← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 207

Sashe 39

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... 😃😃Kasancewar ranan Alhamis ne Imaan na dawowa schl bayan ta yi wanka ta fito ta d'an ci abinci kadan ta koma bedroom ta saka kayanta ta sake fitowa parlor, Ammi dai sai kallonta take don tun daga ganin d'an abincin da ta ci ta san da matsala, Ammi tace "What's wrong with you?" A hankali tace "Ammi cikina xai fara min ciwo ne" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake abincin ya ishe ki?" Kai ta gyada mata ta xauna kusa da ita tace "Ammi na dade fa ban je gidan gwaggwo in gaisheta ba" Ammi tace "Jiya ma ta tambaye ki da muka yi waya, ran Saturday idan kin dawo islamiyya sha biyu sai ki tafi, before four ki taho gida saboda islamiyyan yamma" Imaan tace "Toh Ammi me yasa gobe baxan je ba" Ammi tace "A'a xan je xa mu duba ma Halima kaya an kawo daga dubai, idan kin dawo schl ma baxa ki sameni" Imaan tace "Toh, Ammi ankon mu fa?" Ammi tace "Idan kin je sai ki tambayeta" Imaan tace "Ammi bikin na Anty Seeyama xa a fara yi ko Anty Halima?" Ammi tace "Na Seeyama saura two weeks, Halima kuma saura sati hudu" Imaan tace "Toh Ammi na Seeyama baxa a mana anko ba?" Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kin ishe ni kuma haka" Shiru Imaan tayi, can ta mike tace "Ammi xan je wajen inna" Ammi tace "Toh sai ki dauko magana idan kika tashi dawowa" dariya kawai tayi ta sa takalminta ta fita parlon ta rufe kofar. Inna na share waje Imaan ta sameta, Inna ta mike tace "Baki ji bayana ba Imaan tun daxu ban xauna ba wllh, aiki dai aiki dai, to kuwa idan mutum bai yi aiki ba ai sai kazanta ta ra6e sa, to ni ko yaushe xan yarda hakan ta faru???" Imaan tace "Toh me kike sharewa a nan din, naga ba datti" inna ta xaro ido tace "Toh k'uran dake yashe a kasa kuma uwaki ce ba datti ba?" Imaan ta yi dariya tace "Toh ai sai kiyi ta sharewa" daga haka ta shiga ta bar ta a wajen, bayan minti goma inna ta shigo parlon ganin yanda Imaan take yatsine yatsine ta hade rai tace "Me kuma ya faru?" A hankali tace "Wllh cikina ne xai fara min ciwo" Inna tace "Toh tashi ki tafi gidan ku ba ruwana da wahalan ki, ko ba jini bane" Imaan tace "Toh ai bai xo ba kawai dai yana min ciwo ne" inna tace "Toh kiyi maxa ki tafi uwar ki ta kai ki asibiti, haka wancan karan kika cuce ni kika daga min hankali, ni dai da xaki dinga rufa min asiri duk kika ji baki da lafiya ki daina taho min nan sai kin ji sauki, a gaskiya kina shiga alhakina" Imaan bata tanka ta ba, Inna tace "Kin ko ji abinda nace" Imaan ta daure fuska tace "Sai nan da kwana biyar ko shidda ma xai xo, ni dama haka yake min ba shi bane" Inna ta tabe baki ta mike ta nufi dakinta tace "Ni dai ba ruwana kar a xo a dameni a gigita ni" Imaan ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. wajajen karfe shidda Inna na daki duk ta fiddo da kayan closet dinta tana masu linkin guga jin an bude kofa ta ajiye kayan xata fita parlor, ta labule ta hangi Mujaheed tsaye cikin parlorn, kana ganinsa kasan daga aiki yake don ko tie din wuyarsa bai cire ba kan farar shirt din jikinsa, kallon Imaan dake bacci ya tsaya yi sannan ya kalli kofar dakin Inna, can dai ya karasa kusa da ita ya duka ya kai hannu a hankali kan goshinta yana feeling temperature dinta, sauke hannunsa yyi kan wuyarta ta bude ido tana kallonsa, yace "What's wrong?" Cikinta ta nuna masa kamar xata yi kuka, daga cikin dakin ya ji muryar inna tana cewa "Don Allah a dinga kyakkyawan xato dai, Shikenan ita kuma a rashin lafiya xata kare kamar warce ta kashe mai rai ka wani kai hannu kana tattaba jikinta kaji ko da xafi ko babu, to babu, kuma lafiyar jikata qlau ka matsa wajen tunda fatan ciwo kake mata, dama likitancin hauka ne" Mujaheed ya dinga kallon kofar dakin, inna ta fito tace "A dai ji tsoron Allah a dinga kyakkyawan xato fisabilillahi, lafiyarta lau wllh, al'adarta ce kawai ke kan hanya shine ta langwabe haka, ka shigo kana wani tabe taben jikinta salon a ja mata wani ciwon tunda a haka ake so ta kare" Shi dai kawai tsayawa yyi yana kallon inna fuskarsa daure, can ya juya ya nufi kofa, inna tace "Toh Ina yini... yanxu ka dawo daga aikin kenan" bai tanka ta ba har ya fice parlon. Kafin magrib Imaan ta watsake gaba daya, bata shirya barin part din Inna ba sai kusan karfe goma na dare tare da Yusuf, Inna na kallon Yusuf tace "Isuhu wai daga na fadi ma Mujaheed gaskiya daxu shine har yanxu bai tako nan ba, to me xai bani da Allah bai ban ba, banda ma magana da yake sa ni idan ya xo, ni dai kai da Imaan kun isheni ni kar ma ya sake xuwa" Yusuf yyi murmushi bai dai ce komai ba ya fita yana kallon Imaan dake tsaye gaba daya hankalinta na kan film da ake yace "Ko dai in tafi ne Imaan" tace "A'a ya Yusuf jira ni, ynxu xa a gama" yace "Toh ki kwana nan mana" da sauri ta fice a parlon har tana tuntube, Yusuf ya fara dariya, Inna ta ja tsaki tace "Toh banda ki yamutse min gado ki bar ni da aiki amfanin me xaki min idan kin kwana Imaan?" Yusuf ya kulle mata kofarta suka wuce, a hanya yace "Me yasa baki son kwana wajen inna imaan?" Ta make kafada tace "Karfe uku idan ta tashi sai tasan yanda tayi ta tashi mutum, tayi ta masa surutu har sai baccin ya fita idonsa" Yusuf yyi dariya yace "Dole ma gobe ki kwana can tunda Friday ne" Imaan tace "Sai dai kai ka kwana" daga haka ta shige balcony dinsu tana daga masa hannu yyi murmushi yana kallonta yace "Good night" yana wucewa ta shiga ciki ta kulle kofarsu. "Wannan iskancin da kike ki tafi exams babu karatu baxa ki min shi a gidan nan ba wannan karan" Cewar Ammi kenan tana kashe kayan kallon parlon gaba daya, Imaan ta dinga kallonta kamar xata yi kuka bata dai ce komai ba, Ammi ta nemi waje ta xauna tana danna wayarta, A hankali Imaan tace "Ranan Monday fa ne exams din Ammi, i still have Saturday and Sunday sannan Monday da safe" Ammi tace "Ki tashi ki dau abincin Inna ki kai mata baxa kiyi kallon ba, kuma I promise you har ku gama jarabawan nan baxa ki kunna kayan kallo a gidan nan ba, ko yaushe kika xama dedicated da kallo haka ban sani ba" da mamaki Imaan ke kallonta, can tace "Amma ammi ban taba daukan sama da second position ba fa a schl" Ammi tace "Ur silly First position ba karatu? I want to see ur grade idan kika yi karatu this time around" Imaan ta dauke kai kamar xata yi kuka tace "Ni da ma ba wani kallo nake ba sai lkci lkci kuma da ace 5th nake dauka shine sai ki ce in daina kallo fa Ammi" Ganin kallon da Ammi ke mata ta mike ta sa hularta ta wuce kitchen ta dau abincin inna dake ajiye tun daxu ta fice gidan, har ta isa part din inna ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude kofar ta shiga, xaune ta tadda inna da bowl din fura a gabanta ta daura kafa daya kan daya, Yusuf na xaune parlon shi ma da cup din furan a hannunsa, sai Ummi dake shan furan ita ma, Mujaheed dai idonsa na kan tv ga nasa cup din furan a kusa da shi, Inna na ganin Imaan ta daure fuska ta rufe furan gabanta ta mayar bayan ta tace "Ni dai wllh ya kare, ba ruwana sai kun ga mutum da abu ku wani dinga tururuwan xuwa, to duk na rabar..." Imaan ta ajiye abincin hannunta tace "Toh ni ina ruwana da furanki ce maki nayi xan sha?" Inna ta kalli Ummi tace "Ke tashi ki shigar min da abina ciki" Ummi ta mike ta dau furan ta kai daki ta fito, imaan ta turo baki tace "Sai kace nace xan sha" Inna tace "Toh ai sai ki juya ki tafi koh?" Imaan ta ki fita don har ranta take son fura da nonon barin idan inna ce ta dama kuma ita tayi furan da kanta, inna ta kalli na Mujaheed tace "Dama ga wannan Boss din ya ji sha, ko raina wanda na tarfa masa yayi Oho, da yake Rukayya ce tayi min wahalan aikin furan Ahmadu kuma ya siyo min nonon, cewa ma yayi baxai sha ba ki dauka ki sha, Allah yayi da rabon ki" Yusuf yyi yar dariya yana kallon Imaan, Imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallon TV har sannan, ta kalli rabin cup din furan kusa da shi, inna tace "Tunda fa aka ji yace baxai sha ba fa baxai sha ba, kawai ki dauka rabon ki ne, don ni bani da wanda xan baki in kwana da yunwa" Imaan tace "Toh wai ni nace maki xan sha ne?" Tana magana tana kallon kofar parlon lkci daya ta suri cup din tayi waje a guje Yusuf ya kyalkyale da dariya don yasan abinda xata yi kenan, Inna ta washe baki tana kallon Mujaheed tace "Allah ya kara" mikewa Mujaheed yyi fuska daure ya bi bayanta, Inna ta rushe da dariya har da kyakyatawa tana kallon Ummi tace "Da dai ki tashi ki kulle min kofa da makulli tunda sun fita" Kafin Imaan ta kai rabin hanya dama gaba daya furan duk ya xube saboda gudun da take, Mujaheed ya cafketa daga karshe ta fasa ihu ta sake cup din hannunta ta kama hannunsa tace "Wayyo
Chapter 39 · 0% Book details