Sashe 162
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
mutsu mutsu take, Aunty kuwa sai murna take tana sa albarka, Mujaheed ya dinga kallon Imaan da ta ki yarda su hada ido da kowa, hotuna aka shiga yi a wajen, kowa hoto yake son yi da Bulasawa dake kokarin ganin ya bar wajen, Mariya ta ja Imaan daga wajensu Aunty tace "Come let snap with my family plss" haka Imaan ta dinga bin ta har suka isa inda familyn Bulasawan ke tsaye, Mariya ta ja ta xuwa gun Babanta tace "Abba xa mu yi hoto da ita, she is Fatima by name" Bulasawa na kallonta yyi murmushi yace "Maa sha Allah, keep it up Fatima" ta sunkuyar da kai tace "Nagode Abba" Photographer dake wajen ne ya dinga masu hoto, Sadeeq dake tsaye gefe yana kallonsu ya dawo gefen mahaifin nasa, Imaan na ganin haka ta fara kokarin sulalewa Mariya taki bari ta wuce har sai da aka masu hoton su hudu, gaba daya hankalin Umma na kansu kamar idanuwanta xa su fito, ko fasa auren Mujaheed da Safeenah da aka kusan yi kwanaki bai daga mata hankali kamar abinda ke faruwa yau ba, Wai Bulasawa da kansa yayi acknowledging Imaan, duk Aunty na lura da ita, Mujaheed dai na xaune shi ma sai kallonsu yake, Imaan suna gama hoto da Bulasawa ya bar wajen bayan ya bada donation dinsa na progress din islamiyyar, hotuna Imaan suka dinga yi da Mahaifiyar Mariya da kanninta, Mariya ta ja ta xuwa gun Mahaifiyar Sadeeq tace "Mummy xa mu yi hoto" Mahaifiyar Sadeeq na kallon Imaan da lovely smile tace "Ur recitation was sweet.. keep it up" Imaan na murmushi tace "Thanks Ma" Tsayawa imaan tayi kusa da ita aka fara daukansu hota tare da Mariya, Sadeeq dai bai daina kallon Imaan ba, har dai suka gama hoto da family dinsa ta tafi gun su Aunty, nan ma suka dinga hoto da su Abba da Daddy, Safeenah bata yarda ko da wasa suyi hoto da imaan ba haka ma Umma, duk suka ga Imaan na wajen basa shiga hoton, Imaan da Maimoon suka yi hoto da ya Yusuf da wasu daga frnds dinsa, shi dai Mujaheed na xaune yana danna wayarsa, Imaan na kallonsa ta isa kusa da shi ta durkusa a hankali tace "Yaya baxa mu yi hoto ba?" Daga kai yayi yana kallonta da manyan idanuwansa, ta turo baki ta kama hannunsa tace "Ni dai ka taso mu yi hoto plss" Ya d'an yi murmushi yace "To kira photographer din mu yi a nan" Tace "Noo, background din baxai yi kyau ba, ba ga flowers ba" Safeenah dake ta kallonsu ta karaso wajen kamar xata tashi sama ta xauna kujeran dake kusa da na shi har tana neman faduwa, Imaan na kallonta ta mike daga durkushen da take ta d'an tabe baki ta juya, Ba Safeenah kadai ba har Umma kallonsu take tayi mitsi mitsi da ido gashi ba daman yin komai ga Daddy da Abba a wajen, Mikewa Mujaheed yyi ya kamo hannun Imaan yace "Toh let go" Umma tayi still inda take ta bi su da kallo, gun flowers din suka nufa yana rike da hannunta, Mariya ya mika ma wayarsa duk da photographer dake kokarin daukansu yace "plss snap with my phone also" Imaan dai sai murmushi take, suna tsaye kusa da flowers din aka dinga kashe masu hoto kamar xata shige jikinsa, Mariya ma na daukansu da wayarsa Mujaheed couldn't help it but smiled sweetly, ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa tana murmushin ita ma, Safeenah ji tayi kamar xuciyarta ta fashe, ga wani tukuki da take ji a ranta, Umma dai sai murmushin karfin hali take tana gaisawa da jama'ah tana kallonsu ta gefen ido, Aunty dai na ta rarraba ma jama'ah abincin da snacks da suka kawo bayan sun ware na malamai da daliban saukan, Ammi kuma ta dinga raba buckets da books, Su kam familyn Bulasawa nan suka bar komai da suka kawo na sauka tun daga abinci, gifts, da dai sauransu suka yi wucewarsu, tashin hankali gun Sadeeq ganin har suka wuce imaan ta ki ko da kallon inda yake ba a cewa komai, tun da yake bai taba shiga tashin hankali na wannan lokacin ba tun daga jiya har xuwa yau, saukan ma banda Aunt dinsa ta tilasta sa da baxai xo ba, hatta Mahaifiyarsa sai da ta tambayesa damuwarsa gun saukan ganin gaba daya he is moody yace mata ba komai har dai suka bar makarantar bai ga fuskar tunkarar Imaan ba, ya dai je sun gaisa da su Abba da Daddy, sai su Aunty da Umma, sannan suka bar wajen da family dinsa, kafin azahar su Imaan suka bar islamiyyar a various cars xuwa gida, Tun da islamiyyar ta manya ce babu dalibi cikin masu saukan da ke da niyyar bin d'an uwansa dalibi gidansu kamar dai yanda ake yi yawanci, kowa kama gabansa yayi xuwa gidan iyayensa, ni ko nace ko dadi... Lol. Imaan da Maimoon motar Mujaheed suka shiga ta dalilin wayar Mujaheed din dake hannun Imaan don ita Mariya ta mika ma da xa su wuce, Safeenah ta wani hade rai xaune a gaban motar Mujaheed na driving har suka isa gida, yana gama parking Imaan na kallonsa a hankali tace "Yaya ka tuna promise da ka min few years back?" Ya juya ya kalleta, d'an murmushi yyi yace "Ban manta ba" tana murmushi ta sauka motar, Maimoon ta mika masa wayarsa ita ma ta sauka, Mujaheed xai sauka Safeenah ta rikosa fuska daure, juyawa yyi yana kallonta, tace "Ban ga fa'idar xuwan mu gidan nan ba bayan an gama sauka, I think it's better mu wuce gidan mu Doctor" Makullin motar ya jefa mata a cinya yace "Ki wuce gidan sai na xo, I don't think u have the right to tell me what to do and what not to do" daga haka ya rufe motar ya nufi part din su ta bi sa da kallo kamar idanuwanta xa su fito.