← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 207

Sashe 155

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

albarka, tashi ki raka sa ke" Kudi ya fiddo aljihunsa dubu ashirin ya ajiye kasa kan carpet da ya tashi yace "Kaka tukuicin girkin, naji dadi kuma nagode" Inna tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni... Bukar dai baya gajiya, abincin ma sai an bada tukuici?? Toh Allah maka albarka, ni dai na gode baxan tsaya ina jayayya da kai ba kamar karamar yarinya, nagode" Yana murmushi ya nufi kofa, Inna na kallon Imaan ta hade rai tace "Ke dai sususu ce wllh, baxa ki tashi ki rakasa ba toh" imaan ta turo baki ta mike ta bi bayansa, Inna na kallon Mujaheed tace "Toh kullum aikin kenan fa wllh, sai ya ajiye min damin kudi haka kafin ya fita har na rasa yanda xan yi da kudi a dakin nan, ni fa ya fi min mutane da dama a duniyar nan don yasan abinda ya kamata, ku ma dai ku ji tsoron Allah ku dinga koyi da shi..." Mikewa Mujaheed yyi ya fice daga parlon. Tsaye Mujaheed ya tadda su kusa da flower sai wani sunkuyar da kai imaan take shi ko sai kallonta yake kamar lkcn ya fara ganinta, kamar mai counting steps dinsa ya dinga tafiyar don basu lura da shi ba, murya can kasa Sadeeq yace "Plss ki kalleni dear let me feel relieved, I've missed you alot, but staying far away from you and just listening to ur voice is d best to me" Ita dai ta kasa dago kanta, a hankali ya kamo hannunta ta dago manyan idanuwanta tana kallonsa, yyi murmushin sa mai tsuma xuciyar wanda ya gani cikin cool voice dinsa yace "I love you Imaan, I am always dreaming to be with you by my side as my wife.... I wish xa ki ga yanda na kagu ki xama matata.... I just can't..." Sai kuma yyi shiru ya lumshe ido, Imaan tayi still ganin Mujaheed da ya tsaya yana kallonsu, da sauri ta xame hannunta daga na Sadeeq, Mujaheed ya dauke kai ya ci gaba da tafiya gently, Ko Sadeeq bai juya ba yasan shi ne, kuma ya ki kallonsa, har sae da Mujaheed yyi nisa sannan Sadeeq ya bi sa da wani kallo, can ya gyada kai smiling, Imaan tace "Xan je in kwanta na gaji" yace "Sure dear, hope cramps din yyi sauki?" Xaro ido tayi sai kuma ta rufe fuska da sauri, ya dinga kallonta yana murmushi, ya kai bakinsa kusa da kunnenta a hankali yace "A day will come da xaki san kunya baxae amfane ki ba" turo baki tayi har sannan ta ki kallonsa, murya can kasa yace "I want just a favor from you... And don't deny me plss" tana kallonsa tace "Na me?" Yana murmushi yace "I will text it to you idan na shiga mota ynxu coz I am not ready to dig u out from underground now" xaro ido tayi tana kallonsa, ya hade rai yace "And if you deny me, I won't be happy imaan" Bai jira cewarta ba ya fara tafiya yace "Expect the text now, gobe I might come in the evening in sha Allah" ta bi sa da kallo har yyi nisa sannan ta juya a sanyaye ta koma part din Inna. Bayan magrib imaan na xaune dakin Inna bayan ta gama shirin bacci xata kwanta ta tuna wayarta da text din da Sadeeq yace xai turo mata tun da rana, mikewa tayi da sauri ta dau Hijab ta saka ta fito parlor tasan ma kila yana ta kiranta, Inna dake xaune parlon tana cin abinci ganin ta nufi kofa ta tabe baki tace "In ji baki mance komai naki a dakina ba Imaan" imaan tace "Xan dawo fa, wayata xan je in dauko a gida" cike da damuwa Inna tace "Me kuma xa ki dawo ki min?? Tun safe fa kike nan" Imaan bata saurareta ba ta fita parlon, daga nisa ta hango mutum na tahowa kamar Yusuf kamar kuma Mujaheed, duk da Yusuf ta san ya daina xuwa part din Inna sai tare da Abba, Tsayawa tayi har sai da ya iso kusa da haske taga Mujaheed ne, turo baki tayi ta juya da sauri ta koma part din Inna, Inna da ta bar abincin da take ci ta tafi tana share dakinta ta daga kai tana kallonta tace "Naga jaraba... Har kin dawo??" Imaan ta bi ta gefenta ta shige dakin tana cewa "Ko ba Yaya bane" Inna ta ci gaba da sharanta tace "Toh dama ki kakkabe min xanin gadona ki gyara gadon fess ni ba gantalalliya bace, ba haka nake barin dakina ba in kwana tare da wari" Inna ta mike ganin Mujaheed tace "Wannan shine anyi ba ayi ba, yanxu kayi auren ma baxa mu sarara ba Mujaheed kullum kai ta mana sintiri a gida, ba daxu da rana ka xo ba to me kuma ya dawo da kai, ko akwai ajiyar ka a parlon nan ne baka dauke ba har yanxu" Bai tanka ta ba ya nufi kofar dakin ya bude ta bi sa da kallo baki bude, imaan ta koma can karshen gado kamar xata yi kuka tana kallonsa, Ya wani mugun daure fuska yace "You had better keep on running away from me coz wllh wlh am promising you this... if I should get hold of you I won't take it likely with you.... I will seriously deal with you" a fusace Inna tace "Naga abinda ya isheni, don Allah Mujaheed ka rufa mana asiri, me ta maka kake kunduma mata xagi haka, yarinyar da kamar baxata yi ba daxu Allah ya rufa mana asiri Bulasawa ya rufa mana ya mata allura ya bata magani taji sauki shine yanxu xaka xo kana xaginta kana nuna ta da yatsa kana gaya mata maganganu marasu dadin ji, to ni dai ba ruwana ka tafi ka ba mu waje, ni na ta6a jin inda aka aurar da mutum kuma yyi ta sintirin dawowa gida kamar dai da ajiyarsa da ya mance bai dauka ba, ni dai gaskiya na gaji da kai kar ka sake xuwa min, tunda kayi auren ka kayi xamanka a gidanka ka bar min jikata ta sarara...." Kawai Inna gani tayi ya shige dakin ta fasa ihu tana kwala ma Ahmadu kira iya karfinta, ba kuma wanda xai ce ba wani mugun abun ta gani ba, Imaan ma duk ta rude xata gudu bandaki ya fixgota kawai sai ji tayi xabga mata mari mai lafiya, ta rike fuskarta a gigice, inna na ganin haka ta fice da gudu xuwa waje tana kiran Abba, Mujaheed na kallonta da idonsa da suka kada cikin harshen turanci yace "Muharramin ki ne mutumin nan da kika mika masa hannun ki ya kama, dama iskancin da ku ke yi da shi kenan, yana tsaye kusa da ke kamar xai shige jikin ki kina jin dadi koh? To wllh yanxun nan xan je in sami daddynki in sanar masa komai" a rikice imaan ta rikosa ta dinga basa hakuri tana cewa "Yaya ni bani nace ya rike ni ba, don Allah kayi hakuri baxan kara ba wllh, don Allah kayi hakuri" sosai xuciyarsa ke tafarfasa yana kallonta, ta hade hannayenta hawaye na sakko mata tace "Don Allah kayi hakuri baxan kara ba da gaske Yaya" tana fadin haka ta boye fuskarta a jikinsa tana kuka, har ransa yake jin kukan nata, Bai san lkcn da ya jawota jikinsa ba cikin sanyin murya yace "That's very wrong imaan, I've told you times without numbers... that guy is just here to ruin ur life, to cause you heartbreaks, he is after ur body... He is..." Kasa ci gaba yyi don sosai ransa ke tafarfasa, imaan dai sai sauke ajiyar xuciya take tana kuka a hankali bata ce komai ba, nan ko ko kiris bata yrda da abinda Yayan nata ke fada ba don ita tasan Sadeeq na sonta kamar yanda ita ma take sonsa fiye da xaton mai karatu, dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta da ya rine murya can kasa yace "For my sake xa ki rabu da shi plss Imaan?" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Ni dai ina son sa Yaya, kuma ai aurena xai yi..." Kallonta Mujaheed yake ko kiftawa babu xuciyarsa na bugawa, da kyar tace "Kayi hakuri plss Yaya, da gaske Ina son sa, but in sha Allah baxan bari ya sake rike hannuna ba"
Chapter 155 · 0% Book details