← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 207

Sashe 67

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 1 min read

karasa gawar da ba taka ba a gidan nan, idan abu ya sami yarinyar nan gaskiya xan rufe ido in mance ni na haifi Ahmadu in maka tijara kotu ta raba mu Mujaheed," Yace "Toh yanxu ma ki tashi a tafi kotun mana, duk ke ke karanta mata tsayawa da samari tun bata kai ko ina ba a titi, idan aure take so ae sai ta sanar da Abbanta ayi mata ba ta dinga tsayuwa da maxaje ba tare da saninsa ba, ita har nawa take, ni nasan wlh Abbanta bai sani ba, halan Ummi bata bata labarin abinda na mata kwanaki ba" Inna ta saki baki tana kallon imaan dake shessheka a hankali, can tace "Amma gaskiya ke munafuka ce Imaan, samm baki da hali, banda munafurci ya xa ayi kiyi sabon saurayi amma kiyi ta nuku nuku kina boye min?? me xai bani da Allah bai ban ba, shi kuma gantalallen bai san kakarki na da rai bane da bai taba cewa xai shigo gaisheni ba? Ko uwar ki ce tace ki boye min ban sani ba" Mujaheed ya dinga kallonta da mamaki, rai bace inna tace "Toh ni dai ba ruwana, dama ana boye abun arxiki irin wannan Ashe, me na maki da xaki boye min sabon saurayin ki Imaan?"
Chapter 67 · 0% Book details