Sashe 72
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
man xafinta a kafa Inna ta shigo ba ko sallama, Ammi ta mike tace "Sannu da xuwa inna" inna tace "Aa ba wani sannu da xuwa, yanxu Aisha a kan yar ki xa ki sa Mujaheed gaba kina masifa inda kike shiga ba nan kike fita ba kamar xa ki make sa, to ma ina ruwanki kina 6are xa ki shiga harkan 'yan uwa, ubansa fa wan ubanta ne uwa daya uba daya, to ke kuma a wa Allah na tuba, Ba kunya ba tsoron Allah xaki shiga fadan 'yan uwa, abinda ma ina xaune parlon d'an shafa kafar nata yyi ya fita shine munafukar nan ta dinga ihu tana min birgima ni kuma na koreta, ni dai ba ruwana kar ki lalata mana xumunci gaskiya, ko xane Imaan Mujaheed yyi yau kanwarsa ce kuma yana da ikon yin haka, to banda shi da ya tsaya mata kan lalurorinta shekarun baya da ba sai dai ta mutu ba, ni dai a dinga jin tsoron Allah, gashi nan dai albarkacin Bukar bai kula ki ba, toh ni dai kada a sake sa min jika a baki ba ruwana, banda ma bifillatani agwai da wauta ina shi ina shiga sha'anin family" tana kai wa nan ta fice a parlon, Ammi ta rufe man hannunta tana kallon Imaan tace "Wllh na sake ganin ki xaune inda Mujaheed yake a gidan nan sai na kusa sumar da ke" Imaan dai ba ta ce komai ba. Misalin sha daya Imaan ta mike daga kwancen da take da kyar xata shiga daki ta kwanta, duk jikinta ciwo yake mata ga wani xafi da jikin yayi, Ammi dake xaune parlon tace "Kina ji na" imaan ta juyo tana kallonta, Ammi tace "Dama gobe kice masu baki jin dadi baxa ki iya tafiyar ba, don babu inda xa a dake, ina xaman xamana a kwaso min wahala a bar ni da jiyya" Imaan tayi shiru tana kallonta, can tace "Toh" daga haka ta wuce cikin daki ta kwanta. Washegari karfe tara su Maimoon, Ummi da Rahma suka gama shirin su na tafiya, kaya kala biyu ko wannensu ya dauka Abba duk ya basu kudin kashewa, Yana kallon Ummi yace "Tafi ki duba ko mamana ta gama shirya wa" Ummi ta fita parlon xuwa part din su Imaan, Ammi ta fito daga bedroom din Imaan kenan rike da cup din shayi don da mugun xaxxabi ta tashi safiyar ranan, Ummi ta shigo parlon da sallama, gaisheta tayi tace "Abba yace Imaan ta fito" Ammi tace "Ae kam yau ta tashi babu lafiya" Ummi na komawa ta fada ma Abba haka, Abba yace "Subhanallah ba lafiya kuma" mikewa yayi ya fita, a dai dai part din su Imaan ya hadu da Mujaheed ya dawo daga bangaren inna, Abba yace "Imaan wai bata da lafiya yau" Mujaheed yace "Subhanallah" Abba yace "Let me check on her" Mujaheed bai ce komai ba kamar ya juya yayi tafiyarsa sai kuma dai ya bi bayan Abba, Ammi suka gaisa da Abba, Mujaheed yayi kasa da kai ya gaisheta, Ita ma ba tare da ta kallesa ba ta amsa bbu yabo bbu fallasa, Abba yace "Toh ya jikin nata?" Ammi tace "Toh da sauki, tun jiya dama bata jin dadi" Abba yace "Ikon Allah" Ammi tace "Tana ciki" Abba ya nufi dakin nata, Mujaheed ya bi bayansa kansa a kasa, kwance suka sameta cikin duvet amma still sai shivering take, Abba ya cire duvet din yace "Sannu mamana" Bude idanuwanta da suka rina tayi a hankali, Abba yace "Ina ke maki ciwo" girgixa masa kai kawai tayi, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali ya kai hannunsa jikinta, Abba na kallonsa yace "Ko dai a tafi asibiti" Mujaheed xai yi magana aka bude kofar dakin inna ta shigo a rikice tace "Ahaf, ni dama nasan xa a rina, ba ayi hauri ba ma ya aka kare balle anyi, wllh Ahmadu da ya tattakure ya tattakure kawai sai gani nayi ya haureta"