Sashe 58
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko sati ba ayi ba fa?" Tace "Ba shi bane kawai alama ne" Inna ta xabga tagumi tace "Ke kam kina ganin jarabawa iri iri a rayuwa na lalura, banda haka jinin ma idan xakiyi sai kin ta fama, anya kuwa ba a sa maki hannu ba imaan?" Imaan ta xamo daga kan gadon tace "Wayyo ni dai ki kira min yaya " Inna tace "Waye kuma yaya?" Hawaye na sakko mata tace "Ni dai ki kirasa" Inna tace "Toh su wa encan tsofaffin duk tsami sun cika min parlor kamar ni xan aurar da 'ya sun ki tafiya, ni dai na gaji wllh ana damuna, wata ma ni nafi shekara talatin ban gan ta ba, ni dai gaskiya sun isheni suje can bangaren da ake biki kuma sun ki, duk parlona ya gauraye da warin tsofaffi, wannan fitina da mai yayi kama" Imaan na son yi dariya amma ciwo yaki barin ta tayi, Inna ta fita fuska daure ta kashe TV da ke aiki tace "Kada TV ya buga in ja ma Ahmadu asara gwara a bar shi haka nan ya huta" daga haka ta dau wayarta ta fita don neman me kira mata Mujaheed, wata ta samu a tsakar gida ta nufeta tana kallon mata yan gayu xaune tsakar gidan, tace "Toh dai gida ba na bitilman bane duk wanda ya xubda ko kwayar shinkafa yyi hakuri ya share fisabillahi, kar a tafi a bar mu cikin wari cuta ta kama mu" mika ma matar wayar tayi tace "Gashi Idan kin iya karatu ki duba lambobi xa ki ga ansa Dakta, lambar Mujaheed ne shi ya sa mun shi a haka, sai ki kira min idan kuma baki iya ba don Allah kar ki rikita min wayar in shiga uku" murmushi matar tayi ta nemo number tayi dialing ta mika ma inna, ta amsa ta kai kunne, sai da yayi ringing sau uku sannan Mujaheed ya daga, inna tace "Mujaheed??" Mujaheed yace "Ina ji, ya aka yi?" Inna tace "Toh ga yar uwar ka nan dai rai a hannun Allah, duk inda kake ka rufa mana asiri ka juyo ka dawo, ni sae in iya cewa a daga bikin ma wllh don idan ta mutu ni nayi asara...." Da mamaki yace "Wacece?" Inna tace "Wacece banda Imaan, tun safe Ashe tana dakina babu inda bata mirgina ba don ciwo, tun daga kan gadon har kasan tass, wai yanxu na shiga dakin don kulle bandakina saboda marasu hankali masu shiga bayin mutum suyi kaca kaca da shi kawai naga yarinya duk ta hada xufa a kan gado kai kana ganin ta kasan...." Mujaheed ya katse ta yace "Ina hanya" daga haka ya katse wayar, Inna tace "Atoh haka kawai, bikin banxa bikin hofi..." Daga haka ta nufi part dinta, tana durkushe bakin kofa tana watsi da takalman jama'a can gefe ganin duk ya cika mata bakin kofar ta ji muryar Mujaheed a bayan ta ta mike, tace "Wannan uban sauri haka kamar wanda ya biyo jirgi, to ka shiga tana can ciki ban san isilinta ba" Shiga parlon yayi ganin mutane ya sunkuyar da kansa ya gaishe su ya wuce dakin Inna, karasawa kan gadon yayi yana kallonta yace "Me ya faru?" Ta fashe da kuka sosai tace "Yaya cikina" hannu ya kai cikin yace "Tun yaushe?" Ta cire hannunsa tace "Ni ba cikin bane ke min ciwo, period ne" ya daure fuska yace "Toh me xan maki, ba kin sha magani ba" da kyar tace "Bai yi ba, doctor Habib allura yake min" yace "Toh me ya hanaki kiransa?" Tace "Yana Lagos" yace "Toh bani da allura a nan sai na koma asibiti" ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Toh ka tafi da ni asibitin plss" tana fadin haka ta fara kokarin sauka kan gadon, bude baki yyi ganin yanda tayi ma inna stain din kan gado, bai san lkcn da ya dauke kai yana murmushi ba don har ya hango inna, ita ma xaro ido tayi tace "Na shiga uku yaya" yace "Aa sai ta gani xaki ki shiga ukun ai, yanxu kina daya ne" ji tayi gaba daya ba ciwon ta sauko kasa da sauri jikinta na rawa tace "Wayyo yaya ya xan yi" Tana fadin haka ta nufi bathroom ta murda ta ji a rufe, tsayawa kallonsa tayi kamar xata yi kuka tace "Yaya ta sa makulli" parlor ya koma gun inna yace "Inna xata shiga bayi ina makullin" inna ta mike da sauri tace "Auzubillahi, wani bayin? Aa ta fito ta tafi nasu idan ma baxata iya tafiya ba ka goyata, haka kawai bayina fess ta shiga ta sa min k'arnin jini" Kunya ma yasa Mujaheed ya kasa cewa komai don mutanen dake parlon sun kai shidda, ganin inna xata shiga dakin ya rigata shiga da sauri, ya dau dankwalinta ya rufe saman gadon da shi, Imaan ta marairaice tana kallon inna da ta shigo tace "Don Allah ki ban makulli wllh xan wanke maki bayin" Inna tace "Ai uwata bata ce min je ki kya gani ba, don haka ba bayina xa a shiga a min kazanta da jini ba, ki daure ki tafi can bangaren ku idan ma tafiyar ne baxa ki iya ba sai Mujaheed ya goya ki" Kuka Imaan ta fara yi tace "Na fa ce xan wanke maki wllh" a fusace Inna tace "Kai ku fita ma ku bar min dakina kuje can bangaren ku karata, da na bar ki ma kika kwanta min saman gado duk da ban san al'ada kike ba" Mujaheed yace "Toh ki bata xan wanke maki bayin da kai na" Inna kamar xata rushe masu da kuka tace "Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, wai ana dole ne, hypo uku na xuba bayin nan daxu da safe da nake wankewa, a kan wani dalilin xa aje a bata min da karni...." Ya katse ta yace "Ni kuma xan xuba maki hypo biyar" da kyar da kyar da sidin goshi inna ta bada makullin shi ma sai da aka yi yarjejeniyar baxa a bude mata drum din ruwa ba kada a xuba kazanta, Mujaheed ya dau buckets biyu ya fita debo ruwa a waje, Ita dai imaan na tsaye sai satan kallon saman gado take, Mujaheed na ajiye ruwan a bayin ta bi sa ciki tace "Wayyo yaya pant da pad da xan canxa fa?" Ya kalleta da mamaki yace "Ni ma kike tambaya?" Ta marairaice tace "Plss ko xaka je dakina...." Ya jefa mata wani kallo yace "You are stupid" fitowa bayin tayi ta bude gun kayanta a wardrobe din inna, ai ko taga panties dinta na nan, tace "Yaya toh saura pad" Yace "Bari in xama pad din ki sa" Bata ce komai ba ta turo baki ta shiga bandakin ta rufe, juyawa yayi ya fita, ya tafi gun mai kiosk dake layin ya amso always daya ya dawo, inna dai na xaune ta daura kafa daya kan daya tace "Allah ni dai ya dubeni ya rabani da k'arni, komin xuba hypo da xa ayi a bandakin nan" Mujaheed bai ko kalleta ba ya shiga dakin, yana ta tsaye har Imaan ta fito daure da towel din inna, ya jefa mata pad din kan gado, ta turo baki tace "Thank you" komawa bandakin tayi ba a dau lkci ba ta fito, yace "Sai ki cire xanin gadon ki wanke" ta xaro ido tace "Yaya ya min nauyi fa" bude baki yyi yace "Toh ki bar shi haka nan" kamar xata yi kuka ta isa kan gadon ta shiga cire xanin gadon bayan ya dauke pillows din kai, Muryar inna suka ji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, jinin ta xuba min a kan gado ni Asabe????" Inna ta fashe da kuka tace "Me na maki xaki saka min da haka Imaan" Mujaheed ya dauke kai yana kokarin danne dariyarsa, imaan duk ta gigice, inna tace "Toh sai ki Kwashi xanin gadon don ubanki ki Bukar kai ma Aisha ta wanke min, kai kuma ka fitar min da katifar waje ka sa min shi a setin rana, Allah ubangiji ya saka min, daga taimako sai ta xuba min al'adarta a xanin gado k'arni ya kashe ni" Inna ta kara rushewa da matsanancin kuka tace "Sannan d'an walakanci tana yoyon xata dau tawul dina ta daura salon ta goga min gaibu, ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, tana cutata a gidan nan" Imaan ta wani hade rai kamar xata yi kuka, Mujaheed ya cire xanin gadon ya wuce bathroom da shi, Inna na matsar kwalla ta daga hannu biyu sama tace "Allah kaga xuciya daya nake xaune da kowa gidan nan, duk mai nufina da sharri ka min iyaka da shi" Tana fadin haka ta share idonta ta fita tace "Bari xanje inji ko Aishar ce ta sa ki xo ki cuce ni yau" Imaan ta murguda baki ta fiddo kayanta a press ta saka, bude kofar bathroom din tayi ta ga Mujaheed yana aikin wanke xanin gadon.Imaan dai na tsaye har ya gama wankin bedsheet din tana rike da kayan da ta cire, ya saka xanin gadon a bucket ya fito, a hankali tace "Yaya to wankin bayin fa?" Wani mugun kallo ya watsa mata ya dau wayarsa da makullin mota da ya ajiye kan gado zai fita ta xaro ido tace "Yaya don Allah ka tsaya, baxan iya shanya bedsheet din ni kadai ba ai" ko juyowa bai yi ba balle ya tanka ta, a bakin kofar parlor ya hadu da Inna, Inna ta gwalo ido tace "Har an wanke min bayin?" Yace "A'a xan fita in amso Hypo ne" yana magana ne yana kokarin fita, inna ta cakumosa tace "Sai dai ka raina ma Bukar ko Ahmadu hankali, ce maka nayi bani da hypon?" tana fadin haka ta ja sa xuwa bedroom din fuskarta daure, yace "Toh ki sakeni mana" ko saurarensa bata yi ba har suka shiga dakin, Imaan dake labe bayan kofar dakin tana jin sun shigo dama ta fito da sauri ta fice a dakin, Har bandakin Inna ta turasa ta dauko Hypo biyu ta jefa masa, yace "Biyar fa kika ce Inna" a fusace tace "Toh ai ni ba asararriya bace Mujaheed, Ko sisin Bukar da Ahmadu babu a Hypon,