← Book details Idan Kaya Ya Gaji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 46

Sashe 45

Idan Kaya Ya Gaji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina tunanin da ba dan bansan wanne iri bane shi dana amshi tayin Maigogul.

Abu
ayane yake sani tunani da tsoron komawa gidan jiya.

Nasan abune mai wuya in ba mazinaci bane tunda har Maigogul ya sanshi.
ila mata yake kai musu tunda yace abokin cinikaiyarshi ne.

To inma nace ba shi
in ba waye zai aureni wai?

Bana tunanin akwai nutsattse kamammen da zai iya neman aurena in dai gaskiya zamu fa
ama kanmu tunda ubanmu ma kawaline.

Sannan maza da yawa suna cikin harkar zinace_zinacennan in dai zai ri
eni da mutunci ba gara in aureshi ba me ku kuke gani amma?

In kuma na tuno da ku
urar Allah sai in ji a raina nagartaccen miji kintsattse yananan zuwa lokacine bai ba.

Tunda Allah ya sani na tuba nayi nadamar gabaki
aya ma rayuwata ta baya wallahi Allah kenan.

Dan na gaji da irin rayuwar gidanmu Allah ya sani so nake in nesanta dasu sosai ko zam samu nutsuwa a rayuwata.

Kuma nafi
aunar auren gudun sake tsundumawa rayuwar dana tsinci kaina a baya.

Lumshe idanuna nayi a hankali banfi minti goma da rufewa ba bacci ya kwasheni.

Maigogul
Suna shiga ya cire babbar rigarshi ya fa
a ban
aki yayo wankanshi ya fito daga shi sai wandon shaddarshi da tawul a wuyanshi.

"Uzairu zuchiyata kirasu a waya su kawo mun farfesu mai zafi in sha ni fita zanyi."
Uzairu zuchiyata daya
yafe a gado yana waya da Felisha ya gya
a mishi kai tare da
aura yatsanshi a saman lab
anshi ma'ana yayi shiru.

Shiru Maigogul yayi harda kama bakinshi.

Zama yayi a kujera ya ciro manshi ya shafa ga shadda ya zarota ya kintsa tsab wanka iyakar wanka ya feshe jininshi da turaruka masu
amshin da
i ya
arama yatsanshi zobe guda
aya mai ba
in dutse kasancewar agogon hannunshi cikinshi ba
ine yana son kwalliyar ta fita da kyau.

Uzairu zuchiyata saida ya sallami Felisha kana ya kira Hotel ya fa
a musu sa
on Maigogul cikin minti sha biyar suka kawo farfesun naman akuya lafiyayyen gaske suka dire mishi yana ci yace.

"Uzairu zuchiyata ka shawo kan Lolo ta amince da batun dana kawo mata sabida naga tafi su A'isha wayewa ne kuma turancinma babu laifi tana kwaci
awa shi yasa nayi mata wannan tayin fa.
arshe in nace su Labbai zan bashi kaga harkar ta lalace kuma Lolo ce zata samu samunta ya zama namu babu kokonto.

Wallahi ta aureshi munfa yi bankwana da talauci fa, gaka zaka auri baturiya kaima kaga fa harkar kawalcinma sai in dena Alhaji ya bani jari ko na motocine in dinga zuwa kwatano ina shigo dasu tunda a baya mun
an ta
a harkar"
Uzairu zuchiyata yace.

"Wai Maigogul kai ko wacce sana'a kayi ta ne?"
Dariya yayi mishi kamar bazaai magana ba saida yasha romo sosai kafin yace.

"Hmm har kwasar kashi nayi.

Uzairu zuchiyata har angola munje munyi kasuwanci abunne ya
i kar
armu shi yasa muka koma harkar kawalci kuma muka shigeta da
afar dama shi yasa bana wasa da aikina.

Har a cikin kwata mun kwana.

Ni dai dan Allah tunda Lolo
awarka ce kama za
eta sama dani ubanka to ka shawo mun kanta ko Allah yasa makkannan mu sake komawarta."
Da haka Maigogul ya gama shan farfesunshi ya saka kanshi ya fice.

Uzairu zuchiyata kuma ya koma dakin Lolo.

SABUWA:.

Ina baccina Uzairu zuchiyata yazo ya tasheni da bugun
ofa jiki a mace na tashi naje na bu
e mishi.

Saida muka yi Sallah yayo mana odar lafiyayyen abinci muna ci ne yace dani.

"Lolo in kikayi la'akari da gidanmu da irin mazajen da
an uwanmu suke aure ni sai inga kamar riba zaki
irga.

Ga shawara kyauta wannan Alhajin ta
angarenki ki amince dashi ki barma Maigogul sauran.

Ni dai shawarar da zan baki kenan a ta
aice.

Kinga nima abinda zai fissheni nayi kina ganin shekarun dana kwashe ina neman irin abinda raina yake so da sannu ba gashi kusan nakai ga cimma abinda nake so ba?"
To zanyi nazari akai kafin mu dawo zan yanke hukuncin amincewar ko akasin hakan"
Mardiyya na kira a waya ta ha
ani da su Malama a waya duk muka gaggaisa suna makarantar islamiyya lokacin suna jiran Babansu ya gama ya
aukesu su koma gida.

Nan na fa
a musu zamu yi tafiya ni da Uzairu Zuchiyata zuwa
asar canada su taya mu adda'a.

Uzairu zuchiyata yayi carab ya fisge wayar.

"Mardiyya da bakinku na karatu mai albarka ki ro
a mana Allah yasa in samu nasarar abinda zai kaimu.

Ita kanta uwar taku ku sakata a adda'a"
Mun
an jima muna waya tana fa
a mun matsalolinsu ni dai a kullum abinda nake cewa dasu suyi ha
uri duk runtsi su dinga tsayama junansu suna gani duk lalacewar gidanmu muna iya tsayama kanmu a kan duk wani abu duk girmanshi.

Gaga_gaga washegari tun
arfe goma muka fito zuwa Airport sai
arfe uku jirginmu zai tashi amman ana jiye mana turmutsutsun dake titin Lagos shi yasa aka bamu shawarar mu tafi da wuri mu jira lokacin a Airport.

Mun fita tun goman amman sai karfe
aya muka isa Airport sabida turmutsutsun titin Lagos ( go slow) kai tsaye muka wuce inda ake duba kaya a na'ura domin tantanewa.

Sannan muka wuce wajen jira ga kujeru nan sha
e da mutane.

A wata kujera muka zauna da wasu mata da miji.

Maigogul kuma na kusa da wani Alhaji ya zauna shima ya tsa
a kwalliya.

Hannu Maigogul ya mi
a mishi suka gaisa daga haka ya soma yi mishi surutu kai kawai na girgiza.

Muna zaune aka kira fasinjar Dubai duk suka.

Mi
e suka hau kan layi in suka mi
a takaddar hannunsu aka duba sai su bi wata
ofa su fita a haka har suka
are.

Sallahr azahar muka yi muka dawo
Uzairu zuchiyata nifa yinwa nake ji.

Ya kamata mu nemi abinda zamu ci gaskiya.

Kai kaga Maigogul ya samu mutum sai surutu kawai yake ta zuba mishi babu kamun kai babu komai"
Baki Uzairu zuchiyata ya ta
e kawai.

"Kinga ga wani windo can muje muga me suke dashi ko zamu iya siya kinsan Airport kayansu tsada ko ruwane"
Kafinma mu mi
e Maigogul ya iso inda muke.

"Lolo muje sama akwai gidan cin abinci wannan bawan Allahn da muke tare dashi yayi mun tayi zuwa cin abinci shine nake fa
a mishi tare da yarana nake."
Kallonshi nayi na bi bayan Alhajin da kallo da yake kan
afar bene yana haurawa.

Jikina a sanyaye nabi bayansu har zuwa saman ni da Uzairu Zuchiyata teburinmu daban, Maigogul da Alhajin teburinsu suma daban ga jama'a anan
aiku suna zaune suna cin abinci.

Dafadukan soyayyar shinkafa mai
auke da kayan lambu wadatacce aka kawo mana da kaza akai muka ci muka
oshi muka kora da lemun limka na kwalba.

Godiya muka je muka ma wannan Alhajin.

"Wannan sunanta Sabuwa
ar gaban goshina kenan yarinya
ar albarka mai tausayi.

Ta rabu da mijinta tana da yara hu
u.

Wannan kuma wanta ne Uzairu zuchiyata"
Da sauri muka katse Maigogul ta hanyar sake yima wannan Alhajin godiya gudun kada Maigogul ya sakar mana
era a yayi.

Ai kuwa sai muka ji an soma sanarwa a amsa kuwa cewar fasinjan Canada su hau layi jirginmu yana jiranmu.

Sakkowa muka yi cikin hanzari zuwa
asa muka shiga layi.

"Sabuwa Uzairu zuchiyata ni zan koma zamu ha
u a Lagos ranar da zaku dawo zan tawo in tarbeku.

Duk abinda na baka ka tabbatar kayi amfani dasu kada kayi mana asara"
Alhajinnan yana bayan Uzairu zuchiyata sai ya dube ni yayi mun murmushi ni ina layin mata.

Na lura tun muna wajen cin abinci yake ta mun murmushi.

Kaina na sauke kawai.

"Alhaji ni zan nufi jigawa kuma in babu damuwa ka bani lambarka mana"
Cewar Maigogul yana dariya.

Katinshi ya zaro a ajjihu tare da littafin rubuta ku
i ( check) ya rubuta ma Maigogul ku
in da mu bamu san nawa bane Maigogul yaita runtuma godiya ya nufi hanyar fita.

Da ido kawai na bishi yadda yake tafe bagajan_bagajan ina juyowa muka ha
a ido da Alhajinnan fuskarshi dai
auke da murmushi da wani irin kallon tsan da yake yi mun.

A haka dai har muka fito aka duramu a bus zuwa bakin jirgi duk muka shiga kowanne ya zauna a inda lambarshi ta fito.

Idanuna a runtse har saida jirgi ya saisaita a sararin samaniya kana na bu
e idanuna na sauke ajjiyar zuchiya wai yau mune a jirgi zamu tafi wata
asar Allah mai yin yadda yaso.

Tafiyar ashe ba tafiya bace mai sau
i ba.

Wasane_gaskene saida muka yi tsawon awanni goma sha bakwai a zaune.

Muyi bacci mu farka, muci abinci, muje muyi fitsari haka dai haka dai bamu muka iso Canada ba sai wajajen
arfe takwas na dare.

Tafiya yankin azaba wai damma jirgi akwai da
i babu gajiya babu galabaita sam.

Hannun Uzairu zuchiyata na ri
e gam dan wallahi Allah ina sauke
afata a
asa bayan mun sakko daga
afar benen jirgin sai naji tsoro ya kamani.

Jakata Uzairu zuchiyata ya ri
e mun sai dariya yake yi mun.

"Lafiya Uzairu zuchiyata wani abunne ya samu shalelen Baba?

Naga ka ri
eta ga jakarta ka ri
Cewar wannan Alhaji da muka shiga jirgi tare.

Kaina kawai na sauke Uzairu zuchiyata yace dashi.

"Babu komai rigimace kawai Alhaji"
Sai ya
anyi dariya irinta dattijai.

Mu dai muna ta bin mutane a baya a baya har muka shiga wata
ofa.

Ananne akwatunanmu suke suna yawo akan wani
arfe mai sulu, in jakarka tazo gabanka Sai ka zare, in kayi sanya ta wuce saita sake dawowa zaka
auka.

Uzairu zuchiyata ne ya
akko mana akwatunanmu wannan Alhaji yana biye damu
afa da
afa.

Uzairu zuchiyata ya zuge jakata ya ciro tabarau ya saka, ya feshe jikinshi da turare ya saka namijin goro a baki sabida ya
auke mishi bashin da bakinshi yake yi.

Muna shiga wata
ofar tangaran sai muka jiyo ihu daga can nesa na wata baturiya da fararen fulawowi sha
e a hannunta har tana kuka.
Chapter 45 · 0% Book details