Sashe 55
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ba" Jan kunnenta yayi yace "Baxa kiyi knocking idan kinji ba a amsa ba kiyi wucewar ki" muryar Umma suka ji a corridor tana ma Maimoon masifa wai ta share datti ta kai bakin kofarta lkci daya kuma tana tambayarta ko Mujaheed na dakinsa, Maimoon da ta hade rai tace "Yana ciki" Mujaheed ya xaro ido ya ja Imaan ya bude kofar bathroom dinsa suka shiga ya kulle kofar, dai dai nan kuma Umma ta shigo dakin tana kiran sunansa, Irin tsoratan da imaan tayi ba a cewa komai, Mujaheed ya dukar da ita kasan bayin murya can kasa yace "Kee you better relax now kar in mare ki, ance maki xata shigo nan ne" kai kawai take gyada masa numfashinta na sama, ya cire Hijab din jikinta yace "Nace maki ba fa shigowa xata yi ba, breath in and out gently now" jingina take son yi da bango ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayan ta a hankali to calm her down, tuni Umma ta fice dakin ganin Mujaheed bai ciki, bayan kusan minti biyar jin tana fitar da numfashin a hankali kuma a nutse ya dago kanta yana kallonta, hawaye ne makale idonta, ya daure fuska yace "What?" A hankali ta nuna masa kirjinta, ya mike ya fita bathroom din ya sa makulli kofar dakin sannan ya dawo ya fito da ita dakin, wajen da yake ajiye drugs da allura ya bude yana dube dube, can kasa ya hango inhaler dinta da take bari a dakinsa a da idan ta xo, ya juya ya kalleta ya ga kwanciya tayi kan gadonsa ta takure waje daya, ya mayar da inhaler din ya mike, ya dau gogaggen jallabiyarsa ya saka don tuni jikinsa ya bushe, ya feshe jikin sa da turare, ya dau drawings da ta ciro ya fara maidawa jikin Bangon, Imaan ta mike xaune tana turo baki xata ce masa don me idonta ya kara sauka kan dambun dake gaban mirror, tashi tayi a hankali har sannan hannunta na kirjinta ta isa gaban mirror din ta dau bowl din, karan bude kofar da yaji ya sa ya juya, xata fita da gudu ya bi bayanta da sauri yana cewa "ke har kin manta abinda ya same ki a bathroom ynxu koh, ba ruwana fa idan...." Tuni ta fara sauka stairs, sai da ya tabbatar ba kowa corridor sannan ya bi bayan ta da sauri, amma har ta fita gidan, can ya hangota a durkushe kusa da apartment dinsu, karasawa yyi kusa da ita a hanxarce, ya durkusa kusa da ita yace "Ba nace kar kiyi gudu ba..." Dagata yyi ganin Asthman ne ya tashi ya amshi bowl din, ya wuce da ita cikin apartment dinsu, Ammi ta tabe baki ta mike ta dauko inhaler ta jefa masu, sai da ya ga numfashinta ya dawo dai dai sannan ya mike ya dau bowl din naman ya ajiye a kafarta yana mata wani kallo ya fita parlon, a hankali take sauke numfashi ta bude bowl din ta fara cin naman.