← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 207

Sashe 24

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

juya ya fara tafiya, sai da taga yyi nisa ta bi sa da sauri tana goge idonta...A haraban airport din ta tadda Mujaheed suna gaisawa da wata, Imaan ta ja gefe ta tsaya kamar ance ta waiga taga wani tsaye jikin ride dinsa ya rungume hannu yana kallon saitinta ta cikin black glasses dake idonsa, she couldn't tell ko ita yake kallo, ta dai dauke kai da sauri, bayan few seconds ta kara satan kallonsa taga saitin ta yake kallo still, tayi saurin dauke kai, again ta sake kallonsa, cire glass din idonsa yyi yana kallonta da kyau, a hanxarce ta kauda kai tana son tuna ina ta ta6a ganinsa, bata hakura ba ta kara satan kallonsa ganin bai daina kallonta ba ta juya tana kallonsa directly ita ma, murmushi yyi da har sai da dimples dinsa ya lotsa, ya xura hannunsa aljihunsa ya langwabar da kai yana kallonta dai, Mujaheed ya juya yana kallon Imaan bayan sun gama gaisawa da friend dinsa, ya ga sai kallon mutumi kamar ta samu television take, takawa yyi har kusa da ita yace "Do you have any business with him?" Ta turo baki tace "Toh shi ma ai kallona yake" Mujaheed yace "Wuce mu je kar in kwada maki mari" ta gefen ido ta hararesa ta nufi gun motarsa ya bi bayanta, bude front seat tayi ta juya tana kallon mutumin da bai fasa kallonta ba, Mujaheed yace "Wai kina hauka ne" ta turo baki ta shiga cikin motar, tada motar yayi bayan ya shiga suka bar haraban airport din, sun yi nisa sosai kamar ance ta dago kanta ta ga wani waje da ake gashin kaji, ta kallesa da sauri tace "Yaya" kallonta yayi, ta marairaice masa tace "Don Allah ka siya min kaza plss" yace "In siya maki kaza?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "To kudi kika bani?" Ta turo baki, bai sake ce mata komai ba, ganin xa su wuce gun masu kajin tace "Wayyoo yaya plss" kara gudun motar yyi ya wuce wajen, kallonsa ta dinga yi kafin ta dauke kanta, ganin hanyar da ya dauka tace "To islamiyyar fa?" Yace "Sai dai in ajiye ki ki ta fi da kafa daga nan, ni ba drivern ki bane" yana shiga anguwarsu yyi parking gidaje uku kafin nasu ba tare da ya kalleta ba yace "Sauka" bude motar tayi ta fice fuuu ta nufi gate dinsu sai da ya ga ta shiga sannan ya karasa da mota gate din mai gadi ya bude ya shigar da motar. Ko kallonsa Imaan da har kota kusa part dinsu bata yi ba har ta shiga parlornsu, Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo parlon tace "Dawowa kika yi baki tafi islamiyyar ba Imaan?" A hankali tace "Yaya ne yaki kai ni" Ammi tace "Ba har dadin fashi kike ba, ki ci gaba" Shiru Imaan tayi bata ce komai ba, Ammi ta wuce daki ta bar ta parlon. Bayan magrib Imaan na kwance parlor tana kallo, Ammi ta kirata daga kitchen, ajiye remote din hannunta tayi ta mike ta wuce kitchen din, Ammi ta nuna mata abincin Inna tace "Ki kai ma inna" Imaan tace "Ammi da xa mu kai Daddy airport fa sai da ya sake min warning a kan xuwa wajen inna" Ammi tace "So?" Ta marairaice tace "Toh ni kar inje in sake mata wani abu ta kira daddy" Ammi tace "Ni xan dinga kai mata abincin kenan" Kamar xata yi kuka tace "Ni wlh Ammi nace fa baxan sake xuwa part dinta ba har abada" Ammi tace "Toh kar ki je ki bar abincin a wajen" Imaan ta dau abincin rai ba dadi ta fita, Yusuf da Ummi na xaune parlorn Imaan ta shiga ta ajiye abincin, tana kallon Yusuf tace "Ina yini ya Yusuf?" Yace "Lafiya lau Imaan yau ba ciwon kafa kenan" Inna ta kallesa da sauri tace "Kaji wata mugun alkaba'i, kai fata kake kafar su yi ta ciwo kenan? Shi kenan ita kuma sae ta k'are a ciwo kamar warce ta kashe d'an mutum, ku dai 'ya yan Ahmadu baku da kirki, ku dinga sa ma bakin ku linzami don Allah" Yusuf yyi dariya yace "Daga tambaya kuma Hajiya inna?" Inna ta sharesa ta jawo wani leda tana kallon Imaan tace "Gashi nan Mujaheed ya kawo maki daxu, sai ki xauna a nan ki bude ki tsamma kowa don kema haka kike da sa ido, ni wllh ban ma ji dadin zuwanki ba tunanina baxa ki xo ba in cinye inyi nak" Imaan ta bude ledan da sauri, kaza ce babba guda daya sai kamshi da turiri yake, Imaan ta saci kallon kofa sannan ta saci kallon Inna dake goge plate din da xa a dibar mata ta fice parlon a dari da sittin, sake baki inna tayi da plate din hannunta, Yusuf ya kyalkyale da dariya, inna tace "Kaji daya daga dalilin da xa ku ji ance ta tashi kafa ya rike gobe saboda mugun halinta, toh meye kuma nama ni fatima? Halin fulanawan kenan fa rowa da mugunta, shi naman da xata d'an yaga ma kowa shine xata kwasa a guje kamar k'arya?" Dariya kawai Yusuf yake, inna da har hawaye ya kawo idonta tace "Don ubanta ta yi kiba kafin gobe idan ta cinye kaza daya, kuma Allah ya isa rai da aka sa min" Yusuf ya mike ya fice parlon yana ta dariya, mikewa inna tayi tana share idonta ta nufi dakinta tana cewa "Me aka yi aka yi nama kuma don Allah, wani irin nama kuma?? wani irin nama ne ban ci ba a rayuwar nan, kuma shima Mujaheed din da gangan ne, ai yasan shegen rowa gareta da na tambayesa na wa sai ce min yayi xata dibar min, babu yanda ban yi kokarin fahimtar da shi kan cewar da kamar wuya fa shegiyar ta dibar min, to ga karshenta nan ta gudu, a dinga abu ba tsoron Allah" Ummi tace "Toh shi me ye ma na siya mata kaza bayan ko gaishe shi bata yi wlh a gidan nan" Inna tace "Ohon masu, kya bar ni budurwa, ni dai Allah ya isa" Ranan litinin sabon driver da Abba ya daukar masu ne ya kai su schl....🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
Chapter 24 · 0% Book details