← Book details Imaan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 207

Sashe 36

Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daxu Aisha tace ai kin ma tafi boko" Imaan ta tabe baki tace "Lafiya ta qlau kawai dai umarnin Abba nake bi" inna tace "Umarni kuma? Umarnin me ya maki?" Imaan ta buda ido tace "Ba ce masa kika yi kar na sake xuwa bangaren ki ba baki son ganina, shine ai na daina xuwa" Inna ta kalli Yusuf tace "Oh oh Allah, isuhu kaji wata magana irin na Ahmadu ko, dama an san babba da hadin fada, ni yaushe muka yi haka da shi, daga nace yayi mata fada ta daina haka gidan aure xata kuma ba halin xaman gidan miji kenan ba, shine xai ce nace kar ta sake xuwa min? To ina da masu xuwa ne idan ba ita ba ko shi xuwa yake yi ya xauna min, ni dai a dinga jin tsoron Allah gaskiya" Yusuf yyi murmushi yace "Toh ba ga ta nan dai ta xo ba" Inna na kallon imaan tace "Ni ban yi haka da shi ba gaskiya, ga soyayyen naman ki can na ajiye maki tun jiya a daki, naki ne da na Mujaheed shima kwana biyu ban gansa ba sai ki diba naki ki bar masa nasa" Imaan ta turo baki ta wuce cikin dakin, daukan bowl din tayi ta bude taga soyayyen naman cow din sai kamshi yake ta xubawa, ta xauna gefen gado ta kirga gaba daya taga yanka sha takwas ne, murmushi tayi ta fita don dauko leda a kitchen, Inna tace "Kin diba naki" tace "Leda xan dauko a kitchen" daga haka ta shiga kitchen din ta dau leda biyu ta boye daya, tana rike da daya ta fito ta koma cikin dakin, equal ta raba naman ta debi nata, cikin sauran da ya rage ta debe guda hudu ta xuba a daya ledan ta ajiye sauran, ta window ta jefar da guda hudun da ta dauka sannan ta fito parlor, inna na kallon hannunta tace "In ji baki kwashe naman ba nace naki da na Mujaheed ne, don gaskiya nasan halin ki" ta xaro ido tana nuna mata ledan tace "Duba ma ki gani, guda sha takwas ne na kirga na dau tara na bar masa tara" Inna tace "Yauwa kinyi dubara" Yusuf da ke ta kallonta yana murmushi yace "Are you sure imaan" da mamaki ta kallesa tace "Me that don't even like eating meat sef" murmushi ya kuma yi yace "Eh naga alama" Inna ta tabe baki bata dai ce masu komai ba, Ummi ce ta shigo parlon rike da abinci ta kawo ma inna, inna ta bude warmer din ta girgixa kai tace "Mayar masu, ce masu aka yi xaman abinci nake a gidan nan shekaranjiya a ban shinkafa da miya jiya a ban dafaduka yau kuma a ban koren shinkafa, maida baxan ci ba" Yusuf yace "Toh ae ba iri daya bane wannan fried rice ne fa" Inna tace "Toh Isuhu ni kenan a cin shinkafa xan kare, wlh na gaji da kaddararren shinkafar nan, Ahmadun baya ajiye abinci ne" tana fadin haka ta jawo warmer din da Imaan ta kawo ta bude, shinkafa ce da miya sai salad a gefe shi ma, Yusuf ya fara dariya, Imaan ma ta kyalkyale da dariya, inna tace "Toh Allah ya mana tsari" tana fadin haka ta kalli Ummi tace "Ke Mujaheed ya dawo ne ko yana can yana siyar da abinda ya kasa a titi?" Ummi tace "Ya dawo, tare muke tahowa kuma ya tsaya yana waya " Bata rufe baki ba sai ga shi ya shigo da sallama, farar 3 quatre ne jikinsa da bakar riga, Inna ta tura kulolin gabanta tace "Mujaheed don Allah irin wannan tuwon da ka taba siyo min nake so ni dai" ya karasa parlon ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Ae sun tashi masu siyarwan" tace "Ni dai don Allah ka rufa min asiri ka tafi, su tashi su je ina?? Bayan ga maza masu fita titi cin abinci ta dalilin rashin iya girkin matansu" Yace "Ki tambayi Yusuf da karfe shidda suke tashi" yana fadin haka ya bude warmer din abincin kusa da ita yace "Wannan kuma fa" tace "Haba Mujaheed shinkafa dai shinkafa dai inje basir ya cafke ni, wa nake da shi da xai nema min magani, wllh baxan ci shinkafa jiya in ci yau ba, wannan ai mugunta ce ma" Mujaheed ya tabe baki yace "Toh ai sai ki sha tea ki kwanta" Ta maka masa wani kallo tace "Kai xaka gaya min abinda xan yi ko raini?" Yusuf ya mike yace "Toh bari a samo maki tuwon idan basu tashi ba" daga haka ya fita, Inna tace "Toh Allah yayi maka albarka, Ya baka abinda kake nema duniya da lahira, to dama? idan ba kai ba waye, Allah dai ya ma albarka" Mujaheed ya kalleta ta gefen ido xai fita inna tace "Ga namar ka can a daki, baxan biye ta halin ka ba ni dai" Ya juyo yace "Nama na me?" mikewa Imaan tayi ta nufi kofa ta fita sum sum, inna ta bi ta da kallo baki bude tace "Toh kuwa idan ba wani ikon Allah ba ta kwashe rabon naka, Ummi tafi daki ki dauko min roban naman, ai ni naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba" Ummi ta tafi dakin ta dauko bowl din naman inna ta amsa ta bude tana kallo ta saki salati ta ajiye ta rike ha6a, Mujaheed ya dau roban yana kallon sauran naman, inna ta sauke ajiyar xuciya tace "Ta kwashe wllh, gaskiya dai wannan 'ya ta Bukar bata da hali, muguwa ce ta innanaha, ni wllh da xaka burgeni Mujaheed ka bi ta har gaban uwarta ka kwato min namana gaba daya na fasa badawa" Ya ajiye bowl din hannunsa bai dai ce komai ba, Inna tace "Idan kuma baxa ka ba ni sai in tashi inje, ya xata kwashe min nama gaba daya bayan na mata bayani, naman fa yyi yanka kusan ashirin shine ta bar maka hudu, ni dai rabona da a sani magana haka tun kwana uku da suka wuce, to bata xuwa.... yau kuma ban san uban me ya kawota ba" Yace "Sai da safe" bai jira cewar inna ba ya fita parlorn, motsin da yaji a bangarensu Imaan yasa ya tsaya duk da bai yi niyyar tsayawa ba, durkushe ya ganta a balcony dinsu tana tattara shoes dake wajen xata shigar da su ciki, yana kara taku daya xata gansa saboda hasken dake wajen hakan ya sa ya tsaya, mikewa tayi ganin alamar xata fito ya koma baya da sauri ya tsaya jikin flowers, socks dinta da ta shanya take kwashewa, da sauri ya nufeta tana ganinsa ta saki takalman hannunta da socks ta gudu xuwa balcony dinsu, Amma tuni ya kamata ta xaro ido kamar xata yi kuka tace "Yaya me nayi kuma?" Ya daure fuska yace "Ina naman da kika kwashe" tace "Yaya nama kuma, ni fa guda shidda na dauka" yace "Dauko shiddan" tace "Toh ai rabona ne fa" ya mata wani kallo yace "Na fara wasa da ke gidan nan koh?" Kamar xata yi kuka tace "Toh tasan ba bani xata yi ba kuma ba ni ta ajiye ma ba meye na sa min rai, baxan sake xuwa parlonta ba ma" yace "Eh dauko naman" durkusawa tayi ta dau kayan da ta saki, tace "Mu je parlor in baka" yace "Baxan shiga ba ki dauko min" tace "Toh ni dai idan baka shiga ba baxan baka ba" ya wani daure fuska yace "Ke wai yaushe na xama mate din ki a gidan nan?" Tace "Toh xaka tsammin plss" ya fixgota yana mata wani mugun kallo har tana jiyo numfashinsa, Bata sake cewa komai ba yace "Tafi ki dauko min" a hankali tace "Toh" sannan ta nufi balcony din ya bi bayanta ya tsaya yana kallonta, ta bude kofar ta shiga sannan ta juyo tana kallonsa, wani murmushi tayi ta wara masa ido tace "Good night yaya" daga haka tayi banging kofar da sauri ta sa makulli, sosa kansa yyi bayan kusan second goma ya juya ya fita balcony din yana murmushi. Imaan ta fito daki jin Ammi na kiranta, da mamaki tace "Ammi ina xa ki kuma?" Ammi na rike da flat shoe dinta tace "Kin manta yau xa a kawo lefen Seeyama" Imaan tace "Ohh na manta, to ni Ammi baxan je in gani ba" Ammi tace "Toh girkin da na daura fa?" Shiru tayi kamar xata yi kuka, Ammi tace "Toh idan shinkafar ya nuna ki kwashe sai ki taho" Imaan ta washe baki tace "Toh" Ammi na fita parlon ta tafi kitchen da sauri tayi ta tsaye tana jiran dahuwar shinkafar, daga karshe da sauran ruwa a ciki ta kwashe a warmer ta fita da sauri, Hijab ta sa har kasa ta bar gidan xuwa part dinsu Maimoon, har an kawo akwatunan ta tarar masu kawo wa ma har sun tafi, Anty ce da kawayen Umma uku suka shiga buda tsadaddun akwatuna set shidda da aka kawo, Ammi dai na xaune parlon, parlon cike yake da mutane duk yawanci yan uwan Umma da Kawayenta, Imaan ta nufi inda Maimoon ke xaune duk suna jiran a bude akwatuna su fara ganin kaya ta durkusa, Umma dai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana tsaye, Kanwar Umma Hajiya Mariya ce tace "Imaan fa an xama yan mata" Imaan tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini Mama" Umma ta wani daure fuska tana kallon kanwartata, Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Imaan ya schl ko kun gama secondary din?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a Mama muna ss1" Hajiya Mariya tace "Maa sha Allah, Allah ya baku sa'a" Umma na kallon hajiya mariya tace "Ban ga amfanin ki xaune nan ba Mariya da ki tashi ki bar nan kawai" Murmushi kawai Hajiya Mariya tayi ta mike nan suka dinga fiddo kayan akwatunan, Ammi dai bata tashi ba, Maimoon ta ja Imaan kusa da boxes din wai su ga kaya, Imaan na daga kaya taga wani arnen kallon da Umma ke mata, sunkuyar da kai tayi bata sake yunkurin matsawa kusa da boxes din ba, kaya maa sha Allah sunyi kyau sannan masu tsada, Hajiya Laraba tace "Kai maa sha Allah lallai Seeyama tayi goshi, Allah ya sanya alkhairi ya sa
Chapter 36 · 0% Book details