← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 207

Sashe 88

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

kaka" ta xaro ido tace "Ai ita bata hira, bata fiye son magana ba ma" Dariya Sadeeq yyi yace "Really?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh" yace "Uhm to shikenan, yaushe xan xo mu yi hiran mu biyu kadai, I want to tell you lot of things Imaan" Murmushi tayi tace "Ae Daddyna na gari bai koma ba tukun" Yace "Toh baxa ki gidan gwaggo ba mu hadu can?" Ta d'an yi shiru, murya can kasa yace "Are you there Imaan?" A hankali tace "Toh gobe xan ce ma Ammina xan je can dama ai saura kwana uku bikin Anty Halima kilan idan na je sai bayan bikin xan dawo gida" yace "Toh shikenan idan kin shirya goben sai ki kirani" ta xaro ido tace "But ai sai Ammi ta amince in je, kasan ba a son ina fita ni kadai" yace "Toh Allah yasa ta amince" Tace "Ameen" da sauri Imaan ta cire duvet din kanta jin kamar ana bude window, ganin farin abu tayi ya fadi kasan dakin, ta sauka gadon ta nufi windon da sauri ta bude labule har sannan waya na kare kunnenta, Mujaheed ne tsaye kusa da window din, ta xaro ido tana kallonsa, yana mata wani kallo ya juya ya bar wajen, ta rufe window din ta durkusa ta dau takardan tana kallo, muryar Sadeeq taji a kunnenta yace "Are you there?" Tace "Yea ina ji" yace "Ko kin fara jin bacci ne" murmushi tayi tace "Um" don so kawai take ta bude takardar ta ga content dinsa, yace "Toh shikenan, sleep like a baby dear" murmushi tayi tace "Toh nagode, good night" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta kunna fitilar wayar ta warware takardan tana haska rubutun kai, xumburo baki tayi ta cukwuikuye takardan ta jefar ta kwanta kamar xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwanka da ni"
Chapter 88 · 0% Book details