummi xata ce ma Abba ina nan" Ya daga kafada yace "Ae shi Abba baxai doke ki ba, fada kuma baya nuna wa a jikin mutum" parking yyi yace "Oya fitar min a mota sai da safe" wasu hawaye na xubo mata ta bude motar ta fita tana kallon sa tace "Duk abinda ya faru daga farko har karshe xan gaya ma Abba baxan boye masa komai ba, tare muka shanye furan kuma kai ka sa na shiga dakin Inna in dauko saboda ta xuba maka kadan" daga haka ta bar wajen da sauri tana kuka ya bi ta da kallo baki bude, tuni ta shige gate ta dinga rabe rabe har ta isa parking space din su Yusuf, a haka har ta shige parlour rufin asirinta ba kowa da gudu ta wuce dakin Anty, Anty dake xaune gaban madubi ta bude baki tana kallonta, Saman gadonta Imaan ta hau ta rufa da duvet, Anty tayi murmushi tace "Ina Mujaheed din?" Imaan ta cire duvet din ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Yace baxai dawo ba yau kuma wllh Anty shi yasa in dauko mata furanta sai ma kinga abinda ya tsammin duk ya shanye sauran" hawaye cike idonta take maganan, Anty tayi dariya tace "Ae ko kun sha jaraba yau, don har yanxu Abba da Ammi na can ana ba Inna hakuri, nima gajiya nayi na taho" Imaan ta turo baki ta koma ta rufe kanta da duvet. Washegari Saturday Imaan na xaune gaban madubin Anty tana shafa mai don har tayi wanka, Anty kuma na xaune kan darduma hannunta rike da hisnul Muslim aka bude kofar dakin, Abba ne tsaye bakin kofar, Imaan ta kusa faduwa saboda rudewa, Abba ya kalli Anty yace "Amina amma baki ce min yarinyar nan na nan ba" Anty tace "Ni ma har na yi bacci na ganta jiya da daddare" Abba ya kalli Imaan yace "Ki sameni parlona yanxu" kamar xata yi kuka tace "Abba to shi yaya fa?" Dakuwa Abba yyi mata yace "Stupid girl, yayan banxa ai duk xa ku gane kuran ku yau" daga haka ya juya ya fita, Imaan ta fashe da kuka tana kallon Anty tace "Kinga ni kadai xa a ma fada yaya ya gudu koh" Anty tace "Ni dai ba kin sani nayi karya ba, maxa fita ki tafi ki samesa ba ruwana" da kyar Imaan ta bar dakin sanye da Hijab dinta, Abba dake parlonsa ya mike ganinta yace "Mu je" bin sa tayi tana goge hawayen idonta suka nufa part din inna, tun daga nesa suka hango Mujaheed yana share mata frontage, Yana ganin Abba ya mike tsaye, Ya gaida Abba da ladabi Abba ya masa banxa ya shiga parlon inna, inna ta fito kitchen tace "Ahmadu ne da sassafe haka" Abba ya xauna ya gaisheta ta amsa, ganin Imaan ta hade rai tace "Ya xaka shigo min da ita parlor Ahmadu, ni da dai ta tsaya daga bakin kofa, tsoronta ma nake ji wllh" Abba ya kalli Imaan yace "Koma can" komawa tayi bakin kofar ta tsaya, Abba yace "Shi yaushe Mujaheed din ya xo nan?" Inna ta xauna tace "Ko minti biyar ba ayi ba, Ashe jiya na shiga alhakin yaron bai ma san me ke faruwa ba baya gidan yana asibiti, sai yanxu da ya shigo nake basa labarin abinda yarinyar ta min, ya taya ni jimami sosai yayi mamaki ainun, shine ya ga xan share waje ya amshi tsintsiyar yake sharewa yanxu duk da dai nasan ba sharuwa wajen xai yi ba amma ai dai ya fi babu" Abba ya sunkuyar da kai yana murmushi, Inna tace "Yanda yarinyar nan ta sa na kwana da yunwa jiya gaskiya Ahmadu idan ba a dau mataki ba xan tafi inje duk inda Allah yayi ko kasar waje ne kuwa, don na gaji da cutata da take, jiya mun dade muna magana da Bukar a waya a kan yarinyar tasa yana ta bani hakuri ni dai ban hakura ba" imaan ta fashe da kuka tace "Wllh yaya ne yasa in dauko masa kwanon furan fa" Abba ya kalli inna da ta bude baki tana kallonta, yace "Ke sai kika yarda da yace maki bai san me ke faruwa ba dama?" A hankali Mujaheed ya ajiye tsintsiyar hannunsa xai bar wajen Abba yace "Don't try that, come in now" Inna ta mike tace "Toh amma ko gaskiya Ahmadu ka haifi abinda ya fi karfin ka, ka haifi tashin duniya, yanxu duk dadin bakin da ya shigo ya min da sa hannunsa a sace min fura da nono, Haba da walakin goro a miya, dama wani Mujaheed ne xai amshi tsintsiya ya min shara, ko da kuwa aiki xai kasheni baxai yi ba wllh, wato xuwa yayi ya yaudare ni ya cuce ni to akwai hisabi ai, ni dama nasan ina imaan ta koyi wani sata idan ba sa ta aka yi ba, ilai ga maganata nan, kuma wllh kaji rantsuwar musulmi ko, to baxan yadda ba sai sun san yanda suka yi aka min furata mai kyau mai kamshi da tsafta irin tawa sannan a siyo min kindirmo mai
Chapter 45 · 0% Book details