← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 207

Sashe 3

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita yana waigo Imaan yace "In ji yau baki je tsokanan inna ba ta hada ki da daddy" Imaan tayi dariya tace "Ni ina ruwana da ita ai na daina xuwa part din ta" Daga haka ta juya ta wuce bangarensu. Da daddare Imaan na kokarin saka kayan baccinta ta kwanta Ammi ta shigo dakin, tana kallon ta tace "Ki je Abba na kiran ki" xaro ido tayi tace "Abba kuma Ammi?" Juyawa Ammi tayi ta fita, kamar xata yi kuka ta saka hijab din ta ta fita tana tunanin kiran me Abba ke mata da daddaren nan. A hankali ta bude kofar parlon Abba ta shiga bayan ta cire takalmin kafarta, Abba na xaune a 3 seater cikin parlon Mujaheed na xaune shi ma kan lallausan carpet din dake malale kasa, sai Umma dake xaune kan one seater, Anty ma haka, Imaan ta karasa kanta a kasa ta xauna kasa kusa da Anty, murya can kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Ya karatu" tace "Alhmdllh" yace "Imaan discipline din ki kenan rashin gaida na gaba da ke?" Imaan ta daga kai tana kallon sa, ya daure fuska yace "Ita Hajiya sa'ar ki ce da ba kya gaisheta a gidan nan?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "I am talking to Imaan, kuma ki bar kallona my friend" A hankali ta fara 6ata fuska tana jan yatsunta, lkci daya ta fashe da kuka, Abba ya mata tsawa yace "Daman kuka kika samu don ban xane ki ba yanxu" kuka take yi sosai kamar warce aka duka, Mujaheed ya mike ya mata wani raxanannen tsawa ta mike da gudu ta nufi kofa, xai bi ta Abba ya dakatar da shi yace "Rabu da ita M.A, Allah ya shiryeta" Umma ta tabe baki tace "yaran yanxu da ba a sangarta su ba ma ya aka kare ballantana wannan?" Anty ta mike ta fita parlon, Abba dai bai ce komai ba, imaan bata xarce ko ina ba sai sashin inna, tana shiga parlon ta xube kan kujera ta rushe da kuka, inna ta fito daki da sauri, Yusuf ma dake kwance kan 3 seater ya mike xaune da mamaki yace "Me ya faru Imaan" jikin inna na rawa tace "Me ya samu Aishar?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, tuni inna ta nufi kofa, cikin kuka Imaan tace "Ni ba abinda ya samu Ammina" inna ta dawo tace "Ke dai ki dinga jin tsoron Allah, da yanxu xuciyata ta buga ya kike son 'ya yana su yi, ya zaki shigo da kuka ki janyo min wata fitinar ina xaune" Cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace" inna tace "Wacece haka?" Imaan bata ce komai ba sai kuka, Inna tace "Warcan mata mai kama da zabiya kike nufi wai, ko ba uwarsu fitsararren yaron nan Mujaheed ba?" Imaan ta hadiye abu da kyar tace "Ita" Inna ta share wani xufa tace "Toh xata ga barbadin rashin mutunci yau kuwa, me ta maki?" A hankali Imaan tace "Shine taje ta gaya ma Abba wai ni bana gaisheta alhalin fa ko na gaisheta bata amsawa, shine Abba ya kirani...." Sai kawai ta fashe da kuka, inna tayi wani murmushi tana gyada kai tace "Biri yyi shige da mutum, Sai aka yi ya da ya kira ki" imaan ta kalleta cikin shesshekar kuka tace "Yana min fada....." Tuni Inna ta fice parlon, Imaan ta saci kallon Yusuf da yyi tagumi yana kallon ta ta mike tana turo baki ta fita. Inna na isa bangarensu Yusuf kai tsaye parlon Abba ta wuce, har sannan Abba na xaune da Umma a parlon sae Mujaheed, gaba daya daga kai suka yi suna kallon ta, inna ta tsaya tsakiyar parlon tana kallon Abba tace "Yanxu yaro tun da sauran numfashin Bukar a duniya zaka sa ma 'yar sa ido? Yanxu a kan wannan matar zaka ci mutuncin yarinyar da lafiya ma bai isheta ba sai dai godiyar Allah? Yanxu Ahmadu duk son da d'an uwanka ke maka xaka rufe ido a hadu da kai a ci mutuncin yar sa kwaya daya tal..." Kunce ha6ar xaninta tayi tana matsar kwalla tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba..." Abba kasa cewa komai yyi da farko, can yace "Haba inna, wannan wace irin magana kike...." A fusace tace "Ohh yare nake maka da xaka tambayeni wani irin magana nake, to wllh bari ka ji, a kan Fatima a gidan nan ina iya sa6a ma ko wani mahaluki, kuma baxata gaida matar taka ba, ita katuwar gaida mutane take?" Mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa kamar xai tashi sama inna ta bi sa da wani shegen kallo, sannan ta ja tsaki ta maida dubanta kan Abba dake ta kallonta ta daure fuska tace "Ahmadu yaushe rabon ita matar taka ta kai kafafuwanta bangarena gaisheni? Lallai... ni a su wa xata je gaidawa? Ni din banxa xata gaidar?? To hirrrr wllh, kada wanda ya kara sa ma jikata baki a gidan nan idan ba haka ba sai in sa Bukar ya koma daya gidansa dama shi ya nace xama waje daya da kai, tunda yar sa xa a takura gwara kawai ya bar gidan...Dubi fa Mujaheed haushi ya ji yanxu don na ambaci uwarsa, kana gani saura kiris ya bangaje ni in fadi duk cikin bacin rai, to uwa ta fi uwa ne?? don me kai ma baxa ka tattala ni haka ba, duk ka bi ka daure mata kugu bata gani na da gashi a gidan nan, to mu xuba da ita xan ga ko ita ta haifo min kai duniyar, wannan ai raini ne wllh, wai taji haushi Imaan bata gaisheta ba to baxata gaidata din ba, kar ta kuskura ta sake sa min jika a baki tayi ta kanta kawai a gidan nan" shi dai Abba shiru yyi kansa a kasa, Umma ta rungume hannunta daga xaune tana kallon wani direction din, Abba ya dago yana duban mahaifiyar tasa yace "Kiyi hakuri Inna" ta maka masa wani kallo tace "Sai dai ka ba matar ka hakuri tunda na 6ata mata rai" Tana kai wa nan ta fice. Imaan har ta kusa part dinsu taga shukanta na wake da tayi a babban gwangwani a madadin assignment da aka basu a Agricultural science, a yashe duk root din ya fita daga cikin gwangwanin, ta xaro ido ta ta fi wajen da sauri, lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Wllh nasan Rahma ce xata kwabar min da shuka na" sai kuma ta fashe da kuka na takaici ta durkushe wajen, ba ta lura ba har Mujaheed ya iso wajen, ta juya hawaye sha6e sha6e idonta tana kallon sa ta sake rushewa da kuka, ya daure fuska yana kallon kafarta yace "Me ya faru?" Ta mike cikin rawar murya tace "Yaya kalli fa abinda Rahma tayi ma assignment dina kuma ten marks ne, xa muyi submitting ranan Friday, kalli fa har ya girma, don nawa duk yafi nasu sai ta kwabar min" ganin sai hararanta yake ta juya ta wuce tana ci gaba da kuka, fixgota yyi yana mata wani kallo yace "Shi Abban kika tafi kika yi reporting gun Inna?" Lkci daya ta tsaida kukan da take bayan ta gane biyota yyi, ta fizge hannunta ta kwasa a guje, kiris ya rage ya kamata ta shige parlonsu ta banko kofar tasa key, Ammi dake xaune parlon tana kallo ta mike tace "Meye haka Imaan?" Dariya ta fashe da ta wuce daki da sauri tace "Sauri nake in xo in kwanta fa Ammi" tana shiga bedroom din ta ta sa makulli. Har Imaan ta fara bacci wajajen karfe goma Ammi ta bude kofar dakinta, bude ido tayi Ammi ta hade rai tace "Uban me kika debo ma inna a dakinta?" Ta mike xaune da sauri tace "Na debo mata abu kuma? Haka ta ce?" Ammi tace "Kinga na raba ki da xuwa sashinta ki dauko min magana ba ki ji ko? To ki fito mata da duk ma abinda kika daukan mata gata can bakin kofa" Imaan ta turo baki ta sauko daga saman gadon ta bi bayan Ammi da ta fita, ido hudu suka yi da inna da ke tsaye bakin kofa ta tsuke fuska, Imaan ta hade rai tace "Ni me na dibar maki xaki biyo ni cikin daren nan" Inna tace "Duk cikin jikokina babu mai ta6a min kaya ban basa ba sai ke, duk kece mai mugun halin nan don haka maxa ki fito min da alkaki na, don ba a rame na bar sa ba ina sane da abinda nake ba fara haukacewa nayi ba" Ammi dai ta nemi waje ta xauna, Imaan ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tace "Wai yaushe naje da har xan dibar maki kayan ki ni da ba ci ma nake sosai ba, to ma ba xaki gansa hannuna da xan fita ba" Wani tsawa Ammi ta yi mata tace "Kin tafi kin dauko abinda kika diba ko sai na mare ki" Imaan ta harari inna ta wuce kitchen sai ga ta ta fito da ledan alkakin, Inna ta saki baki ta warce ledan tace "Naga Ikon Allah ni Asabe, da yake Aisha ce ta xauna ta min tuyar bayan ta kwa6a dole ki kwaso ki kawo maku ku ci, to ni kar in sake ganin kafafuwanki a bangarena don halin ki abun tsoro ne, wannan ai ba tarbiya aka maki ba ki shiga har karkashin gadon mutane ki jawo kwalla ki debe min kayana, yanxu banda jinin ka jininka ne kin xata idan na ja Allah ya isa baxai bi ki ba, ni wllh darajar d'a na kike ci a gidan nan gaskiya, kar in sake ganin ki a parlona ni dai dama baki tsinanamin komai sai dai ki malale kan kujera kina mik'a, duk kin ru6ar min da kujeru" tana kai wa nan ta juya ta wuce, Imaan bata yarda ta kalli Ammi ba ta wuce daki ta rufe kofa tayi kwanciyarta tana turo baki.
Chapter 3 · 0% Book details