← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 207

Sashe 133

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Imaan ta bude kofar xata fita sai kuma ta juya tana kallonsa, Bude ido yyi yana kallonta shi ma, ta turo baki ta fita da sauri ta kulle kofar. Inna dake ta xuba waina a plate tana diga miya kamar xa a ba jarirai ta kalleta tace "Har kin fito knn, toh sai ki koma ki tambayar min shi ko in xuba masa wainar, tun safe yake nan ni dai ban ga ya ci komai ba, to rabuwa da ni haukane da xai daga hankali haka? Ni dai ba ruwana" Imaan xata fita Inna tace "Ji walakanci ina mata magana tana wucewa, baxa ki shiga ki tambayar min shi bane in je da kai na?" Dawowa tayi tana turo baki ta shiga dakin, Inna tayi tsaki tace "Babu abinda ta mance a halin ubanta mara kirki, nan ya wanke ni tass jiya da daddare, ni dai na yafe masa ba ruwana, ba don naka naka bane ai yanxu da sai dai in kora figaggiyar 'yar nan tasa ince ta fita, Toh kada laifin ubanta ya shafeta" Imaan na komawa dakin ta samesa idonsa rufe kamar daxu, ta d'an yi jim, can ta karasa kusa da gadon tace "Inna tace ta xubo maka wainar shinkafa?" shiru yyi har sannan bai bude idon ba, tace "Ka ji" nan ma bai ce komai ba, ta d'an ta6a kafarsa tace "Yaya ka ji?" Nan ma shiru kake ji, tabe baki tayi ta juya xata wuce ya fixgota ya bude manyan idanuwansa da suka sauya kala yace "Sai kin min ihu a kai saboda baki da hankali?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta ta6a hannunsa ta durkusa kusa da shi a hankali tace "Baka da lafiya ne Yaya?" Mikewa xaune yyi ta dinga kallonsa, murya can kasa yace "Make me a cup of tea" Mikewa tayi ta nufi kofa ya bi ta da ido, Inna dake duke har sannan tana jiran ta fito tace "Xai ci ko in rabar ma tsofaffin nan?" Imaan tace "Shayi yace in kawo masa" bata jira me Inna xata ce ba ta shiga kitchen ta dau cup ta bude flask ta xuba ruwan xafi a cikin cup din sannan ta dawo tana kallon Inna tace "Ina Kayan shayin?" Inna tace "Wanda ke da shi ku ka siyo ku ka ajiye min kenan, toh kar ma ki bata lkcn ki ki koma bangarenku ki xuba masa kayan shayin a ruwan xafin nawa ya kusa karewa bbu wanda xan ba ma wllh" Wata tsohuwa dake xaune parlon tace "Haba Hajiya Asabe sai kace ba iyayensu ke siya maki ba?" Inna ta mike tana kallonta, can tace "Ehh lallai duniya ta lalace, toh wllh har na mance rabon da iyayensu su siya min kayan tea, sai dai yaron nan Bulasawa, kuma baya jiran wani ya kare yake kawo min wani, kawai mata tsohuwa baki san kan komai ba ki tsomo mana baki muna magana, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah" Tuni imaan ta fice ta wuce part din su tana turo baki, Bedroom dinta ta fara shiga ta dau wayarta tayi dialing number Sadeeq, katsewa yyi ya kirata, a hankali tace "Good morning...." Yace "Morning my dear, hope kin tashi lafiya?" Imaan ta langwabar da kai tace "Sure, happy birthday once again..." Yana murmushi yace "Thanks much baby, I was so happy with ur text earlier this morning, naji dadi sosai baby" murmushi tayi tace "When xaka xo ka amshi gift din ka?" Yace "Ohh wai baxa ko xo party din ba?" A hankali tace "I might, I might not, kasan fa yau muna biki a gida.... But all the same ka dai xo ka fara amsar gift din ka" yace "Ni dai sai kin xo party din dear" murmushi tayi tace "Na ji" yace "Toh yaushe xan taho amsar gift din?" Tana juya ido tace "After Juma'at prayer" Yana murmushin sa mai kyau yace "Toh sai na xo baby" tace "Amma fa kar ka shigo layinmu, ka tsaya bakin titi xan fito" yace "Alryt dear xan kira ki idan na iso" tace "Tohm bye" daga haka ya katse wayar. Kitchen ta wuce don hada ma Mujaheed shayi, Ammi dake bayan kitchen din da Mama Hadiza suna magana tana kallon Imaan ta window tace "Me kike nema?" Imaan tace "Inna xan xuba ma kayan shayi nata ya kare" Ammi bata ce komai ba suka ci gaba da maganan su da Mama Hadiza, imaan ta hada shayi mai kauri ta rufe cup din ta fita, Ko kallon Inna bata yi ba ta shige cikin daki Inna na cewa "Ni dai dakina ya xama kamar kasuwa yau duk a tafi a bar ni da wari..." Ajiye shayin Imaan tayi tana kallonsa tace "Gashi yaya" ya bude ido ya mike xaune ta dau shayin ta mika masa tana kallonsa ya karba, makulli ya mika mata yace "Go to my bedroom and get me my phone" ta xaro ido tace "Ni kuma? A'a sai da in gaya ma Maimoon ta dauko sai ta bani, ni ba ruwana" Bai ce komai ba ya dinga sipping shayin a hankali, Mikewa Imaan tayi ta fita, tana fitowa parlon Inna ta kusa cin karo da Mama Hansai "Inna na ciki kuwa? Ga Ta Rasulu can tana fada da Hajiya Rukayya" Cewar Hansai kenan tana haki ta shige parlon Inna, Imaan dai tayi wucewarta, tsakar gida ta tadda ta Rasulu tsaye tana fadi Umma na fadi, Ta Rasulu na tafe hannu tana jujjuya ido tace "Nan nan aka auro ki kina raka yayarki Shafa tallan shinkafa da wake a kasuwar tasha, Hijabi duk a yakune, Zani duk duwaiwai a waje tsabar kodewa shine kin xo kin samu gida kin xama kamar buhun masara xaki kawo ma mutane raini toh wllh idan ban sa yarana mata sun nakada maki shegen dukar da xai fidda maki hakora uku ba kice ba Yar gidan mai salati bace ni, Ni nafi karfin ki wllh ni ba Asabe bace...." Muryar Inna suka ji tana sakin salati da karfi tace "Rukayya ita aminyar tawa ta Rasulu kike ma xagi ta uwa ta uba?? Ita ta rasulun kike kokarin dambe da?? La ila ha illallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, karshen duniya ta kama, ayi maxa a kira min Ahmadu amma banda Bukar...." Imaan ta girgixa kai tayi wucewarta ciki ta wuce sama, bude kofar dakin Mujaheed tayi ta shiga ta lumshe ido ta nufi saman gadonsa ta dau wayarsa, calls kusan ashirin yyi missing, yawanci kuma duk na Safeenah ne sai abokansa dake ta nemansa tun safe, ta tabe baki ta juya xata fita sai ga kira ya kara shigowa wayar, kallon screen din tayi ganin Safeenah ne tayi tsaki har ta isa kofa sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren Safeenah tace "Haba Mijina, tun asuba Ina ta kira no response are you okay?" imaan ta tabe baki tace "Toh ba shi bane" Da mamaki Safeenah tace "Wacece wannan?" Imaan tace "Kanwarsa ce, sai ki jira idan na kai masa wayar" bata jira cewarta ba ta katse kiran ta fito dakin ta kulle kofar. Ba karamin taro aka hada a tsakar gida ba Inna na ta ma Umma tijara Ta Rasulu na taya ta, ba abinda suka mance basu gaya mata ba, mutane sai bada hakuri suke, Ammi dama ko a gyalenta sai aikinta take, haka ma Mama Hadiza da ta ki fitowa, Aunty ce dai ta taho tana bada hakuri Inna ta tsigaleta ita ma ba shiri ta bar wajen, inna na ganin Imaan ta fixgota tana nuna ma jama'ah ita tace "Tana kamar haka fa Ahmadu ya aurota, amma yanxu ku dubi yanda ta koma kamar alade, Toh komai ta samu raruma take ta boye... ya ki halal ya ki Haram, duk ta tsiyace min d'a na... Shine kuma saboda abinci xata yi ma aminiyata rashin mutunci... Allah ya tsine ma abincin da xa aje a xaxxage a shata, tunda a kansa xaki xagar min Ta Rasulu, to wllh yau sai Ahmadu ya xaba ko ni ko ke a gidan nan ba ruwana, dama har yanxu ban huce casun da kika hanani ganin karshensa ba..." Umma dake ta kai koma ta kinkimo babban cooler din shinkafa da nama, da wani cooler din tuwo da na miya, da na fried rice da soyayyen kaji, da na masa duk ta dire masu a gabansu tace "Ni dai na xama kadangaren bakin tulu, ba kuma wani ya haifa min Mujaheed ba balle a nuna min iko da shi, Ikon ku ya tsaya iya Bukar da Ahmadu amma banda Mujaheed, abinci kuma ga shi aje ayi ta ci ayi kashi...." Ammi dake tsaye gefe ta taho har inda Umma take tace "ke dai a kwakwalwarki hauka ya kare, ita Innar kike fada ma magana haka saboda shinkafa" dakatar da ita umma tayi ta hanyar daga mata hannu tana mata matsiyacin kallo tace "Ni ban yi da juya ba, kije can ki ji da sauran ciwon da kika haifo duniya..." Aunty ta riko Ammi ganin finciko Umma xata yi, babban Jambox Hajiya Saude ta dauka ta kunna waka ya kauraye tsakar gidan kawayen Umma suka fito aka fara taka rawa irin na manya ana jujjuyawa, Umma na ganin haka ita ma ta shige cikin masu rawa ta fara takawa tana tafe hannu, Inna ta gwalo ido sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni kika xaga Rukayya?? Ni din??" Ta Rasulu ta dinga bude kulolin abincin tana ball da su duk abincin ya tarwatse a kasa, tana huci tace "Don kaza kazan ki dake da abincin kun ci kaza kazan ku...." Mama Hadiza ta fito daga part din su Imaan da sauri ta tafi ta dauke jambox din da waka ke tashi ta kashe sannan ta tarwatse sa a kasa tana kunduma ma Umma xagi tace "Idan kina tunanin uwata xa ki gaya ma magana yau ki xauna lafiya kin yi karya wllh, dama can ba son auren nan Mujaheed yake ba, ke ce ke son auren saboda abun duniya, xabin ki ce yarinyar ba tasa ba, kuma wllh wllh kin ji rantsuwar musulmi koh?? To baxa a daura auren nan ba, bari Ahmad din ya shigo.... in sha Allahu sai kin ji kunya yau, sai mun kunyata ki
Chapter 133 · 0% Book details