Sashe 130
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ji Abban imaan, ai su Mama Hadiza da Hajiya Aisha na wajen ni ba sharri na mata ba, wllh kunya kamar in nutse, dama imu imu ne abun xai xo da sauki amma fa ga dangin amarya sun cika wajen kuma Yan babban gida, bayan ta gama da yarinya mai bada tarihi ta tafi ta kwashe duk abinda aka ajiye ma amarya da ango a gabansu ta wuce ta bar wajen sirara, haka ta dinga ma mutane fada wai kada a xubda datti sun xo cin shinkafa da miya da kaza mayunwata kawai, maganganu dai ga su nan xar kayan kunya xar takaici Abban Imaan, yanxu fisabilillahi hakan ya dace?" Girgixa kai kawai daddy ya dinga yi yana salati, Umma tace "Toh ganin abun sai gaba yake sai naje na sameta nace toh fa ga ruwa can ya cike parlonta ta bar pampon bandaki a bude, shine Inna ta bar wajen ba shiri da kawarta Baaba ta rasulu, yanxu nayi laifi a nan Abban Imaan?" Daddy yace "Aa dai dai kenan" Umma tace "Toh nasan yanxu suna can kila ma ta tara jama'ah ana jirana, kuma ko me xata gaya ma Abbansu Mujaheed wllh yarda xai yi ya xauna a kai, shi sa ma nace bari in maka bayani tukun" daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta, kuma hakan da kika yi shine dai dai, don da ba don haka ba baxa su bar wajen ba, kada ki damu nasan abinda xan yi, kiyi wucewar ki ciki" Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh ngd Abban Imaan da ka fahimce ni" cikin gidan ya nufa ta bi bayansa bayan ta sauke boyayyen ajiyar xuciya. Inna ce xaune parlonta kan tabarma ta daura kafa daya kan daya fuskarta shabe shabe da hawaye tana fyace majina da hankicin hannunta, ta rasulu dake xaune kan darduma ta girgixa kai kamar xata saki kuka tace "Ni Ahmadu babu abinda ya fi min ciwo irin yanda muka dinga yawo muna xaga garin kaduna a adaidaita sahu muna neman wajen casu bayan mun dawo mun ga karya Rukayya take, daga karshe sai dawowa gida muka yi bamu gane wajen ba, mai adaidaita na bala'i mu ma muna bala'i, haka muka yi asaran dari biyun mu don da kyar mai adaidaitan ya amshi dari biyun wai sai dari shidda xa mu basa, wllh mune har sabon kawo neman wajen casu, babu wajen casu babu labarinsa" Mujaheed dai na xaune parlon sai kallonsu yake, Yusuf ma haka, Aunty da Ammi da Mama Hadiza ma duk suna xaune, Abba dai kansa na sunkuye yana sauraronsu, Cikin kuka Inna tace "Duk a kanmu sanyin daren yau ya kare muna yawo a daidaita neman wajen casu kaman yan iska, kuma ace inyi hakuri saboda ba a san ciwo na ba, ni wllh yau duk sai mu tattara mu tafi Police station, wacece kuma Rukayya da xata min wannan toxarcin, me aka yi aka yi ta, Rukayyar banxa Rukayyar hofi, ni dai wllh Ahmadu na xuba ido yanxun nan in ga matakin da xaka dauka kan katuwar nan, bikin ma ni sai in iya cewa a dage sai an bi min hakkina da na Aminiyata ta rasulu tukun, shkkn haka aka kare casun yau banda mu, ba mu ci Yar shinkafa da kazar da aka raba ba" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka, Yusuf ya sunkuyar da kai yana murmushi, Ta rasulu na matsar kwallan da ya cika idonta tace "Ni wllh Asiya bata isa ta min haka ba, don sai dai in sa Muhammadu ya xabi ko ni ko ita...." Sallama aka yi bakin kofa, Inna ta amsa cikin rawar murya tace "Bukar yau dai bamu samu casun bikin Mujaheed ba, Rukayya dai yar iska ce wllh"