← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 207

Sashe 26

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Thursday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka ta ci abinci ta fito parlor ta xauna kusa da Ammi dake xaune, ta langwabar da kai tace "Ammi ina son xan je supermarket in siya pad da turarurruka" Ammi ta kalleta tace "Duk uban turarrukan da kika kwaso ranan sun kare kenan Imaan?" Yar dariya tayi tace "A'a ba su kare ba amma sun kai rabi" Ammi tace "Toh sai ki kira babanki bani da kudin da xan baki ki karo turare" Imaan ta bude ido tace "Ya min transfer din 30k ranan da xai tafi ai" Ammi tace "Tohhhh har 30k, lallai kam Allah ya taimaka" dariya Imaan tayi ta mike ta koma daki, Hijab dinta gogagge har kasa ta fiddo ta saka sannan ta dau karamar jakarta ta sa atm card ta feshe jikinta da turare ta fito parlor, ta durkusa kusa da Ammi tace "Toh Ammi ba ni kudin transport don Allah" Ammi tace "Ki duba gaban mirror a daki" tashi tayi ta shiga ta dauko sannan ta dawo parlon, tace "Yauwa Ammi ina son xan biya ta gidansu Mariya, tun Tuesday bata xo schl ba bata da lafiya" Ammi tace "Waye kuma Mariya?" Imaan tace "Lahh wannan da ke xuwa dubani wani lkcn idan bani da lafiya" Ammi tace "Kice min dai gidansu xa ki je ba supermarket ba" Imaan tace "A'a fa Ammi, kawai tunawa nayi, Ban ma san ko xan gane gidan ba fa tunda sau daya muka taba xuwa da Maimoon, idan ban gane ba kawai sai in dawo gida" Ammi tace "Gwara dai ki gane don ki dubota tunda tana yawan xuwa duba ki" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka tayi ma Ammi sallama ta fita Ammi na tunatar da ita tayi addu'an fita gida, tana isowa part din su Yusuf taga Umma da wata kawarta xaune a waje kan fararen kujeru, Imaan ta dauke kai duk da sun hada ido har ta wuce su ta nufi gate, Hajiya Salaha tana kallon Umma tace "Wace fitsararriya ce wannan kuma" Wani murmushi Umma tayi tace "Yar wajen Aisha" Hajiya salaha tace "Ikon Allah ita ce ta girma haka?" Tabe baki Umma tayi, Hajiya Salaha tace "Ita Aishar ta sa kar ta gaishe ki gidan nan kenan?" Umma tayi yar dariya tace "Ga dahir kin gani, ai fa ko idona xai makale cikin nata shegiyar baxata gaida ni ba uwar ta hanata" Hajiya Salaha tace "Tabdi ita wannan yar ficicciyar yar?" Umma tace "Ba shine bayan na dawo gidan nan naga ita da Mujaheed da bai san ciwon kansa ba bai san ciwon mahaifiyarsa ba tamkar su yi 6ude, ya maida Aisha kanwar uwarsa bashi da tamkar ta gidan, ita kuma yar mai ciwo yau mai ciwo gobe tunda sickler ce idan kin ga abinda yake mata ko kanninsa su Ummi bai masu, in takaice maki duk dai Aisha ta bi ta shanye min shi yanda ta shanye kanin ubansa, yanda kika san xai mata sujjada" Hajiya Salaha tace "Ikon Allah" Umma tace "Ae tuni na tashi tsaye, nice can nice nan, da taimkon Allah da taimakon Magajiya na kwato d'a na da karfi da yaji, yanxu ko ga maciji basa yi a gidan bangaren ma ya daina xuwa, I can't risk that, uban waye bai san tsafi Aisha take ba, gashi dai ta hana kanin babansa karo matar da xata haifo masa 'ya yansa duniya ta rufe masa baki ta hada sa da 'ya sickler kullum ana hanyar asibiti ana kashe Dan banxan kudade, Allah kenan, kuma in dai ina numfashi a haka yarinyar nan xata kare yau lafiya gobe babu, in Allah ya yarda sai yar nan sai ta xame masu jaraba duk sai ta tsiyace su muna nan muna gani, kee duk wanda xata ra6a ma wllh sai ya tsiyace, haka nan kuma xata yi ta xama ba mashinshini.... to ubanwa xai iya da ita ta kassara tattalin arxikinsa, ni fa duk duniya billahil azim bani da makiyiya da ya wuce Aisha, wllh xan iya yin komai don in toxarta ta da yarta, ni ko kishiyata ban jinta yanda nake jin Aisha, kuma yanda tasa aka toxarta ni aka min kishiya sai na toxarta ta ita ma ko ba jima ko ba dade, ina nan dai kan bakana lokaci kawai nake jira" Hajiya Salaha tace "Ae ko kar ki yarda wllh, ki mata fiye da wanda ta maki ma" Umma tace "Yanxu gobe ma akwai inda xa ni tare da magajiya da sai ki fito mu je tare, wani take take na fara gani nake son taka ma abun burki tun wuri" Hajiya Salaha tace "Haba na me kuma?" Umma tace "Ki ji fa don walakanci yanxu sai su yi ta makala ma Mujaheed ita ya kai ta asibiti, ga uban kudaden da xai kashe wanda nasan ko ance xa a basa baxai amsa ba to akan wani dalili? Shi ya dauro mata ciwon? Na samu na rabasa da shegiyar yarinyar suna kara lika masa ita to gwara in kara xage damtse, ba wani ke nemo masa kudin ba kuma kudinsa ba na banxa bane, su je can su da suka haifeta su karata da cutan ta" Hajiya Salaha tace "Gaskiya kam Allah ya kai mu goben idan kin fito ki kirani" Tunda Imaan ta fito Yusuf dake xaune tare da mai gadi da sabon drivernsu ke kallonta, yyi murmushi yace "Ina xuwa Imaan din daddy?" Rufe fuska tayi tace "Shopping mana" Ya wara ido yace "Kaji Hajiya Imaan, in taso mu je ki min shopping din nima" dariya tayi ta make kafada tace "mu je dai ka biya min" yyi murmushi yace "abun yar haka ne kenan, to wa xai kai ki?" Ta buda hannu tace "Napep xan shiga" ya bude ido yace "Salon ki kwaso k'ura ki dawo mana da asthma?" Turo baki tayi yace "A'a bari driver ya kai ki ya dawo dake kawai" Ta wara ido tace "Da na ji dadi" Ya kalli sabon drivern dake murmushi yace "Toh driver xa a ajiye mana ita a supermarket" ya mike yace "In sha Allah, bari in fiddo motar" daga haka ya shiga cikin compound din, Sai a sannan Imaan ta ga Mujaheed dake xaune kan farin kujera nesa da su yana danna wayarsa, tana kallonsa ya jefa mata wani harara, ta turo baki ta dawo kusa da Yusuf tace "Ya Yusuf jiya da na fita inna ta debar maka dambun koh?" Dariya yyi yace "Aa bata ban ba" ta tabe baki tace "Ba wani nan nasan dama jira take in tafi sai ta xuba maka ita ma ta ci, ni da ba ma cin dambu nake sosai ba" yace "Ae ko sai kin ji dadin da dambun yyi, cewa tayi ita ma ta rama abinda kika mata" bata fuska tayi tace "Ai nasan sae ta baka nice dai baxata ba" Driver na shiga compound din ya gaida su Hajiya da ladabi yana rike da makullin motar ba ta amsa gaisuwar ba tace "Ina xaka?" Yayi kasa da kai yace "Hajiya karama xa a ajiye a supermarket" Umma na masa wani kallo tace "Anya kasan wanda ya dauke ka aiki gidan nan kuwa?" Shiru yyi yana kallonta, tace "Toh ita warcan da kake gani ubanta daban a gidan nan, kuma ba shi ya dauke ka aiki ba, mai nan bangaren ne ke biyanka don haka ka maida hankalin ka, ka wuce ka ban wuri nan da 'yan mintuna xaka ajiye kawata gida" kansa a kasa ya risina yace "Ayi hakuri Hajiya ban sani bane" tace "Ehh ka sani yanxu ai" hakuri ya kara bata ya juya ya fita compound din, Yusuf na kallonsa yace "Ya aka yi?" Yayi kasa da kai yace "Hajiya ce tace xa a ajiye bakuwarta yanxu" Tsaki Yusuf yyi ya mike Mujaheed ya daga kai yana kallonsa, Yusuf na kallon Imaan yace "jira in dauko mota in ajiye ki" a hankali tace "Toh nagode" banda hararansa babu abinda Hajiya take don tasan shi xai sa driver ya fita da imaan, ta ja tsaki bayan ya fita da motarsa waje, Imaan ta bude front seat ta shiga ya bar layin, sai bayan sun hau saman titi yace "Amma dai baxa ki shanya ni a mota idan kin shiga shopping din ba" yar dariya tayi tace "Kasan me ya Yusuf kawai idan ka kai ni ka wuce ba gida xan dawo ba" Yace "Ina xa ki?" Tace "Xanje duba kawata bata da lafiya" yace "Wani anguwa?" Ta fada masa tana kallonsa yace "Su Imaan an fara hankali xa a je duba Mara lafiya" dariya ta fara yi, har suka isa Supermarket din Yusuf na tsokanarta, Bayan yyi parking yace "Kar ki shanya ni Imaan, in har kika dde to baxa ki same ni nan ba, ga ATM dina kiyi amfani da shi ai kinsan pin din" tace "Ya Yusuf ka wuce kawai ba gida fa xan koma ba nace, kuma Daddy ya turo min kudin shopping din" yace "Anya gidan kawarki kadai xaki je kuwa Imaan" ta turo baki tana kallonsa, yyi murmushi yace "Toh yi hakuri, napep xaki hau xuwa gidan kenan?" Ta gyada masa kai yace "In ji kin fito da nose mask din ki?" Tace "Ehh yana jaka" yace "Toh kar dai ki jima gidan kawar don ni baxan iya ba ammi hakuri ba" tayi dariya tace "Sae ka bata ni dai idan xata dokeni" dubu daya ya mika mata yace "Sai ki hau napep din tunda Daddy ya baki kudin shopping" ta amsa tace "Nagode" daga haka ta daga masa hannu ta nufi entrance din supermarket din. Tun a bakin entrance din yake kallonta har ta shiga mall din yana biye da ita a baya, gun turarurruka ta nufa, bayan ta dau wa enda take so har shidda, ta tafi gun pad, ta duka ta dau pad manya biyu kenan sai gashi yana xuwa toward her, suna hada ido gabanta yyi mugun faduwa don rass ta ganesa, da sauri ta ajiye pads din hannunta ta dau dettol dake wajen guda biyu, har ya iso kusa da ita kallonta yake daga cikin bakin spec dake idonsa, ta dauke kai ta dau wani sabulun ma ta sa a basket din hannunta xata wuxe, yace "Assalamu alaikum" ba tare da ta kallesa ba ta amsa, yace
Chapter 26 · 0% Book details