← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 207

Sashe 62

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.Suna isa gidan bakin inna ya mutu murus sai 'yan idanuwa ganin gida ne ba na wasa ba, ni ko nace dama Umma ce xata yarda 'yar ta ta auri mai rufin asiri kawai?? Inna ta fito cikin motar tana cewa "Fito da kafar ki ta dama in sha Allah gidan xama ne, yi nayi bari na bari, aure kuma da kike gani d'an xaman hakuri ne duk shi muka yi muka kawo yanxu da rai da lafiya, Allah ya maki albarka yasa gidan ki ne ke kadai don na xauna da kishiyoyi ban ji da dadi ba, kishiya masifa ce" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, inna na washe hakora tana kara kallon katon gidan tace "Toh kai Mujaheed baka da abinda xaka ce mata ne ka tsaya wani sandandan kana kallonmu, wannan ai ya ma fi gidanka girma wllh" Yace "Kece baki mata nasihar tun a gida ba amma ni nayi tun a can" Kuka kawai Seeyama take, inna ta hade rau tace "Ji shashanci don Allah, to ki bude ido ki ga gidan mana idan ba sae kin daina shegen kukan nan ba" Mujaheed ya karasa kusa da ita yana kallonta yace "Be the best wife you can be lil sis, wishing you a peaceful married life" rungumesa tayi tana kuka, shi ko ya dinga kallon imaan da ta ja can gefe tana 6a66aka dariya har da rike ciki, ganin kallon da yake mata ta shige cikin gidan da sauri bata kuma fasa dariyar ba, cike da damuwa Inna tace "Ni dai wllh wannan 'ya ta Bukar gani nake kamar ciwace ciwacen ta ya shafi kwakwalwarta, to banda haka taya xa a kawo yar uwarki dakinta tana kuka, ke baki bata hakuri ba kina dariyar mugunta, to Allah dai ya kai mu naki kiga iskanci wllh" tana fadin haka ta janye seeyama tace "Mu shiga ciki kiyi kukan a tsanake kin ji jikalle, kai kuma Mujaheed bayan isha ka xo ka daukeni, idan kuma ya kama a nan xan kwana to shikenan" daga haka suka wuce ciki shi kuma ya fita compound din da motarsa yana girgixa kai. Bayan Magrib da rashin arxiki inna ta sallami duk kawayen Umma yan kawo amarya, Aunty da Ammi dama basu dade ba suka bar gidan, tsaye inna tayi bakin kofa rai bace tana cewa "Wannan ai ba yi bane, sai kace baku da maxaje baku da mafada, amarya dai ga ta an kawota lafiya har ta hakura ta daina kuka, to ai kuma sai kowa ya kama hanyar gidansa sai kuma wata shekarar idan ta haihu, amma duk kun wani ja6e ba niyyar tafiya, a dai dinga jin tsoron, ni ma nan da ku ka ga ban tafi ba kakar ta ce, ni na haifi ubanta Ahmadu, bai baci ba ko da cewa nayi xan kwana, amma mutane karere kawai ku cika gidan yarinya kun ki tafiya, ko ita Rukayyar ce tace ku kwana tare da su bani da labari? To ni dai ba ruwana" Wa enda suka fita iskanci yi suka yi kamar basu ji abinda take cewa ba, wasu kuma haushi yasa duk suka bar gidan, a fusace inna tace "Mata wasu katangala kawai rai ba ga ta sun xaune ma yarinya a gida, ni ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, ku barta daga ita sai kawayenta su ma a xo a sallamesu su kama gabansu mana" Inna na kallon imaan dake kokarin fita ta gefenta tace "Ke kuma ina xaki sanyi ya kare maki ki cuci d'a na da kashe kudi?" Imaan ta turo baki tace "Ina xuwa ni dai" inna tace "Toh kar dai kiyi nisa don Mujaheed ya kusa xuwa yanxu, ba ruwana in kwana su Ahmadu su min fada" imaan bata ce komai ba ta fita, tana ganin motarsa ta gane don layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Imaan, nan ne gidan sistern naki?" Kai ta gyada masa, yace "Maa sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya" tace "Ameen" yace "Amma ba nan xaki kwana ba dai koh?" Ta xaro ido tace "In kwana kuma?" Murmushi yyi ya rungume hannu sa yace "Shi na gani ai, Idan kika kwana ai xaki yi inconveniencing amarya da angon" turo baki tayi tace "Toh ni dama ta ya xan kwana" yar dariya yayi yace "Gaskiya ne, yaushe xa ku koma gida?" Tace "Muna jiran yaya ne, xai maida ni da Maimoon da Grandma dinmu" yace "Ohk yayanku kenan" ta gyada masa kai, yace "Idan bai taho ba let me drop you people mana" ta xaro ido tace "Bayan ma yana hanya yanxu, ai shi ya kawo mu" Yace "Ohk then...." Bata kuma cewa komai ba, shi kam yyi shiru yana kallonta, a hankali yace "Kin yi kyau" Dauke kai tayi tana murmushi, shi dai bai fasa kallonta ba, murya can ciki tace "Kai kuma baka sa glasses dinka yau ba" wara ido yyi yace "Ya 6ata.... sai dai ki siya min wani" ta kallesa tace "Da gaske?" Yana murmushin sa mai kyau yace "Yea" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Ko baxa ki siya min ba" Ta d'an kallesa tace "Xan siya" yace "Toh yaushe xan xo amsa?" Tace "Idan na siya" yace "Toh gobe nake so, I can't do without it" da sauri ta kallesa sai kuma ta dauke kai tana murmushi tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen... Da yamma xan xo amsa" ta girgixa kai tace "A'a kawai ka bar shi next tomorrow" Shiru yyi yana kallon bayanta.... Can yace "Or wancan ne yayan naku?" Imaan ta juya da sauri taga motar Mujaheed yayi parking, ta gyada masa kai a hankali, tunda Mujaheed yyi parking d'an nesa da su dama yake kallonsu, Sadeeq yace "Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa" shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "Is it necessary?" Yayi murmushi yace "Baki son yan gidanku su san ni kenan?" D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni xan shiga ciki in kira su Maimoon" yace "Ohk" gate ta nufa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Sadeeq kuma ya nufesa, sauke glass Mujaheed yyi ya bude motar ganin sadeeq, ya fito yana kallonsa directly cikin ido, sadeeq ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Mujaheed ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Sadeeq yace "I am Dr Abubakar Ahmad" Mujaheed ya gyada masa kai kamar baxae ce komai ba, sai kuma yace "Muhammad Ahmad" Sadeeq yace "Maa sha Allah it's nice meeting you" Mujaheed yace "Same" Sadeeq yace "Alryt xan koma, sae da safe" Mujaheed yace "Ohk... kun yi sallama ne" Sadeeq yace "Sure" daga haka ya nufi motarsa ya shiga ya wuce. Inna bata fito parlon Seeyama ba sai da ta kada kan sauran mutanen dake parlorn, har Mujaheed ya gaji da jira cikin mota, Inna ta fito gate tare da Maimoon da Imaan ta shiga bayan mota tana cewa "Mujaheed kaga Gantalallu kila da so suka yi su kwana a gidan, don da ban masu jan ido ba baxa su tafi ba, ni dai ba ruwana" Maimoon ta bude front seat ta shiga, imaan ta shiga back seat gun inna, Mujaheed dai bai kulata ba yyi reverse, Inna tace "Ni bikin Imaan da na Maimoon ma gaskiya sae na xabi wa enda xa su raka su daki, iyaka kawai in xauna bayan mota ni da su don ina fatan ya xamo rana daya, Mujaheed ya ja mu in kai su dakunan su ya maida ni gida idan Allah ya yarda, ba katuwar da xata bi mu" Mujaheed dai driving yake har ya bar layin ya hau saman titi, lkci lkci ta madubi yana kallon imaan da ta ki yarda ta kalli gaban motar, inna tace "Mujaheed kaga kawayen uwar ka kamar mayu kuwa, wllh da kyar na kora su, duk sun ban wahala, ita ina ta samo su haka wasu lafta laftan mata ba kyan gani kamar aladu? kaii Rukayya dai shahararriyar mahaukaciya ce wllh" taka brake Mujaheed yyi bayan ya tabbatar bbu motar dake bayansa ya gangara gefen titi, inna ta saki salati tace "Lafiya Mujaheed, me ya sami motar" ya bude motar ya fita ya bude side dinta yana kallonta yace "Ita uwar tawa ce mahaukaciya?" inna ta bude baki tana kallonsa, sai kuma ta kalli Imaan tace "Ga reshen bishiya can, sauka ki karyo ki kawo masa...." Imaan ta hade kai da kafarta tana dariya kasa kasa, a fusace inna ta kunduma masa xagi tace "Na ce mata mahaukaciyar sharri na mata, da hankalinta ina ita ina gunduma gunduman matan da ta ajiye matsayin kawaye, wasun su idan suka xaune kanta shegiya nake idan bata suma ba bayan sun latse ta" yace "Ku saukar min a mota ku samu wanda xai kai ku gida Hajiya" kamar jira Inna take ta sauka da sauri tana kallon Imaan tace "In dai kin san motar ba ta Bukar bace ki sakko ki bar masa tsiyar sa" Imaan ta hade rai tace "Inna bai ce har da mu ba fa" Irin kallon da Mujaheed yyi mata yasa ta sauka da sauri don ya dade bai mata irin kallon ba, Inna ta kalli Maimoon tace "Ke kuma idan ba ta Amina bace motar ki sakko kema" Maimoon ta bude front seat ta sakko, inna ta fara matsar kwalla tace "Ku sama min Adaidaita sahu" ko kallonta Mujaheed bai yi ba ya rufe back seat dinsa ya shige motarsa ya kara gaba, inna ta bi motar da kallo tace "Allah dai ya isa, kuma sai Ahmadu ya min iyaka da Mujaheed yau, ni xai toxarta ya walakanta a bakin titi a kan Rukayya" Imaan ta tsayar da adaidaita ta fada masa inda xai kai su, Mai adaidaita yace "Ba can xan yi ba" bai gama rufe baki ba inna ta shige adaidaitan ta xauna, Imaan da Maimoon suka saki baki suna kallonta, Mai napep din ya juya yana kallonta yace "Baaba nace
Chapter 62 · 0% Book details