Sashe 74
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.Abba ya juya ya kalli Mujaheed jin abinda inna tace, Imaan ta mike xaune da kyar tace "Ba fa kafana ke ciwo ba" Inna tace "Toh ina ke maki ciwo" Komawa tayi ta kwanta bata tanka ta ba, Ammi dake tsaye bakin kofar dakin sai kallonta take, Abba na kallon Mujaheed da ya kasa cewa komai yace "Amma me yasa xaka haureta jiya?" Ya sunkuyar da kai yace "It wasn't intentional" Abba ya gyada kai yace "It wasn't intentional, OK that's good kayi kokari" Daga haka ya juya ya kalli Ammi yace "Ta shirya ta fito mu je asibiti" daga haka ya fita dakin, Mujaheed ya harari Inna fuska daure xai fita tace "Oho dai ta rufa ma ka asiri amma ko tantama babu haurin da ka mata ne ya ja mata wannan ciwo" Ammi ta basa hanya fuska daure, kansa a kasa ya fita dakin, Inna tace "Kyansa duk inda imaan xata ga Mujaheed daga yanxu ta gudu tayi ta kanta, ni dama tun da naga yanda yake laftar 'ya yan jama'ah a anguwa yana d'an yaye bai fi shekara 3 ba nasan akwai bala'i a gaba wllh, duk ya bi ya addabi 'ya yan mutane da cizo da yakushi a anguwa, kowa ya gansa sai ya adana d'an sa, lkcn d'an Hansai Garba na kamarsa kullum sai ya ciji garba yakushesa, Hansai tayi ta jin haushi don ta xo jegon Huraira a gida, in takaice maki kafin Hansai ta bar gidan idan aka bude jikin garba duk ta6on cixon Mujaheed ne, to kuma meye baxai yi ba yanxu?" Imaan na daga kwance sai dariya take da kyar, Ammi dai ko kallon Inna bata yi ba tana fiddo ma imaan kayan da xata sa, inna tace "Toh Allah dai ya kiyaye gaba yyi maki tsari da shi, amma gaskiya imaan ki guji duk inda Mujaheed yake, idan kun dawo asibitin xan xo dubaki idan Allah ya yarda, tafiya dai ta sha ruwa" daga haka ta fita dakin, Ammi tace "Kin tashi kin shirya ko xaki kwanta nan kina dariyar walakanci ne?" Imaan ta tashi ta saka kayan da Ammi ta fiddo mata, Inna na fita taga Abba tsaye a waje, tace "Ahmadu tafiya dai ta sha ruwa koh?" Yace "A'a xa su wuce tare da Yusuf yanxu, shi Mujaheed xa su je asibiti da Imaan" inna tace "Toh madallah, hakan ma yayi, to ko in bisu asibitin ne" Ta gefen ido Mujaheed ya kalleta da sauri, Abba yace "Ehh to xa ki iya bin su" Tace "Toh bari in kulle dakina kada a barsa a bude gaskiya" daga haka ta wuce sashin ta, Mujaheed ya nufi motarsa don fitar da motar waje, Abba ya bi sa da kallo har ya isa parking space ya shiga motar, Imaan ta fito sanye da Hijab har kasa, da kyar take tafiyar, Abba yace "Sannu mamana, Allah ya sauwake" a hankali yace "Ameen" yace "Mu je can kofar gidan, ban gane fita da motar da yayi ba" tare suka fita compound din, Ya bude ma Imaan front seat ta shiga, Abba na kallonsa yace "Inna na tahowa yanxu, tare xa ku tafi" yace "Ehh na sani" Daga haka Abba ya koma cikin gida, Mujaheed na ta kallon gate har sai da yaga inna ta fito tana washe baki sannan ya ja motarsa yayi zooming off, Imaan ta xaro ido tana kallonsa, yana isa titi ya kashe wayarsa ya ajiye ya dau hanyar asibitin da yake aiki, Sai da suka yi nisa fuska daure yace "Ni kika je kika hada da mamarki koh?" Tace "Ko dai ita taga ina kuka" ya gyada kai yace "Xa ki gane kuran ki" Ta turo baki ta jinginar da kanta da kujera, Suna isa asibitin bayan yayi parking ya juya yana kallonta yace "Sauko min a mota" Bude ido tayi da sauri, ya bude door din motar ya fita, a hankali ta ta bude side dinta ta saukar da kafafuwanta kasa, xagayowa yyi ganin bata fito ba yace "Baxa ki sauka ba" kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Wani harara ya watsa mata yace "To daukan ki xan yi?" Bata ce komai ba ta sauko motar, ya rufe ya kama hannunta suka shiga cikin asibitin. Yana xaune office misalin sha daya bayan ya kunna wayarsa kiran Abba ya shigo wayar, murmushi yyi ya daga ya kai kunne, Abba yace "What's taking you people too long Mujaheed" yace "Drip aka sa mata Abba, jikin da sauki sosai, she is fast asleep now" Abba yace "Toh Allah ya sauwake, why did u left inna behind?" Yace "Abba Kasan yanda take abinta, xuwa xata yi tayi ta fada every slight mistake" Abba yace "Haka ne, da yaushe xa ku dawo kenan" yace "Nan da azahar in sha Allah" yace "Toh Allah ya kai mu" Mujaheed yace "Ameen" daga haka Abba ya katse wayar, Mujaheed ya juya yana kallon Imaan dake kwance kan gadon duba pregnant women tana bacci, mikewa yyi ya isa kusa da ita yana kallon ruwan da ya kusa rabi, Hannu ya kai forehead dinta yaji da dumi har sannan, ta bude ido a hankali, daure fuska yyi yace "How are you feeling now?" Yamutse fuska tayi tana son mikewa xaune yace "Lie still and answer my question" murya can kasa tace "Kai na yana min ciwo" yace "Shi kadai?" Tace "And am hungry" ya kalli abincin da ta ki ci da yawa daxu kafin a mata alluran a sa mata drip ya dauka ya bude ya ajiye kusa da ita ya daga ta xaune, xaro ido tayi tace "Yaya abincin daxu kuma??" yace "Kin taho da abinci daga gida ne" ta hade rai tace "Ni dai baxan iya ci ba bayan ya huce kuma an ajiye k'ura ya gama shiga ciki" wani kallo ya mata yace "Toh sai ki tsaya da yunwar ki ai, wannan abincin dake rufe meye ya samesa da baxa ki ci ba, Bayan har ynxu ma da dumi abincin" yana fadin haka ya dau cokalin ya debi abincin ya kai baki, ta tabe baki ta dauke kai tace "A'a ni dai bana so, tun da safe fa, ko ta gefe gefe ai dust xai iya bi ya shiga, sai dai kai ka cinye a kawo min wani" Yace "Toh xaki ga wani kuwa" daga haka ya kai abincin table dinsa ya xauna ya fara ci, ta dinga kallonsa kamar xata fashe da kuka, ganin ko kallonta bai yi ba tace "Ni dai ka bani waya in kira Ammina ta kawo min abinci" yace "Baxan bayar ba" komawa tayi ta kwanta ta fara kuka har bacci ya sake xuwa mata, mikewa yyi ya rufe sauran abincin da bai cinye ba ya fita office din. Wani takeaway din ya fita ya siyo mata na abinci, yana dawowa ya tasheta ya ajiye mata abincin a gabanta sannan ya juya ya fita, ta mike xaune ta bude abincin ta fara ci a hankali, har ya dawo dakin bata gama cin abincin ba, ya xauna kan office chair dinsa, tana kallonsa tace "Yaya ni baxan iya cinyewa ba" bai tanka ta ba hankalinsa na kan laptop din gabansa, ya gama abinda yake sannan ya juya yana kallonta ya ga ta ajiye abincin ta kwanta, mikewa yyi ya karasa kusa da ita ya dauke abincin ya ajiye ta bude ido tana kallonsa tace "Yaya ina son xan yi magana da Ammina" yace "Baxa kiyi ba" yana fadin haka ya koma table dinsa, ta turo baki ta juya masa baya. Karfe biyu Imaan ta bude ido jin an kama hannunta, ya karasa cire mata drip din yace "How are you feeling?" Ta mike xaune da kyar tace "Da sauki, I want to go home" Yyi disposing roban ruwan ta sakko saman gadon, da sauri ya rikota ganin xata fadi duk da ita ma ta kama gadon, kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Ya saketa yace "Toh ni nace ki sakko?" Komawa saman gadon tayi ya fita dakin, ba a dau lkci ba ya dawo ya dau wayarsa da car key yace "Mu je" ta xaro ido tace "Idan na fadi fa?" Yace "Sai ki tashi" daga haka ya nufi kofa, sauka tayi saman gadon ta tsaya na kusan minti daya har ta ji ba jirin kuma sannan ta nufi kofa a hankali kamar mai counting steps dinta ta bude kofa ta fita, tsaye ta gansa yana jiranta, ya mata wani kallo yace "Da kin bari na sake shiga office din ki gani" daga haka ya wuce ta bi bayansa, sallama yyi da co workers dinsa suka fita asibitin, a Wani pharmacy ya tsaya ya sauka ya siyo mata drugs da aka mata prescribing sannan ya dawo ya shiga motar suka bar wajen, sai da suka kusa gida a hankali tace "Yaya baxa ka siya min kaza ba plss" yace "A'a sai dai in siya maki akuya" murmushi tayi tace "Toh siya min" A waje yyi parking yace "Sauka..." Ta bude motar ta fita sai da ta shiga gate ya ga ledan maganin da ya siya mata" fitowa yyi motar rike da ledan ya wuce ciki da sauri, ganin har ta kusa apartment dinsu ya wuce nasu bangaren kawai, Babu kowa parlon, ya haura sama dai dai fitowar Anty dakinta tace "Ya jikin Imaan din?" Ya saci kallon kofar Umma kafin yace "Da sauki, Umma bata nan ne?" Anty tace "Ehh tun da ta ji kai ka kai Imaan asibiti ta fice gidan tun safe bayan ta gama bambaminta" Mujaheed ya xaro ido ya jingina da bango yace "Wa ya gaya mata Anty?" Anty tace "Abban ku, tunda ba tsoron ta yake ba" Ji yayi xufa na keto masa, Anty ta wuce ta bar sa wajen tsaye, da kyar ya ja kafafuwansa ya wuce dakinsa. Ammi ta hada ma imaan ruwan xafi a bayinta ta fito tace "Ga ruwan ki shiga, saura ki salance ruwan" Tashi Imaan tayi ta wuce dakin nata. Wanka Mujaheed yayi ya shirya jin lkcn Asr yyi yayi alwala ya fita gidan, yana dawowa masallaci dama part din inna ya nufa don Allah yasan yana tsoron haduwarsa da mahaifiyar tasa Inna ta