← Book details Idan Kaya Ya Gaji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 46

Sashe 26

Idan Kaya Ya Gaji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman yanzu me ake ciki dangane da makomar auren naki?"
Adama ce ta basu labarin na sake shigar da wata
arar harma an kaima Babangida sammaci.

Gaza yace.

"Bana wallahi in dai Babangida bai bini a hankali ba saiya rasa rayuwarshi.

Nifa Lolo da zaku yarda sawa zanyi a kamosho in saka mishi wu
a a wiyanshi wallahi sai ya sake ki.

Ko in kasheshi kya yi idda ne ko takaba oho dai.

Uban kowa ya huta.

Su su Maigogul babu abinda suka saka a gabansu sai son kudi.

Ku duba yadda duk muka zama
a duk babu na gari"
Rahama ce tayi carab tace
"Gara ka bari abi matakin Shari'a tukunna.

Yaci albarkacin ubanshi da
anshi Gaza.

Na ro
eka kada ka aikata abinda zaka sake komawa gidan yari ga madamsy nan ka barta da wa?"
"Ahh in barta da Allah mana.

Wai ke Rahama an fa
a miki tsoron gidan yari nake yi?

Naci dubu wallahi sai ceto.

Wallahi ke wuya a Lagos wuya a kwatano, wuya a tafa wuya a mararraba, wuya a shagamu fa."
Madamsy ce ta shiga yi mishi kirari yana
ara botsarewa da
yar suka harha
u aka bashi ha
uri daya tsaya abi matakin kotu tukunna in hagu ta
iya a wannan karon dole ayi dama.

Ni dai da ba da
in jikina nake ji ba na mi
e na fito ni dasu Labbai zamu koma can
akinsu.

"Lolo zan samu dubu uku a hannunki zanyi ku
in motane wallahi kun ganni ba
i zanje tasha in taro zan kaisu ges house
an ku
en jikina dasu nayi girki."
Maigogul ke magana yana gaban murhu yau dai shi yake girki a gidan duk da ba wani sabon abu bane.

Yayi gwafe_gwafe a gaban wuta jallof sai
amshi take zubawa wallahi saida yawuna ya tsinke"
To zan aiko maka dashi"
"Allahu Akbar kaga
ar albarka wacce aka haifa tsiya na bacci.

Lolo ta Maigogul Allah yayi miki albarka.

Ba zaku tsaya kuci abincin nawa bane?

Duk da ba
i na dafama.

Bari in zubo miki ke ka
ai zaki samu arzikin cin abincinnan Lolona uhm bana so kina damuwa Lolo kin ganni nan Hamsha
in garna
in mai ku
i nake miki fatan ki aura.

Lolo kika auri mai ku
i dani zaki tafi ai bazan iya zama ba"
Ya tashi harda
an gudunshi ya zari kwano a kwando ya zuba mun da dama kuwa ga nama an yayyanka
anana abinci sai
amshin kori yake yi.

Hawayene masu zafi suka zubo mun daya tawo da sauri ya bani kwanon.

Madadin in amsa sai na fa
a kafa
arshi na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuchiya.

Shiru Maigogul yayi yana ri
e dani da hannu
aya ga abinci a
ayan hannun nashi.

"Aikin banza da wofi yanzu nan har Ma
igogul ya kai irin wannan uban a wajenki Lolo?

"
Cewar Rakiya.
agoni yayi yana share mun hawaye da gefen malum malum
inshi yana wani irin murmushi.

"Lolo kiyi ha
uri ki dena yawan kuka ni Maigogul ina tare dake har abada.

Zaki yi albarka zaki samu rayuwa mai kyau a gaba.

Amshi abincinki kije kici ki
oshi"
Amsa nayi na kalleshi muka yi murmushi.

Sai kawai ya amshi kwanon ya sake zuba mun abincin na kar
a na fita Rakiya sai shewa take yi.

Da muka isa
akin su Labbai saina bu
e kayana na zaro dubu shida naba Sadiya ta kaima Maigogul dubu hu
u Rakiya dubu biyu.

Abincin daya bani kuma nasa su Mardiyya a gaba suka ci.

Saida suka gama na aiketa ta siyo biredi suka kara da shayi.

Ganin lokacin shan maganina yayi ne yasa nima na sha shayin na warwatsa magungunana na jingina da bango ana
an hira ina saka baki sabida in
warara kaina.

Hmmm wajajen hu
un yamma muka jiyo sallamar yaro wai ana sallama da Sabuwa inji wani mutum a
ofar gida.

Ina kyautata zaton Yaya Kamilu ne.

Wanka na fito da sauri na soma saka kayana.

"Mardiyya kije ki ce ma mai kirana ganinan fitowa likitane shi ya taimakeni a asibiti kuma shi yaita biyan komai na maganina"
Na fa
a mata ne tun kafin su zargi wani abun su soma tuhumata ko in bar
walensu da hasashen da bansan wanne iri bane.

Fita tayi a nutse nima na samu zarafin shiryawa na zura hijabina na ja hannun Malama muka fito.

Ai kuwa shi
inne yana jingine a bakin motarshi Mardiyya na gabanshi yana mata tambayoyi tana amsawa na isa da sallama.

"A_a Sabuwa har kin warware an shiga cikin
an uwa ko?"
Dariya nayi mishi kawai.

Ya yafito Malama halamun taje.

Sakinta nayi taje suka gaisa yake tambayarta ita izufinta nawa tunda yaji Mardiyya tayi sauka"
"Sabuwa ashe yaran namu malamai ne dan ko ni babu sittin a kaina akwai dai arba'in."
Murmushi kawai nayi Mardiyya ta kama hannun Malama zasu koma ciki yaa kirayi sunanta.

"Mardiyya tsaya ku shigarma da Ummi kaya"
Both ya bu
e ya zaro manyan fararen ledoji ya mi
a mata.

Tana kan kar
a na hango Babangida yana daidai
ofar gidanmu yana tawowa idanunshi a kaina
Har su Mardiyya suka shige bai
arasoba.

Isowarshi ke da wuya sai cewa yayi
"Sabon farka kika samu shine kika yi
aryar kurumcewa kika gudu kika bar gidan aurenki da yaranki, kika tafi kika barni da kewarki da tunaninki ashe?

Malam dan abu ta kazan ubanka...

Bata fa
a maka tana da aure bane?

Ko da yake son zuchiya bazai barka ka tuno wannan ba.

Nine mijinta wanda zamu
are rayuwarmu tare"
Kawai saiya cukume Kamilu.

"Ki shige gida Sabuwa wallahi ko in miki dukan tsiya na rantse tunda baki da mutunci matar
addara maras kamun kai ko ki koma ciki ko ni dashi muyi mutuwar kasko wallahi"
Kamilu yace.

"Sabuwa shige gida abunki zanyi mishi bayani"
Ina Babangida da dambe ya kama Kamilu Ni Ko nasa hannu aka na kwarmata ihu dan na fahimci Babangida ranshi yayi mugun
aci sosai yafi
arfin Kamilu.

Ai kuwa jama' a kamar jira suke yi suka fiffito ciki harda su Adama.

"Tabb Lallai Babangida abun naka yakai
Labbai maza kirawo Gaza yazo ya raba wannan fa
Ina gefe ina kallo kukanma ya
i zuwa mun dan nasan bama a soma komai ba.

Ina bu
e idanuna na hango
ar Shuwa na tawowa wajenmu.

Gaza kuwa a guje ya tawo matarshi na biye dashi.

Su Rakiya ma sai gasu afujajan babu ko mayafi.

Yana isowa yasa hannu ya
are Babangida a jikin Kamilu fa
a ya koma a tsakaninsu.

Babangida ya naushi Gaza 'Gaza ya rama.

"E lallau yau sau nayi ajalinka wallahi wai ni ka fasama baki Tabb yau zaka gane waye Gaza"
a ya zaro kamar
ibtawar idanu ya yanki Babangida, Babangida idanunshi sun rufe da kishi sai tijara yake yi.

Madamsy ce tayi saurin shiga tsakaninsu.
ar Shuwa ganin jini na fita a jikin Babangida yasa ta dinga danna ihu kowa da kowa ya fito.

Da
yar fa
an ya lafa da taimakon mutane, da taimakon su Rakiya da suke ta cakume Gaza.

Maigogul dai baya nan.

Sun sha naushi in nausa da Babangida sosai shi kuma Gaza ya yayyankeshi a waje kusan hu
u ga jininshi nan kaca kaca.

Kamilu yana ri
e da hannun Gaza ga dattijai anata bashi ha
uri.

"To naji amman ya bar unguwarnan kuma kada ya sake zuwa layinnan da sunan zuwa wajen
anwata wallahi ko yaranshi na gani sun zo gidanmu saina illatasu.

Ai kai
aramin dan abu ta kazan ubane mu iyayenka ne yaro a iskanci."
Babangida na
aure hannunshi da
an kwalina daya fa
i yace.

"A fito mun da yarana to.

Kuma wallahi ko mutuwa kuke yi kuna dawowa Sabuwa tawace ina son matata sonta a jinin jikina da jijiyoyina suke yawo bazan saki Sabuwa ba sai dai duk abinda za'ayi ayi
Kai kuma wallahi bazan ta
a yafe maka hakkina a kanka ba."
Gaza sai ihu yake yi ganin matarshi shi ya hana ya kai Babangida
asa.

Labbai ce ta tarkato yaran ta turasu gabanshi.

Shine ya ja hannayensu suka bar layin.

Gaza ya ja hannun matarshi suka tafi.

Su Rakiya suka bishi Rakiya sai
ebo zagi take tana dura ma Gaza.

Shi kuma yana fa
a yana sake rantsuwar fa
anma yanzu aka soma.

"Kinga
anwata kiyi ha
uri zuwanane duk yaja wannan abun.

Ki shiga gida ki tabbatar baki
auki damuwa kin
aura ma kan ki ba.

Kinsan ba lafiya gareki ba.

Ashe Babangidan naki mahaukacin zaki ne.

Duk da naga halamun makauniyar soyayyar da shi kanshi bai gane soyayya bace a tattare da amonshi ba, amman tabbas yana mutuwar sonki.

Ki je zamu yi waya kinji ko?"
Kai kawai na
aga Adama ta ja hannuna muka shige ciki.

Naci kuka kamar raina zai fita har saida ciwo ya bigeni sai Dr Kamilu Adama ta kira bai jima ba ya dawo yaita rarrashina yana bani kalma har dai raina ya
anyi sanyi amma fa ba sosai ba gaskiya.

Babangida:.

Yana tafe su Mardiyya na binshi a baya ya ri
e hannunshi da
ankwalin Sabuwa wanda ya ji
e da jini sharkab.

A guje
ar Shuwa ta biyosu lokacin har sun hau abun hawa.

"Baban faty ashe dama zaka iya zuwa wajen Sabuwa matar da tabi tsohon saurayinta.

Bayan data dawo kuma ta wuto gida kai tsaye.

Inaga dai bokancin Sabuwa da mahaifinta yayi tasiri a kanka dan bokace ita da ubanta nasan baka san wannan ba"
Kallonta a matsayin mahaukaciya Babangida yake yi.

Idanunshi a mugun rine ga yaranshi jikinsu duk yayi sanyi .

"Malam ja abun hawannan mu tafi kaji ba hankali bane da'ita"
ar Shuwa tace.

"Tafiya zaka yi ka barni wai?"
"Ke in kinga dama kema kiyi zamanki a gidanku.

Ba Sabuwa ba ko wacce macen ma ta fice mun a raina gayyar tsiya"
Da fa
a yake maganar dan a mugun hasale yake.

Fuu abun hawan ya wuce ya bar
ar Shuwa tana she
a dariya a titi.

"Ai wallahi Babangida ko tsirara zanyi yawo dolen dole saika rabu da Sabuwa har shegiyar
arta sai ta bar gidanka domun ba Yarka bace.

Ai tunda Sabuwa ta kwace mun Khalid to dole ta rabu da Babangida.
Chapter 26 · 0% Book details