Sashe 93
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ba tare ku ka xo ba ai?" Ta girgixa kai tace "Na riga ta" har sannan ta ki yarda su hada ido, a hankali yace "Kinyi kyau sosai, I love the Hijabs you are wearing, you look so cute in them" boye fuskarta tayi tana murmushi, ya dinga kallonta, kamar warce ta tuna abu ta xame hannunta da sauri tace "Na manta na daura abu a kitchen kar ya kone" yace "Xa ki wuce ciki knn?" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri, ai mun gaisa" ya d'an yi murmushi yace "Sure, amma ina son mu yi hira sosai, I told you I've got plenty things to let you know imaan" tace "Toh may be later koh?" Yace "After Magrib or Isha?" Ta gyda masa kai, yace "Ohk then, Allah ya kai mu lkcn, before then wait...." Yana fadin haka ya bude motarsa ya fiddo wani abu kamar box mai kyau yace "You put this on for the wedding" kin amsa tayi, gently yace "Take plss Imaan" ta kallesa a sanyaye, ya gyada mata kai murya can kasa yace "Take it" risinawa tayi ta amsa tace "Nagode" ya mata murmushin da ya bayyana dimples dinsa ta mayar masa da light murmushi sannan tace "Sai anjima" daga haka ta nufi gate ya bi ta da ido har ta shiga gidan, sosai gabanta ya fadi ganin Mujaheed ya fito parlon gwaggwo, ya dinga kallonta ta fara tafiya a hankali, kamar warce aka ture ta durkushe nan kasa ta fara yarfe hannu tana xaro ido, ya karaso inda take yace "Daga ina kike?" Hawaye har ya kawo idonta tace "Ammi ta aikeni, yaya na gurde kafar fa" bai tanka ta ba ya nufi gate fuskarsa daure, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa ta dinga addu'ar Allah yasa Sadeeq ya bar layin, kallon box din da ta boye a Hijab ta dinga yi kafin ta bude a hankali taga babban dankunnen gwal mai kyau sai talli yake a kwance cikin fancy box din....