Sashe 188
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tace "Lallai kam, ace duk yanda suke da Imaan baya nan xa a kawo lefe da kudin aurenta, abun bai yi ba gaskiya, daxu daxun nan da safe na gama maganan nan" Inna tace "Atohh, ko tsari babu wllh, Ahmadu ya ki saurarata da yake kunnen kashi garesa, ni bari a kara kiransa in jaddada masa halin da na xo na samu Mujaheed a san abun yi" tana fadin haka ta fice kitchen din, Umma ta kashe gas ta bi bayanta da sauri, jakarta ta dauka ta bude ta dau wayarta ta mika ma umma tace "Kira min Ahmadun" Umma ta nemo lambar Abba ta kira ta sa a hands free ta mika mata, Abba na dagawa Inna tace "Toh wllh Ahmadu Mujaheed na nan rai kwakwai mutu kwakwai, ko magana bai iya yi balle ya ci wani abun, idan xa a ji ta nawa to a dakatar da masu kawo kayan nan xuwa sati mai xuwa, aure bai fi rai ba ku ji tsoron Allah Ahmadu.... Mujaheed rai garesa" Abba dake ta saurarenta yace "Sun kira suna tahowa nan da wani lkci, don haka babu fa'idar fasa komai, sannan ba wai jimawa xa ayi ba balle kice, da sun tafi xa mu taho da Abubakar da likita tunda yaro Mujaheed din ya xama" Inna tace "Toh kuwa kun xama abun tsoro wllh, Allah ya mana tsari da ku" daga haka ta mika ma Umma tace "Kashe min wayata maxa, ni dai ina ganin jarabawan rayuwa" Umma ta katse wayar gaba daya rai ba dadi, don tun safe da ta ji labarin xa a kawo lefen Imaan ta gane xancenta bai yi tasiri ko kadan a gun uwar Sadeeq ba, tun sannan ta kasa xaune sai da ta taho gidan Mujaheed don fada ma Safeenah abinda ake ciki, tana xuwa kuma ta iske Mujaheed kwance wai ba lafiya an sa masa drip, abinda ma ya tsayar da su basu fita ba kenan amma da tuni sun baxama neman duk abinda xai sa a fasa shigo da lefen Imaan gida, a hankali Umma tace "Ba a kyauta ma Mujaheed ba amma gaskiya" Inna tace "Toh wa gareni da xan ma magana ya ji, ai Ahmadu ya dauko hanyar lalacewa shi ma, shi dama Bukar bana sa shi a lissafi kwata kwata" Umma tace "Toh ko xaki ma shi yaron magana, naga kuna shiri sosai" Inna ta mika mata wayar tace "Yauwa duba xa ki ga Bulasawa ki kira, ae yana da fahimta, kawai ce masa xanyi Imaan tace tana jin nauyinsa don Allah in masa magana a dakatar da kawo kayan don yayanta bashi da lafiya yana kwance har da karin ruwa leda uku" Umma ta amshe wayar da sauri tace "Toh hakan ma yyi wllh" tana kiran number Sadeeq ta sa handsfree ta mika ma Inna, Inna ta karbe wayarta ta nufi kofar ta fice parlon gaba daya, Umma ta bi ta da wani kallo tana murmushi, dai dai nan Safeenah ta sakko kasa tana kuka sosai har lkcn tana rike da kuncinta, hankali tashe Umma ta nufeta da sauri tana cewa "Lafiya Safeenah me ya same ki?" Cikin kuka sosai tace "Hajiya a kan wannan shegiyar yarinyar Mujaheed xai sa hannu ya mareni har sau biyu, Mujaheed ya rasa warce xai mara sai ni? Mujaheed slapped me???" Bude baki Umma tayi tana kallonta da mugun mamaki tace "Shi Mujaheed din ya mare ki??" can ta juya ta wuce sama kamar xata tashi sama, Sosai Imaan ta rikice jin muryar Umma tana bubbuga kofar dakin kamar xata cire tana kiran sunan Mujaheed, Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta rikosa cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya ka gani ko" Xaunar da ita yyi gefen gado ya duka kusa da ita murya can kasa yace "Relax now, ba shigowa xata yi ba na rufe kofar" Inna ce ta shigo parlor tana tabe baki tana kallon wayarta, ganin Safeenah na rusa kuka ta isa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki, can tace "saboda na xubda girkin da kika masa shine kika xauna nan kina kuka? Ke kya yarda a cuci wani naki??" Bata jira cewarta ba ta wuce sama, tana isa parlon Mujaheed ta dinga kallon Umma dake ta jijjiga kofa, hankali tashe tace "Lafiya?? Makalewa suka yi a ciki??" Umma ta ki cewa komai xuciyarta kamar ya fashe ta huta, da karfi Inna tace "Mujaheed???" Mikewa Mujaheed yyi daga durkushen da yyi gaban imaan da taki kwantar da hankalinta jin muryar Inna ya nufi kofar ya bude a hankali, mari Umma ta sauke masa tana huci tace "ita Safeenahr ka daga hannu ka mara???" Wani salati Inna ta xabga tana kallonta tace "Kina da hankali kuwa Rukayya, Mujaheed din kika mara hka???" Muryar Safeenah suka ji tana cewa "Wllh baxan xauna gidan nan ba yau in har sabida wnn matsiyaciyar Mujaheed ya mareni wllh baxan xauna" Mujaheed ya daga kai yana kallonta fuska daure yace "Ki tafi gidan ku sae na neme ki, kar ki kara ko minti biyar gidana...." Inna tace "Fakat, maxa tattara ina ki ina ki kiyi wucewar ki mayya" gwalo ido Umma tayi tana kallonsa kamar yanda Safeenah ma tayi, cike da karfin hali Umma tace "Safeenar kake cewa ta tafi gidansu Mujaheed??" Bai yarda ya kalleta ba a takaice yace "Ehh Umma ta tafi gidansu" juyawa Safeenah tayi da sauri ta fita parlon, Umma ta kasa cewa komai tana kallonsa with shock can ta juya fuu ta wuce, Inna tace "Tunda kema mayyar ce sabida me baxa ki ji haushin koran Safeenah ba, in sha Allahu xamanta ya xo karshe a gidan Mujaheed...." Shiru Inna tayi tana kallon Imaan ganin hawayen idonta tace "Me aka maki kike kuka?" Kin cewa komai tayi ta juya masu baya, Inna na kallon Mujaheed tace "Kasan yau xa a kawo kayanta da lefe, nace su Ahmadu su jira ka ji sauki ayi komai da kai sun ki saurarata... Yanxu ga dai waya ka Kira min Bulasawa na kirasa daxu ban ji yyi magana ba kila kiran ma bai je ba" Imaan ta juya da sauri tana kallon Inna tace "Me xa ki ce masa??" Inna tace "Wannan ba matsalar ki bace sirri na ne da shi" Mujaheed dai na rike da wayar yana kallonta, ganin haka Inna ta kwace wayarta ta juya ta fita xuwa gun mai gadi don ya kira mata Bulasawa, ganin ana wangale gate din ta tsaya sai ga motar Abba, parking Abba yyi ya fito tare da Daddy da kawu Audu da wani frnd din Daddy daga cikin motar, Inna ta bude baki tace "Kaddai ku ce har sun kawo kayan ni Asabe??" Abba yace "Sun kawo har ma sun tafi, an saka biki nan da wata guda dai dai da lkcn da xa su gama xana jarabawa, sun kuma bada sadakinta dubu dari takwas" Inna tace "Toh da kyar idan Mujaheed xai yafe maku, don wahalan da yyi da ita ku da ku ka haifeta ma baku yi ba, amma sbda butulci ku amshi kudin auren yarinya ba shi sbda cuta ta kamasa?? Toh aji tsoron mutum" daga haka ta juya ta wuce ciki fuska tsuke....