Sashe 23
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyeta yyi a balcony ta durkushe wajen yace "Baxa ki shiga ciki ba" cikin rawar murya tace "Baxan iya ba ka kira min Ammi" ya kalli kofar parlon sannan ya daga ta yyi knocking, daddy ne ya bude kofar, Mujaheed yyi kasa da kai, daddy yace "Subhanallah me ya faru?" Mujaheed yace "Faduwa tayi parlon inna" daddy bai ce komai ba ya basu hanya, Mujaheed na rike da ita suka shiga parlon, xata kwanta kan kujera Daddy yace "Take her to her room" Mujaheed ya wuce bedroom dinta daddy ya karasa ya bude masu kofar, kan gado ya kwantar da ita, Daddy na kallonta yace "Ina maganin shafan ki?" Kamar xata yi kuka tace "Yana kan dinning table" juyawa daddy yyi ya fita sai gashi ya dawo rike da methylated cream din dake cikin tube, Mujaheed ya amsa yace "Bari in shafa mata daddy" daga haka ya durkusa yana kallon kafar, daddy ya juya ya fita ya rufo masu kofar, cire Hijab din jikinta tayi ta daga rigar baccin jikinta xuwa gwiwa ta marairaice tace "Yaya ka min a hankali plss" ya mata wani kallo xae shafa mata bayan ya matso cream din ta rike hannunsa da sauri tace "Wayyo Ammina" buge hannun yyi ya mike ya turata ta fada kan gadon ya koma ya durkusa ya fara shafa mata cream din tun daga saman gwiwanta har xuwa fararen toes dinta, runtse ido tayi tana yarfe hannu, ya fi minti biyar yana shafa mata daga karshe taji ya daina, a hankali ta bude idonta, taga ya mike yana kokarin rufe tube din, da sauri ta tashi xaune ta bude zip din yar rigar jikinta tace "Yaya saura bayana" xata sauke rigar kamar warce ta tuna abu ta wani xaro ido ta mike tace "ina xuwa" bathroom ta shiga ta dau towel dinta ta sauke rigar jikinta ta cire sannan ta daura towel din ta fito, ta hau saman gado yace "Kee meye haka?" Ta xaro ido tace "Wayyo to ya xanyi ina son ka shafa min a bayana ne, ciwo yake min da daddare" tana fadin haka ta rungume pillow ta sauke towel din, ya second goma yana kallonta, girgixa kai yyi ya bude man ya matso ya hau saman gadon ya shiga shafa mata daga shoulder dinta har xuwa bayanta, ya kusa minti biyar yana hka, can ya leka fuskarta Bayan ya cire hannunsa ya ga idonta a rufe, har ya rufe tube din bata juyo ba bata bude ido ba, duka ya kai mata a kafarta ta mike xaune a firgice tace "Ammi ba bacci fa nake ba" dauke idonsa yyi, ta wani xaro ido tace "Yaya" ya mike ya ajiye tube din gaban mirror ya fita dakin ya kulle mata kofa, daddy na parlor har sannan, yyi masa sae da safe sannan ya fita parlon. Washegari da safe Imaan ta fito sanye da kayan islamiyya ta shiga kitchen sanin Ammi na can, gaida Ammi tayi, Ammi tace "Kin tashi lafiya?" Ta langwabar da kai tace "Bayan Ammi jiya baki shiga kin duba ni ba nasan kuma ba bacci kike ba, faduwa fa nayi a parlorn inna" Ammi tace "Ehh ban shiga ba, ina jin cikin mafarki kika dauko duvet a closet kika rufe jikin ki" Ta xaro ido tana kallon Ammi, sai kuma tayi dariya tace "Ashe ke kika lullube ni" Ammi tace "Ke da kika kwanta zindir" dariya kawai Imaan tayi, Ammi tace "Garin yaya kika fadi jiya" Imaan tace "Plate ne a hanya, shine Inna ta dinga korana wai kar ace a parlonta na fadi, yaya ne fa ya dawo da ni ko tashi bana iyawa, Allah inna ta iya mugunta" Ammi tace "Toh yyi kyau, amma kina kallon agogo dai ko?" Da sauri Imaan ta leka parlor don ganin agogo, cup ta dauka ta koma parlor ta wuce dinning don hada shayi, takwas saura minti biyar ta fita gidan bayan tayi ma Ammi sallama. Tun da ta dawo karfe sha biyu bayan tayi azahar take ta bacci har karfe uku da mintuna, Fitowa parlor tayi don xuba abinci ta ci, ganin jakar Daddy a parlorn ta kalli Ammi dake tattara masa takardunsa tace "Ammi daddy wucewa xai yi?" Ammi tace "Ko xa ki bi sa" shiru tayi lkci daya mood dinta ya canxa, ta dawo kusa da Ammi ta xauna cikin sanyin murya tace "Ammi me yasa mu ma baxa mu koma Abuja gun daddy ba, bana son yana tafiya ya na barin mu" Ammi tayi dariya tace "Toh ai sai ki gaya masa" dai dai nan Daddy ya fito yana waya, ta mike tana kallonsa kamar xata yi kuka, yana gama wayar ya kalleta yana murmushi yace "Ya aka yi mamana" hawaye ya cika idonta tace "Daddy mu ma mu koma Abuja mana, sai kayi ta zama kai kadai" yace "Wataran xa ku koma my dear, kinyi azahar ma kuwa?" a hankali tace "Nayi" yace "Good" tace "Daddy airport xaka je?" Yace "Ehh, flight xan bi" ta marairaice tace "Toh xan raka ka airport plss daddy" Ammi ta jefa mata wani kallo tace "islamiyyar fa?" Ta marairaice tana kallon Ammi, Daddy yace "Ba sai ta shirya ba mu fita gaba daya, idan ya so sai a ajiyeta a makarantar idan sun dawo airport" da sauri Imaan ta shige dakinta don fara shirin islamiyya , da kyar ta ci abinci bayan Ammi ta tilasta sanin bata wani ci abincin ba daxu da ta dawo, ganin daddy ya fita da jakarsa ta kai plate din kitchen da sauri ta fito ta xura hijab din islamiyyarta ta sa safa da takalmi ta dau jakarta xata fita Ammi tace "Ki tafi da jakar laptop din" dawowa tayi ta dau jakar ta fice da sauri ba tare da ta bi ta kan kudin da Ammi ke cewa taje daki ta dauka ba, Mujaheed ne tsaye kusa da motor daddy rike da makullin mota yana jiran dawowansa daga part din inna da yaje sallama, Maimoon ce ta kwalo ma Imaan kira tana tambayarta inda xata, Imaan tace "Ni motar daddy xan bi ku wuce kawai idan kun shirya kar ku jirani" Mujaheed ya hade rai yace "Ina zaki?" tace "Daddyna xan raka airport idan ya so idan muna dawowa sai a ajiye ni a islamiyyar" yana girgixa kai yace "kama gaban ki.... uban wa xai ajiye ki islamiyya ni na maki kama da driver din ki, daina kallona ki bar nan wajen my friend" Hawaye ya fara kawowa idonta ta tsaya tana kallonsa har sannan, strictly yace "Baxa ki daina kallona ki bace min a nan ba?" Juyawa tayi ta nufi sashinsu da sauri, lkci daya ta fashe da kuka, yana ganin haka ya xaro ido yace "Imaan" kin juyowa tayi, ya fara dube duben babban compound din kafin ya bi bayanta da sauri, har ta kusa shiga balcony dinsu ya fixgota ta juyo ta kara fashewa da kukan shagwaba, rikicewa yyi hango daddy da yyi yana tahowa daga part din inna, yace "Toh me nayi maki, kina son kiyi lattin islamiyya ne?" Cikin rawar murya tace "Toh bayan lkci bai yi ba" yana Satan kallon direction din da daddy ke tahowa yace "Toh naji goge idonki mu je" ta turo baki tace "Saboda kaga daddy na koh?"Wani kallo ya dinga mata kafin ya kama hannunta suka koma gun motar, bude back seat tayi ta ajiye laptop dake hannunta ta shiga tana kallonsa ganin irin kallon da yake mata tace "Yaya ka tuna watarana da za mu je gidan Mama fa'ixa abinda ya faru?" Bai tanka ta ba ya dauke kai, sai da daddy ya fara shiga yyi ma Ammi sallama sannan ya fito ya nufo parking space, yana kallon Mujaheed dake tsaye yace "Sorry for keeping you waiting son" murmushi kawai Mujaheed yyi, daddy ya bude back seat ganin Imaan ciki yace "Mamana why not seat at the front" tace "Noo, I am more comfortable here" yace "A'a dawo gaba" Mujaheed yace "Abba tace ta fi son nan ne" Daddy yyi murmushi ya shiga motar shi ma, Mujaheed ya shiga maxaunin driver, mai gadi ya bude masa gate ya ja motar. Sae da suka hau saman titi Daddy yace "Mujaheed pls ku dinga hakuri da grandma dinku, ita haka Allah yayi ta, mu wa enda ta haifa ma muka iya xama da ita balle ku grandchildren, ya kamata kafi kowa sanin halinta tunda ka xauna gunta, kasan abinda take so kasan abinda bata so, plss bana son in ji kun sake samun matsala kaji?" Yana murmushi yace "In sha Allah Abba" Daddy ya kalli Imaan da ta dauke kai yace "Ke kuma kar ki yarda ta kirani tace kin mata wani abu, wllh zan sa6a maki, tsakanin ki da ita respect babu wasan grandma and grandchild tunda bata so, I repeat respect her ynda xa ki respecting Ammin ki" Imaan tace "Ni dama na daina xuwa part dinta.... Kullum sai tace an mata rashin kunya" daddy yace "Don't try dat, you make sure kinje gaisheta everyday, kinsan Allah duk kika yrda ta kirani ta kawo karan ki xan bar duk abinda nake in dawo in ci kaniyar ki" kamar zata yi kuka tace "Toh yaya fa? Ae shima yana mata rashin kunya, Rahma da Ummi ma haka" Ta madubi Mujaheed ya mata wani kallo ta murguda masa baki, daddy yace "Ae duk na ja masu kunne kuma suna jin maganata ke ce dai mai kunnen k'ashi" Imaan ta bata fuska xata yi kuka, the remaining journey to d airport was silent, Imaan dai sai kumbure kumbure take. Suna isa airport din wajen karfe hudu da rabi, suka raka daddy har ciki, daddy na rike da jakarsa yace "Thanks much sai mun yi waya Muhd" Mujaheed ya dukar da kansa yace "Allah ya tsare Abba" Daddy yace "Ameen" yana kallon Imaan dake goge hawayen idonta, murmushi kawai yyi ya mata side hug yace "Sai mun yi waya anjima daughter, na maki transfer ta account din ki" daga haka ya sake ta ya juya ya wuce, Imaan ta fashe da kuka, Mujaheed dai na tsaye har sai da ya tabbatar baya ganin daddy sannan ya kalleta ya hade rai yace "Toh ki bi sa mana" ta gefen ido ta kallesa bata ce komai ba tana kuka, ya ja tsaki ya