Sashe 195
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga kun dawo dai dai..." Safeenah ta tabe baki tace "Ni ko ina xan sha masa kamshi ya hango wata a waje, gwara inyi ta lallabasa a haka...." Umma tace "Toh ni ba wannan ba, Safeenah shirye shirye dai sai gaba yake a gidanmu don yau ma aka dauko mai gyaran jiki xata fara mata gyara..." Safeenah tace "Saura sati uku fa Hajiya, ba sai a xuba ido ba a ga ikon Allah, idan fa mutum ya fiye axar6a6i da kyar ya dinga ganin abubuwa yanda yake so, ke dai kawai ki xuba masu ido ki daina damun kan ki, auren nan ance ko an daura bai fi na minti goma ba in ma an daura kenan to me xai dameki, ni ban cika yarda da irin mutanen nan ba amma gaskiya mutumin nan da alama yana da gaskiya sosai, duka duka nawa ya amsa wajen mu..." Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ban son in sakankance ne da maganar mutumi a xo ayi abun nan Ina ji Ina gani, wllh da na shiga uku, shi sa gwara in buga nan in buga can, yanxu ma xan je gidan Hajiya Balaraba" Safeenah ta tabe baki tace "Toh ni dai sai mun yi waya xan hada ma mijina breakfast ya tashi" Bata jira cewar Umma ba ta katse wayar ta ajiye ta ja tsaki tace "Ance maki ba don abinda Mujaheed yyi min sbda yarinyar da irin rainin da take min xan bata lkcina a kan abinda ya dame ki ne, nima ta kaina nake shi sa na xage" shiru tayi tana imagining ace da gaske d'an Bulasawa ya auri Imaan, Tabb har takasu ma xata iya dinga yi ita surkar Bulasawa, kawai wataran sai a wani xo da motoci kusan biyar gidanta a sunan Imaan ce ta xo gaida Yayanta, ta sakko daga motar da gwalagwalai iri iri tana yatsine yatsine tana mata kallon banxa, tabbb, da sauri Safeenah ta kauda tunanin a ranta tana cewa Allah ya kiyaye hakan ma baxae faru ba, in sha Allahu talaka bawan Allah xa ki aura ki xo gidana in taka ki yanda nake so in walakantaki, murmushi Safeenah tayi wai ta hango imaan ta xo ce ma Mujaheed basu da abinci a gida shi kuma yace ta debo mata a nasu ta bata, Safeenah ta tabe baki tace "Ae Kyawunta ma baxai bari wannan mafarkin nawa ya xamo gaskiya ba, Allah dai yasa idan an rabata da yaron Bulasawan ba wani mai kudin xai kuma xuwa mata ba don wannan shine anyi ba ayi ba...." Safeenah ta d'an yi murmushi a ranta tace muna wargaza auren nan xa mu yi mata maganin bakin jini in sha Allahu, ita da aure sai dai taga wasu na yi, shiru tayi tana tunanin to kada kuma fa ta rasa miji wataran iyayen suce a hadata da yayanta tunda da aure tsakaninsu.... sosai gaban Safeenah ya fadi ta xauna gefen gado da sauri xuciyarta na bugawa, lkci daya ta girgixa kai tace "A'a gwara dai a rabata da d'an Bulasawan kawai, duk tsiyarta kuma baxata sake samun kamarsa ba sai dai kasa da shi" murmushi Safeenah tayi ta mike ta fita dakin dai dai fitowar Mujaheed daga bedroom dinsa, rungume sa tayi tana shigewa jikinsa tace "What should make for breakfast sweetheart?" Tabe baki yyi ya kauda kai. Sosai Imaan tayi wani fresh tayi kyau ta dalilin gyaran da aka fara mata, har wani sheki da glowing skin dinta yake, duk ta gifta ka dama kamshin da xaka ji na musamman ne, a haka kuma take fita tayi jarabawa kullum, tun biki na saura sati biyu dama wayarsu ya ragu sosai da Sadeeq, yawanci kuma ita ke kiransa ma, shi ko sai dai ya bi miss call dinta. Yau Wednesday Imaan na dawowa daga exam bayan tayi wanka ta sauya kaya Inna ta xubo mata abinci da yaji nama ta ajiye mata a kusa da ita tace "Ni dai wai yaushe xa ku gama wannan kaddararren jarabawan ne ki nutsu waje daya a maki gyaran nan cikin kwanciyar hankali, wannan ae fitina ne ana gyara yana bin iska tunda kullum sai kin fita..." Imaan na kallon abincin da Inna ta ajiye mata tace "Ni fa bana jin yunwa" Inna ta kalleta da sauri tace "Ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, ko kumallon kirki fa baki yi ba daxu, a haka xa a kai ki gidan Sadeeq din nan da sati biyu a rame duk k'ashi a wuya?? Ni dai ba ruwana bari Amina ta shigo tunda Aisha ta sallama mata ke gaba daya" Imaan ta tura abincin xata kwanta kan kujera a fusace Inna tace "Ni fa bana son a dameni gaskiya sai ince ki tattara kayanki ke da mata mai gyara ku koma bangaren ku yanxu nan, ya xan dinga maki magana kina walakanta ni, dama katuwar mata mai gyaran jiki ce tace ki ci abinci kafin ta dawo taje siyo wasu kayayyaki a kasuwa ta dawo, to idan ta dawo ba ki ci ba fa..." Imaan tace "Inna to ko dai yaya ba shi da lafiya ne har ynxu?" Bude baki Inna tayi tana kallonta da mamaki, can ta xauna tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe, waye kuma Yaya??" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Inna tace "Wai akwai abinda ya hada ki da Mujaheed ne bayan kasancewar Ubansa wan ubanki? Akwai wani dangantaka tsakaninku ne dama da ban sani ba? Wato kwana biyu shiru bai shigo ya takura ki ba shine duk kika damu tunda ke gantalalliya ce, toh sai ki tashi ki tafi gidansa, Toh wai ma ina ruwanki da wani yaya ke da xa ki yi aure nan da kwana sha biyar? Ko dai akwai ajiyar ki a gunsa ne bai baki ba kafin a kai ki daki in kirasa ya baki?" Imaan ta wani hade rai tace "Toh kawai daga tambaya? Naga ya dade bai xo ba kuma ba haka yake ba" Inna tace "Toh idan lalacewa yyi ya fara hakan fa?? Ko idan ya xo me xai bani banda ya tsokane ki ya cuce ki ya wuce don ma naga tunda yayi aure yyi hankali ya daina sa ki kuka, Ke dai ki dinga jin tsoron Allah kiyi ta kanki ba ruwana, to ni ko shekaranjiya na sa Ummi ta kira min shi katon ya ki dauka, wa ya sani ko fushi yake na daina xuwa gidansa, sai kace gidan aljanna Allah na tuba, ni dai ba ruwana wllh" daga haka Inna ta shige daki, imaan ta bi ta da harara ta jinginar da kanta da kujera bata ce komai ba.... Ana saura kwana 7 biki Imaan ta gama jarabawa kasancewarta science student, Maimoon da Mariya kuma nan da kwana shidda xa su gama jarabawan don art class suke, yau kusan kwana hudu basu yi waya da Sadeeq ba, bai kirata ba ita ma bata kirasa ba, tana bedroom din inna bayan la'asar hannunta rike da hisnul Muslim wayarta ya fara ring, daukar wayar tayi tana kallon mai kiranta, ganin number Sadeeq ta daga ta kai kunne tayi shiru, shirun shi ma yyi na kusan second goma sannan yace "How are you?" Murya can ciki tace "Am good" yace "Ina waje" ta kalli agogo bata dai ce komai ba, yace "Or are you busy?" Tace "Ni ba bari na ake ina fita ba..." Ya d'an yi shiru sannan yace "What did you mean?" Tace "Bana fita" yace "Ohk gida ake biyo ki da papers din ki kenan?" Turo baki tayi tace "Waye ubana da xa a biyo ni gida da papers?" Yace "What exactly are you trying to say?" Kin cewa komai tayi, Yace "Ohk then kar ki fito..." Xai katse wayar frnd dinsa Saleem dake tsaye gefensa jikin motarsa ya amshi wayar ya kai kunne yace "Haba amarcy ba dadewa fa xa kiyi ba, ki d'an fito pls, just few minutes" a hankali Imaan tace "Toh" Saleem ya katse wayar yana kallon Sadeeq yace "Amare fa lallaba su ake basa laifi Dr" Sadeeq dai bai ce komai ba yana rungume da hannunsa, Saleem yyi murmushi yace "To saki ran kafin ta fito mana" Nan ma dai Sadeeq bai tanka sa ba, Hijab Imaan ta saka sai dai ba har kasa ba, ta fito parlor ta sanar ma Inna sadeeq na kiranta a waje, Inna dake xaune parlon tare da mai mata gyaran jiki suna hira sai kallon takwarar tata take, can a hankali cikin sanyin murya tace "Ashe dama haka kike da kyau ban sani ba Imaan?" Dariya sosai mai gyaran jiki ta shiga yi tana kallon Inna dake sa ta nishadi tun xuwanta, kwata kwata bata gajiya da fadan Inna da labaranta masu kai da marasu kai, ga uwa uba tsaftarta, komai na Inna burgeta yake, Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba bata dai tanka Inna ba ta nufi kofa ta fita, Inna na kallon mai gyaran jikin tace "Allah kuwa yar nan, dubi fa yanda take walkiya da kyalli, ga kamshi kaca kaca ta ko ina a jikinta, duk inda ta gilma sai ya kamu da kamshin da take yi, ni dai xan kara maki dari biyu da tsinkin sabulu a kudin da xa su biyaki, gaskiya kin fito min da jikata, kai har dambun nama xan maki ni dai" Matar dai sai dariya take tana ma Inna godiya, Imaan na isa part dinsu ta shiga don daukan hijab mai tsayi, Ammi ta fito daga kitchen jin an bude kofa, Imaan ta gaisheta sannan ta nufi dakinta, Ammi ta bi tada ido, ba a dau lkci ba ta fito sanye da hijab har kasa, tana kallon Ammi a hankali tace "Ana kirana a waje ne..." Shiru Ammi tayi tana kallonta, hakan yasa Imaan ta sunkuyar da kanta, Ammi ta karaso kusa da ita ta sa ta xauna saman kujera ta xauna kusa da ita tace "What's wrong with you Imaan?" Imaan ta kalleta da sauri tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Noo there is something kar ki ji komai ki gaya min..." Imaan ta girgixa mata kai a hankali tace "Da gaske ba komai Ammi...." Ammi tace "Toh shikenan, but don't forget baki da wanda ya wuce ni a duniya, idan baki gaya