Sashe 109
Imaan Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read
*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah. Subscribe and read happily.Aunty tace "Daxu da kika fita baki kulle kofar bne Inna?" Inna na sharban kuka tace "Wllh na kulle Amina sai dai idan sabon makulli aka yi aka bude kofar..." Da mamaki Aunty tace "Ikon Allah, amma mu je dai a kara duba dakin Inna kila dai baki duba a nutse bane" a fusace Inna tace "oh oh Allah, Wani dakin xa aje kuma bayan nace maki duk na xaxxage kayan kwallan, wllh sacewa aka yi, kuma wannan barawon da ya san ni ne, yasan me nake ciki a rayuwa" Aunty na kokarin danne dariyarta tace "Gaskiya wannan abu da mamaki, anya ba Imaan din bace ta dauke kayanta kuwa??" Inna ta tsuke fuska tace "Don Allah Amina ki rabu da ni kiyi ta kanki, idan baxa ki fadi alkhairi ba kiyi hakuri ba don ni ba don Allah kiyi shiru, ta ina Imaan xata dauke waya bata gaya min ba" Tuni Mujaheed ya koma dinning ya xauna ya bude warmer yana diban abinci, Sallaman Abba yasa Inna ta mike tana matsar hawaye tace "Ahmadu yau an shafa min bakin fenti a gidan nan, ban san wanda ya shiga ya sace wayar da Bulasawa ya bani in ba Imaan ba, wayar tayi na miliyan Ahmadu, ka rufa min asiri mu tafi aje a sake dubawa, da wani idon xan kalli Bulasawa idan yaji labarin waya ya bata a wajena" Abba dake tsaye ya ma rasa abinda xai ce sai kallonta yake da mamaki, can dai ya girgixa kai yace "Wayar ta miye yaron ya kawo da ba mu da labari??" Inna ta wani hade rai tace "Ta imaan ce wayar ya kawo mata kyauta, kuma ta hannuna wayar ya biyo, ko an daina ihisani ne a duniyar?" Abba yace "Amma da ya bada ai sai ta kawo nan ta nuna min tunda shi Sadeeq bai nan, wannan bai kamata ba sam inna, a kan wani dalili ma xai bata waya??" Inna tace "Kaga Ahmadu kayi hakuri kar a shashantar da xancen bacewar waya mu tafi mu nemi waya duk inda ya shiga" Abba ya dinga kallonta, a fusace tace "Ahmadu kana kallona, don Allah ka shiga gaba mu je, idan ma ya kama a fiddo duk kayan cikin dakin sai a fiddo, yau dai xan ga batar nono a kirjin Budurwa" Kofa Abba ya nufa ta bi bayansa fuska a tsuke, Aunty ta fita ita ma, su Maimoon ma suka bi bayanta, Mujaheed dai cin abincin sa kawai yake a nutse, Umma da ta makale a kitchen, tana jin sun fita ta fito da sauri, duk ta hada xufa tace "Mujaheed, wani Bulasawan Inna ke nufi?" Mujaheed ya kalleta yana cin abincinsa a hankali yace "Ni ma ban gane xancen da take ba gaskiya" Umma ta tafi sama sai gata ta sauko da hijab xata tafi bangaren Inna, shi dai Mujaheed bin ta kawai yake da kallo har ta fita, Tana isa part din ta shiga parlon ta ga su Maimoon na ta fito da kaya daga cikin daki, Inna na tsaye daga gefe sai wurwurga ido take, Abba dai na tsaye daga bakin kofa ya rungume hannu, Aunty kuma na can uwar dakan Inna, Inna ta saki salati ta rushe da kuka tace "Kin ga ta kanki yau patuu, tunda uwata ta haifeni ba a ta6a ban ajiya ya bace ba..." Umma ta shigo parlon cike da damuwa tace "Wai har yanxu ba a ga wayar ba Inna?" Inna na goge hawaye tace "Wllh ba a gani ba Rukayya, ranan Ina bakin pampo ina gurje daudar wajen sai ga yaron ya shigo...." Umma tace "Wani yaro?" Inna tace "Bulasawa mana, waye bai san imaan da Bulasawa ba kuma a gidan nan, ba dai Bulasawan da kansa ba, d'an cikinsa ne dai, wllh yana bani wayar bayan ya fita kinga inda na ajiye wayar can" Umma ta kalli inda Inna ke nuna mata, Inna ta fashe da wani sabon kuka tace "Ni dai yau xan ga batar nono a kirjin budurwa ni Asabe" Umma dai ta kasa tsaye waje daya, Kai kana ganinta xaka ga tashin hankalin da ya ki boyuwa karara a fuskarta, Dakin Inna ta shiga ta gama xagaye xagayenta sannan ta fito tace "Kuma Inna babu kowa parlon San da aka baki wayar?" Inna ta d'an yi shiru sannan da sauri tace "D'an ki ne Mujaheed kadai a parlon a lkcn, Toh ga dankareren dankunnen zinari ma da ya bata ta bani ajiya bai bata ba, duk da ranan ba kowa a parlon ta bani, waya dai Mujaheed na wajen lkcn" Inna ta xaro ido ta dafe kirji tace "To ko dai sata Mujaheed ya fara a gidan nan ba a sani ba??" Umma dai sai hada xufa take tana kallon inna, Inna ta kalli Abba tace "Anya Ahmadu baxa a caji Mujaheed ba, wllh shine a parlon ranan, Ni dai na shiga uku na lalace" Abba dai bai ce mata komai ba, Umma ta dake tace "Inna bari in kashe gas na daura ruwan shayi, xan dawo yanxun nan, ae wannan babban magana ce" Inna tace "Yi maxa kar ki ja wata fitinar ba a gama kashe wata ba" da sauri Umma ta fita, tana komawa bangarensu bata ko kalli Mujaheed ba ta wuce sama jikinta na rawa. Washegari har Ammi ta gama soye soye a kitchen shiru imaan bata fito ba, dakinta Ammi ta shiga don ya ci ta fito ynxu ta gama shirin islamiyya, kwance Ammi ta ganta cikin duvet, ta cire duvet din tana kallonta ta kai hannu jikinta, janye hannun tayi tana kallonta tace "Imaan?" A hankali imaan ta bude idonta da ya rine tana kallon Ammi, Ammi ta xauna gefen gadon da damuwa tace "What's wrong imaan?" Da kyar ta nuna ma Ammi kanta murya can kasa tace "It's aching me" ta nuna ma Ammi kafafuwanta ma, Ammi ta dinga kallonta cike da tausayi tace "Kin daina shan maganin ki ko daughter!" Imaan ta girgixa mata kai kawai ta kasa cewa komai, mikewa Ammi tayi ta wuce bathroom dinta ta hada mata ruwan wanka ta fito ta daga ta, ita ta taimaka mata har xuwa bathroom din sannan ta fito, ta ciro mata kayan da xata saka sannan ta fita, Imaan na fitowa wanka ta kwanta kan gado daure da towel ta rufe jikinta da duvet, Ammi ta dawo dakin rike da cup din shayi da ledan bread ta ajiye kasa tana kallonta tace "Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani" Ganin she is shivering Ammi ta dauko cream dinta ta taimaka mata ta shafa sannan Imaan ta saka kayan da Ammi ta fiddo mata, shayi kawai ta sha da drugs dinta sannan ta kwanta Ammi ta fita da cup din. Aunty ce xaune parlon Abba bayan ta kawo masa breakfast, ganin mood dinsa tace "Don Allah ka daina damuwa da abubuwan inna, kun fa fi kowa sanin halinta, Bai kamata kuna sa abun a rai ba, kuma uwa ce fa" Abba ya girgixa kai yace "Ni kadai baxan iya dinga nuna ma Inna abinda ya dace da wanda bai dace ba, ya kamata ku ma ku dinga contributing...." Aunty ta sake baki tace "Mu a suwa Alhaji, ku ma ya ku ka kare balle mu, ai sai ta kora mu gidajen iyayenmu..." Abba yace "Wannan ba point bane, idan a nuna mata ta gyara ai da matsala babba, Dama ta fi sauraran Sadeeq to shi baya nan, ni kuma inyi magana ta fara min kuka, wllh duk abubuwa sun taru sun min yawa a kai" Aunty tace "Ai tana jin maganan Mujaheed ma" Abba ya kalleta yace "Toh cewa tayi a tafi Police station Mujaheed ne ya dauke waya, har da kukanta fa, Yanxu fisabilillahi maganan nan ya maki dadi?" Aunty ta kasa danne dariyarta tace "Tsufan kenan ai Alhaji, a dinga yi mata uxuri don Allah, Toh shi me Mujaheed din yace?" Abba ya girgixa kai yace "Ni ban ma gansa ba tun jiyan, sai daxu da muka hadu masallaci, gaskiya Inna na daga min hankali da yawa ban san yanda xan yi ba" Aunty tace "Toh Allah dai ya kyauta" Yusuf ne yyi sallama bakin kofa Aunty ta amsa ya shigo parlon ya mika mata wayarta yace "You missed a call" Abba na kallonsa yace "M.A fa?" Yusuf yace "Yana bedroom dinsa" Abba yace "Kira min shi ku taho tare" Yusuf ya amsa da to sannan ya nufi kofa, hanya ya ba Umma ta shigo parlon sannan ya fita, Daga Aunty har Abba suka dinga kallonta, duk gaba daya a sanyaye take tace "Alhaji xan je gidan Mariya wai suma ta dinga yi jiya basu yi bacci ba, yanxu haka suna asibiti tun asuba wai" Aunty tace "Subhanallahi, Toh Allah ya bata lafiya ya yaye ma duk musulmi ciwo, in sha Allah xan shigo anjima nima" da sauri Umma tace "A'a Hajiyar mu tace mu taho da ita zaria kawai, yanxu Ina xuwa Zaria xa mu wuce da ita" Abba yace "Toh Allah ya bata lafiya, ya sa kaffara ne" tana goge hawayen da ya cika idonta tace "Ameen" Abba yace "Da driver xa ku tafi kenan?" Umma tace "A'a adaidaita xan hau xuwa asibitin daga can sai mu tafi a motar mijinta" Abba yace "Toh Allah ya kiyaye hanya, do you need anything?" Tace "Ehh a min transfer din abinda ya sauwaka" Abba yace "Alright" sallama tayi masu ta fita parlon Aunty na mata Allah kiyaye hanya, bayan ta rufe kofa Aunty ta duba call din da tayi miss taga Ammi ce ta kirata, dialing number din tayi yana fara ring Ammi ta daga suka gaisa, Ammi tace "Dama tambaya xanyi ko driver na nan Hajiya..." Aunty tace "Ehh toh bai dawo daga kai su Maimoon islamiyya ba..." Ammi tace "Toh dama Imaan ce bata ji dadi ba xa mu je asibiti" Aunty tace "Subhanallahi tun yaushe?" Ammi tace "Yau dai da ciwon nata ta tashi" Aunty tace "Toh bari in ma Yusuf magana ko shi sai ya kai ku asibitin" daga haka ta katse wayar, Abba yace "Mamana ce ba lafiya?" Aunty tace "Wllh kuwa, Wai ciwonta ne ya tashi" Abba ya d'an yi shiru sannan yace "Bari Mujaheed ya shigo mu ji ko xa a kaita asibiti ne ko a bata medication a gida" dai dai nan Mujaheed ya shigo tare da Yusuf, Abba ya mike yace "Mu je ka duba Mamana wai bata ji dadi ba" Mujaheed ya d'an yi jim, sannan ya bi bayan Abba suka fita parlon, Aunty na kallon Yusuf tace "Kai baxa ka je dubata ba" Yace "Xan je anjima mum" Har bedroom din Imaan Abba da Mujaheed suka shiga Ammi dai ta tsaya daga bakin kofar, bacci take suka sameta, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali yana kallonta ya kai hannu forehead dinta, bude ido tayi ganinsa ta ja duvet ta rufe kafarta da sauri. Abba ya karasa kusa da gadon yace "Sannu mamana, ya jikin?" Da kyar tace "Da sauki Abba" Mujaheed na kallonta yace "Where are you feeling pains?" Ba tare da ta kallesa ba ta nuna masa kafafuwanta da baya, yace "Kin sha magani ne?" Kai ta gyada masa, Yace "Ina drugs din" ledan maganin dake ajiye ta nuna masa ya dauka ya duba su sannan ya ajiye yana kallon Abba yace "Let me get some injections da drugs" Abba yace "Ohk" daga haka ya nufi kofa Ammi ta basa hanya ya fita. Abba na kallon imaan yace "Allah ya sauwake imaan" ta d'an yi murmushi a hankali tace "Ameen" Abba ya juya ya nufi kofa yana kallon Ammi yace "Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen thumma Ameen" yace "Amma kada a gaya ma Inna" Ammi tace "In sha Allah" kofa ya nufa yace "Xan fita office, I will call later" Ammi tace "Allah ya kai mu, Allah kuma ya tsare" yace "Ameen" sannan ya fita parlon. Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon imaan tace "In kara hada maki shayin ne?" Da sauri ta girgixa kai, Ammi ta dinga kallonta sannan ta juya xata fita, murya can kasa tace "Ammi don Allah ki shafa min maganin a kafa kafin Yaya ya dawo ni bana son ya shafa min"