← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 207

Sashe 167

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number 07087865788kMikewa Mujaheed yyi da sauri ya wuce sama, Safeenah ta wani tabe baki ta ki tashi sai ma kwanciyarta da tayi kan kujerar, Inna na kallon Imaan da ke tsaye tana kallonta tace "Lafiya kika fito ko basa nan ne?" A hankali Imaan tace "Nima ban sani ba" Inna ta kutsa kai ta shiga parlon tace "Ina kuma xa su ranan lahadi su bar kofa ba makulli kamar tababbu, ko dai baccin asaran suke..." Suna hada ido da Safeenah dake kwance Inna tace "A'a Safara'u, to tace min ba kowa, anya Imaan na da lafiya ma kuwa, Ina Mujaheed din?" Safeenah ta mike tana kirkiran murmushi tace "Sannu da xuwa Inna" Inna ta xauna tace "Yauwa sannu Safara'u, ana ta shan iska kenan, to ba kya sha ba gari duk xafi don ma dai akwai Ac, ai nima idan naji xafin yayi yawa dama daga ni sai yar shimi da xani nake xama na parlor, kar xafi yyi min illa..." Mujaheed ne ya dawo parlon sanye da jallabiya milk color kansa a kasa, Inna na kallonsa ta washe baki tace "Ina kwana Mujaheed" ya karaso ya xauna yana dube duben parlon yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, yau ba aikin kenan" Yace "Sai da yamma" tace "Toh ai jiki da jini, in gaya maka daga gidan ta Rasulu nake mun je mun yi sirrin mu shine nace bari in biyo mu gaisa kafin mu koma gida" magana take masa amma gaba daya hankalinsa na kan kofa, Inna tace "Sai kuma wannan yarinyar tace min baku nan, kai kaji walakanci..." Bata rufe baki ba kamar jira yake yace "Tana Ina??" Inna tace "Oho ni dai ba na shigo ba, dama tun da muka fito take min walakanci tana ganin mai adaidaita xai min rashin kirki ta gudu ta bar mu..." Mujaheed bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa Safeenah ta bi sa da kallon gefen ido, Bai ga Imaan a waje ba ya karasa gate yana kallon mai gadi yace "Warce suka shigo yanxu da kaka ta fita ne?" Yace "Ehh ta fita" Mujaheed ya fita gate din, can ya hangota har ta kusa titi, ya fi minti daya tsaye yana kallonta kafin ya juya a hankali ya koma cikin gidan, Inna na kallonsa tace "Ta ki shigowa ne halan? Rabu da ita ban iya wahala ni dai ai ta aan hanya" Bai ce mata komai ba ya wuce sama Safeenah da ta wani daure fuska ta bi sa da wani kallo. Bayan kusan minti talatin Mujaheed ya sakko downstairs sanye cikin kananun kaya hannunsa rike da makullin mota, Inna na xauna ga plate din farfesun kaji gabanta tana ta yaga tana ma Safeenah hira, Safeenah dai na xaune sai kallonta take uninterested, Inna na kallon Mujaheed tace "Ina kuma xa ka?" Yace "Ba dadewa xan yi ba...." Daga haka ya fita parlon, da sauri Safeenah ta mike ta dau Hijab ta bi bayansa, Inna na cewa "Maxa je ki ku yi sallama" Har ya shiga mota Safeenah ta samesa cike da shagwaba tace "Ina kuma xuwa sweetheart, bayan ka min alkawarin baxa ka fita ba yau" Ya tada motar ba tare da ya kalleta ba yace "Ba jimawa xan yi ba" Tace "Ohk then, bari in raka ka" sai a sannan ya kalleta yace "I don't think it's necessary Safeenah" da wani expression take kallonsa, yace "Forget about the previous plan on what to cook, tunda grandma na nan kiyi tuwo kawai with vegetable soup, I will be back soon" tana masa wani kallo bluntly tace "Wllh baxan yi ba, sai ka taho da tuwon daga inda xaka yanxu..." shi dai ba kulata ba ya rufe motarsa ya gama warming mota ya danna horn mai gadi ya bude masa ya fita. Mujaheed na isa gida yyi parking a waje, ya shiga compound dinsu, tun da ya shiga yake kallon part din su Imaan, gently yake tafiya, ya kalli apartment dinsu sannan ya wuce, yana isa part din su Imaan ya danna bell, sai kuma ya bude kofar yyi sallama ya shiga, Ammi ta leko daga kitchen taga ko wanene, gaisheta yyi ta amsa tana welcoming dinsa ta fito, Bai xauna ba yace "Dama kawai na shigo mu gaisa ne" tace "Toh nagode, ya gida?" Yace "Alhmdllh" tace "Maa sha Allah" ba tare da ya kalleta ba yace "Imaan na ciki ne?" Tace "A'a" da sauri ya juya yana kallonta, tace "Yanxu na aiketa taje kai ma Aunty sako" Bai san lkcn da ya sauke ajiyar xuciya ba yace "Toh, sai anjima" tace "Allah ya bamu alkhairi" fita yyi parlon ya wuce part din su, Umma na xaune parlor da Rahma suna magana kasa kasa, Umma na kallonsa da murmushi tace "A'a sannu da xuwa Mujaheed, yanxu ko nake cewa bari driver ya dawo xa mu je can gidan Hajiya Balaraba daga nan sai mu biya naka, tunda ku ka tare ban je ba" ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Toh ina Safeenar?" Ya mike yace "Tana gida tace a gaishe ku" Umma ta bi sa da kallo ganin sama xai wuce tace "Ina kuma xaka?" Yace "Xan dau wasu takardu a daki" Daga haka ya haura sama, murya can kasa Rahma tace "Ita fa Mariyan ma ba kowa take kulawa ba wllh Umma, bari dai Ummi ta dawo ki ji, ai ajinsu daya har schl" Umma tace "Toh ita Imaan din ta ta6a xuwa gidansu Mariyan ne?" Rahma tace "Suna xuwa da Maimoon sosai ma" Umma tace "Atoh, Da bata xuwa ai baxa su santa ba har su mata kyauta gun sauka, har fa da yin hoto da uwar yaron da kishiyarta" Rahma tace "Imaan da bata kula maza amma saboda taga d'an mai kudi ne she didn't think twice kafin ta fara kulasa, kila ma a gidan nasu suka hadu" Umma tayi wani murmushi, murya can kasa tace "Toh xa ki yi abinda nace maki din?" Rahma tace "Toh umma ai ba shiri muke da ita ba fa, gwara ma Ummi" Umma tace "Toh yanxu ai xata dawo..." Dakin Aunty Mujaheed ya bude yana kallon ciki, Maimoon ce xauna kasa kusa da Aunty dake xaune kan stool tana mata kitso, Imaan kuma na xaune kasan rug tana kallonsu, Imaan na ganinsa tayi saurin dauke kai, ya shiga ya rufe kofa idonsa a kanta, Maimoon ta gaishesa ya amsa, Aunty ta sake kitson da take tace "Welcome son" Mikewa Imaan tayi tace "Toh Aunty ni xan wuce" Aunty tace "Au kin fasa kitson kenan, dama nasan baxa ki yi ba, kice ma Ammi xan shigo nan da anjima" Imaan dake murmushi don ita kanta tasan kawai dai tace Aunty ta mata kitson ne amma ba yi xata yi ba, lokaci daya murmushin fuskarta yyi fading ganin Mujaheed ya fita dakin, tana ganin haka ta hade rai ta koma ta xauna tace "Toh tunda xa ki je shikenan, sai mu koma tare" Aunty tace "Toh shkkn" Mujaheed ya fi minti biyu tsaye corridor ganin bata fito ba ya bude kofar dakin, Aunty tace "Yau dai yan miskilancin na kusa ne ko doctor, Ina yini toh?" D'an murmushi yyi yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Atoh, ka shigo Ina welcoming dinka kayi kamar baka ji ba kuma ka fita" ya shafa kai a hankali yace "An kira ni ne a waya na fita" Aunty tace "Ohk, ya amarya?" Yace "Tana gaishe ku" Aunty tace "Toh muna amsawa" duk irin yanda ya kafe imaan da ido bata yarda ta kalli direction dinsa ba, har ya juya ya fita, Imaan bata bar part din Aunty ba sai da ta gama ma Maimoon kitso suka koma part din su tare da Auntyn, har sannan kuma Mujaheed na xaune parlor, ya bi su da ido har suka fita Imaan ta saci kallonsa suka hada ido da sauri ta dauke kai ta shige gaban Aunty tana turo baki. Daren ranan Imaan na part din Inna suna dakinta, Inna sai famar rura wutan dake kasko take da baki, Imaan kuma na tsaye kamar xata yi kuka, Inna ta ajiye wutan tace "Ke dai ki daina haka imaan, ni wllh idan kina bani wahala xan tattara lamarin ki in xubar a kwandon shara, ya xa ki dinga ban wahala ina taimakon ki? Baxa ki cire kayan ba ki xo ki durkusa, kai wllh Bukar dai ya haifi jaraba" Imaan tace "Toh wai ni kin manta bana son hayaki ne, yanxu idan asthma dina ya tashi fa?" Inna tace "Meye kuma asma? Kiyi ta kira ma kanki ciwo, Ke dai ki ji tsoron Allah, abinda nace d'an minini xan yarfa a wutan ki shaka ko kadan ne sai ki fita da gudu, idan fa aka kashe ki ko digon hawaye na baxan yi asara ba wllh" Imaan ta rungume hannu tace "Wllh bana so ni dai, gwara inyi wanka da shi, haka kawai inje asthma na ya tashi inyi ta wahala" Inna tayi tagumi tace "Kai ina shan wahala ni patuu, ni dai ba don ki kadai Allah ya halitto ni ba wllh" tana fadin haka ta mike ta dau kullin magani ta wuce bayi tana cewa "Sai ki cire kayan, idan ya kama ma in cuda maki maganin da kai na sai in cuda maki baxan yi asaran kudi ne a banxa ba" Imaan na turo baki ta fara cire rigar jikinta, tana cikin cire skirt taji an bude kofar dakin, xaro ido tayi ta fasa ihu ta durkusa a kasa, da gudu Inna ta fito tana cewa "Shikenan ta fada cikin garwashi ta kai ni ta 6aro gun Bukar...." Inna ta gwalo ido ta kalleta ta kalli garwashin wutar don ta tabbatar bata fada ciki ba, Inna na nunata tace "Anya imaan xaki wanye lafiya da duniya kuwa??" Imaan da ta takure gu daya tace "Ni dai Inna wllh kice masa ya fita" da sauri Inna ta kalli kofa ganin Mujaheed tsaye ta xaro ido tace "Me xan gani haka?? Kai ya haka xaka afko mana daki ba sallama, baka ganta a tu6e bane Mujaheed, yaushe ka xama haka?" Shi dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita, Inna ta tafe hannu tace "Yau naga abinda ya isheni, toh tsaye ya gan
Chapter 167 · 0% Book details