Sashe 12
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya kalli Imaan dake goge hawayen idonta yace "Don yayanki ya debi apples kike kuka Imaan?" Ta marairaice tace "Toh daddy ai ba shi ka siyo ma ba gashi ya kwashe min gaba daya kuma wllh baya cin apple" Daddy yyi murmushi yace "Shi yace maki bai ci" cikin rawar murya tace "Ae nasan baya ci tun da can" Daddy yace "Toh anjima idan na fita xan karo maki" a hankali tace "Toh nagode" yace "Wai amma me ya hada ku da yayan naki all of a sudden Imaan" Ammi da ta fito parlon tace "I am still wondering also, lkci daya aka yi parting" Daddy yace "Ko kin masa wani abun ne dai" ta turo baki ta dawo kusa da daddy tace "Kawai dai naga ya xama mugu ne shi sa na daina kulasa" Dariya kawai daddy yayi, Ammi tace "Har nan ma ai baya shigowa yanxu" Daddy yace "Toh Allah ya kyauta" Imaan tace "Daddy ni dai ka daukan min personal driver dina plss" daddy yace "Ba Abbanku xai daukar maku driver ba, ai mun yi magana da shi bayan tsohon drivern ya wuce" Tace "A'a daddy ni dai nawa daban nake so, kilan ba yanxu driver din ma xai xo ba, yau fa Yaya bai bari na shiga motar ba don na bata masu lkci da kafata na tafi islamiyya shi sa tun da na dawo duk jikina ke ciwo sai da Ammi ta shafa min magani na kwanta da na tashi shine naji sauki"' Murmushi kawai Daddy yayi ya mike yace " Bari in yi wanka daughter " daga haka ya wuce bedroom dinsa, Ammi tace "Sai ki tashi ki kai ma Inna abinci ko yau ma baxa ki ba" Ta kalli Ammi da sauri tace "Ammi ca tayi bata son sake ganin kafata a part dinta fa, kuma in je yanxu ta gaya ma daddy" Ammi tace "Tashi ki dauki abinci ki kai mata nace" Daga haka Ammi ta bar parlon, mikewa Imaan tayi ba don ta so ba ta shiga kitchen, kusan duk abinda Ammi tayi ma daddy sai da ta dibar ma inna duk ta ajiye a basket, Imaan ta dau basket din me dauke da abincin ta fita, har ta isa part din Inna fuskarta a daure yake irin ko kulata din nan baxata yi ba, ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Mujaheed na xaune yana kallon inna dake bada labari tayi mitsi mitsi da ido, banda murmushi babu abinda yake don da wuya yake dariya, su Maimoon da Rahma kuwa dariya har da kyakyatawa, Inna ta saita hannu sama tace "Ji kawai muka yi ratatatata.... Ba sai kakan ku ya shige karkashin gado ya bar ni da halina da 'ya yana ba, lkcn Bukar na bayana sai tsala ihu yake, Ahmadu kuwa fitsari ya dinga saki yayi sau uku a wando...." Ganin Imaan Inna tayi shiru ta jawo daya daga apples biyar dake cikin leda a gabanta ta kai baki, Har sannan su Maimoon dariya kawai suke, imaan ta ajiye basket din hannunta tana kallo chocolates din da Daddy ya kawo mata a hannunsu Maimoon, ta saci kallon Mujaheed ta juya xata fita Inna ta tabe baki tace "Ga dambun naman ki can a daki ni dai na ajiye maki bana bi ta halin ki ba" ba tare da ta juyo ba tace "Bana ci" inna na ci gaba da cin apple dinta tace "To wa yayi asara?" Mujaheed yace "Yana ina a dakin?" Da sauri Imaan ta juyo ta shige dakin, Inna tace "Ya xaka ce yana ina bayan ka ci rabon ka da wanda ma ka dauka ban baka ba" yace "Haba" tayi tsaki tace "Yana nan cikin roba xa ki gansa a rufe, duk naki ma ya fi yawa" Imaan ta fito rike da uban dambun naman da inna ta ajiye mata a bowl mai murfi ta nufi kofa, inna tace "Wannan liyafar hala Bukar ne ya dawo?" Imaan tace "Bai dawo ba" daga haka ta fita, Inna tace "Duk ta ma fige kamar bata cin abinci" Rahma tace "Mu dai ci gaba da ba mu labarin da kike yi don Allah inna" inna ta gyara xama xata ci gaba, mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon. Imaan na komawa bangarensu ta tadda Yusuf ya shigo gaida Daddy, Ya bi ta da kallo ta boye bowl din hannunta tana wara masa manyan idanuwanta tace "Nasan ka ci naka dai" fitowar Daddy parlon yasa Yusuf bai ce mata komai ba, daddy yace "Engnr ashe kana gari" Yayi murmushi yace "Ina nan daddy, da fatan kun iso lafiya" yace "Alhmdllh My son, ya aikin fa" Yace "Mun gode Allah Daddy" daddy ya xauna kujera yace "Madalla, kowa dai lafiya koh?" Yusuf yace "Duk lafiya" Yusuf bai wani dade ba ya mike yace xai wuce, daddy yace "Baxa ka tsaya mu ci abinci ba" Yace "Alhmdllh daddy na ci abinci" Ammi dake dinning tana jera abincin tace "Anya Yaya Yusuf" dariya yayi yace "Ammi wllh na koshi" tace "Toh shikenan" sallama yyi ma daddy ya fita. Bayan magrib daddy xai je gaida inna babu yanda bai yi da Imaan su je ba ta ki, har hakan ya basa mamaki ya tafi shi kadai, inna na goge tiles din parlonta daddy ya shiga da sallama, ta mike tace "Amma dai gaskiya Bukar ka dinga kwa6a ma yar ka ta daina karya, ce min fa tayi baka dawo ba" Ya xauna yana murmushi yace "Sannu inna, ina yini" ta shimfida tabarma ta xauna tace "Lafiya lau, amma ai karya ba shi da amfani kuma a gaskiya Imaan ta iya karya" Shi dai bai ce komai ba, tace "Toh ya hanyan?" Yace "Alhmdllh mun baro hanya" tace "Wannan karan kuma kamar baxa ka sake dawowa ba" yace "Aiki ne yyi yawa Inna" tace "Toh Allah ya bada sa'a ya tsare mana ku a duk Inda kuke, ya maka albarka" yace "Ameeen inna" Tace "Toh ya xa ayi, Allah ya kaddara a can abincin ka yake, banda haka na tabbata da kana gidan nan da ka dinga share min hawaye daga bakin cikin da nake fuskanta" Daddy na kallonta da mamaki yace "Bakin ciki kuma Inna?" Inna tace "Yo bakin ciki mana Habu... Kaga yayanka baxai fito daga masallaci ya tako nan tun asuban ba ya gaisheni sai ina jin wajen karfe tara xai taho da safe ya duka can bakin kofar ya gaida ni a gurguje ya kara gaba, bana sake ganinsa Bukar sai ina kokarin kulle kofa ta da daddare shi ma Allah yasa ya yi minti biyu xaka ga yace sai da safe daga haka ya wuce, Kaga matar nan tasa Rukayya take ko wa? Uwarsu Mujaheed dai wllh kaji rantsuwar musulmi tafi wata biyu ina ga bata tako ta xo nan ta gaisheni ba sai ta gan ni a tsakar gida ko a can bangaren, ita kuma dayar mai kama da fulanin Bararoji wato Amina da suke ce ma Anty sai ta bushi iskarta xata kwaso kafafuwa ta xo gaisheni, ita wnn farar wa take da suna? Uwar wannan yarinya Imaan d'an wankin da take min da duk ta watsar sun xugeta, in kuwa wannan 'ya taka Imaan borinta ya tashi ta ki kawo min abinci to ranan fa da yunwa xan kwanta a gidan nan, Aisha ta fi karfin ta taso takanas ta kawo min da kanta, to me yafi wannan bakin ciki Yaro? Gashi gaba daya 'ya yanku sun rainani sun maida ni ba bakin komai ba, sun maida ni kakarsu tun ma ba wannan katon Mujaheed ba da ramammiyar 'yar ka, sai wannan kazamar Ummi, ni nasan da sun ga ido wllh taka ni xasu dinga yi suna wucewa, isuhu kadai ke raga min a gidan nan sai wannan yarinya Seeyama, Imaan idan ta fara balbale ni wlh shiru nake, haka ma Mujaheed yaron da aka haifa a gabana, to ina dalili ina da gata na ta ko ina don dai d'an abincin da ake yarfa min a kwano sai a maida ni bola" Daddy dake ta saurarenta ya dago kansa a karo na farko yace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace tace "Na gaji da jin wnn axxalumin kalman, ayi ta baka hakuri ana cutan ka, ni dai a fita harkata, don idan tsiyata ta debeni wllh sai an fita har kasashen waje ana nemana" Daddy yace "Xa a gyara Inna, duk ki yafe masu, ita Imaan xan sameta yanxu, shi ma Mujaheed din xan gamu da shi" Tace "Atoh, sai ka xaunar da su ka tambayesu kaji ko xaman gidan ne basa son inyi, ka tambayesu dalilin da yasa basa fitsaran su a waje sai a cikin gida cikin gidan ma a kan uwarka, kayi masu jan ido ka nuna masu bacin ranka Yaro" Daddy yana murmushi yace "In sha Allah" nan suka ta6a hira amma kusan hiran gaba daya na complain ne daga karshe daddy yace mata xai wuce masallaci don an kira isha. Daddy na dawowa masallaci ya dinga kallon Imaan dake xaune parlor tana cin abinci, ya xauna yace "Imaan yanxu ita innar kika mayar abar wasar ki a gidan nan?" Kallonsa ta dinga yi kamar zata yi kuka, ya hade rai yace "would you take ur eyes off me silly girl, haka kike ma uwar ki? I warned you the last time a kan haka shine kika sake repeating foolishness din yanxu ko?" Ta sunkuyar da kanta, ya gyada kai yace "Nasan maganin ki, tashi ki bar min parlor" tashi tayi da sauri ba tare da ta bi ta kan abincin ba ta shige bedroom dinta ta kulle, ita dai Ammi bata ce komai ba, Daddy yace "I don't like this nonsense character of her, ita innar abokiyar wasanta ce, ke kuma Aisha baki taka mata burki, a kan me xata dinga rainata, I don't like that, and I am going to teach her manners soon" Ammi ta tabe baki ta mike ta dauke abincin da ta bari ta kai kitchen ta rufe, ta tsaya kitchen din tana wanke plates da ke sink. Washegari wajen karfe bakwai da rabi Imaan ta fito sanye da uniform din islamiyya, kanta a kasa ta gaida Ammi dake jera breakfast a dinning, Ammi dake kallonta tace "Wato ke