← Book details Idan Kaya Ya Gaji Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 46

Sashe 20

Idan Kaya Ya Gaji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman kafin ta rufe baki Mustapha ya dawo.."Mardiyya ku tattaro mu tafi a kaiku gida"
Labbai tace
"Na zaci za'a barsu anan na
an wani lokaci ai?"
Rakiya tace.

"Su tafi maza.

In aka barsu Hala ke zaki
auki nauyin basu abinci ko?

Komu da Allah ya kawo mu wayewar garin yau munyi farin ciki da muka ga yau da rayuwarmu ruwane ka
ai amman a gidannan muma shi zamu kamfata kowa ya kama gabanshi.

Gidansu da gidan kakaninsu akwai abinci suje can su
arata.

Ita kanta uwarsu dadine yayi mata yawa dan banga haka a gidan ubanta ba.

Kinsan in da
i yaima mutum yawa sai yace Allah ya kasheshi ya huta."
Kai Mustapha ya girgiza ya tarkata kan yaran suka fice.

Babangida fa jiki yayi tsanani dauriya ce kawai da addu'o'in da yake ta jerowa yasa ya kai war haka.

"Kaini asibiti Mustapha yaran sai a mayar dasu gida wajen Aisha ko Ramatu.

Mardiyya mamanku bata fa
a miki inda zata je ba, ko kinji tana waya haka?"
"A_a Baba bata fa
a mun komai ba.

Abinda na sani shine jiya bata ko magana har muka dawo daga islamiyya "
Ido ya lumshe kawai yana dafe da kanshi har suka
arasa asibiti.

A
ofar asibitin suka ga Kawu manga da matan su wawo isowarsu kenan.

"Mustapha ya zamu yi da naso ka rakani asibitin inaso inga Khalid ne?"
Shiru Mustapha yayi yana tunani can kuma sai yace.

"To yanzu abinda za'ayi muje mu duba Malama Babba sai mu futo mu sauke yaran in yaso sai mu wuce."
Fitowa kuwa suka yi dukkansu.

"Ai ga Babangidan ma ya iso"
Cewar Safiya matar Bashiru.

A tsanake ya isa wajensu aka gaggaisa duka.

Kawu manga yace.

"Ina ka shiga Sa'a ta kirani a waya ta kawo
arar baka kwana a asibiti ba?"
Kafin yace wani Abu su Safiya suka wuce tare da yaran zuwa ciki.

Wajen ya rage daga Kawu manga sai Mustapha sai shi mai gayyar.

"E ban kwana a asibiti ba gaskiya "
Kura mishi idanu yayi kafin yace.

"To me yasa?"
"Sabuwa ce akai mun waya jiya da daddaren wai ta gudu.

Wannan dalilinne yasa na bar asibitin.

Tun jiya muke nemanta cikin dare har izuwa safiyar yau babu labarinta.

Yanzu ma nazo in duba jikin Malama ne inaso Mustapha ya rakani mu kai report ofishin
an sanda, mu ba da cigiyarta a gidan TV "
Kawu manga shiru yayi baice komai ba.

Bai kai ga cewa uffan ba su Wawo suma suka iso asibitin tare da dukka mazan gidan baki
aya.

Nan aka shiga gaggaisawa nan kuma suka dunguma zuwa ciki.

Bibbiyu bibbiyu ake shiga sabida bazai yiwu su shiga fin haka ba.

Kuma da sun fito sai su nufi hanyar waje, dan tsaiwar ba zata yiwu ba sabida yawansu.

Babangida sai kallon su Mardiyya yake yi da suke zaune a takure a kan benci.

Mardiyya itama uban nata take kallo ta saka fuskar tausayi.

Sai da ya rage saura Babangida da Mustapha ne ka
ai a tsaye suna jiran Kawu Manga ga Wawo su futo su su shiga shine ya dubi Malama Babba ya mi
o mata hannunshi.

Allah sarki yarinyar ta taso ta ri
e hannun Baban tana mishi murmushi.

Sai yaji tamkar hawaye zasu sakko mishi.

"Mardiyya ku kun shiga kun duba jikin Malama ne?"
A sanyaye yayi maganar linkib da rauni.

Itama a sanyayen tace.

"Bamu kai ga Shiga ba Goggo Sa'a tace kar mu shigo bata son ganinmu shine nace musu mu zauna anan"
Wani irin abune ya soki
irjinshi jin abinda Sa'a ta fa
ama yaran.

A zuchiyarshi sai yafi ganin lefinshi da bai tabbatarma da
an uwanshi cewar su Mardiyya sunfi mishi ko wanne yara soyuwa a zuchiyarshi ba.

Sai yasa
afa ya shure yaran yake nuna musu
iyayya duka hantara, kyara duk shi ka
ai.

Baima kamata yaga laifin Sa'a ba sam.

Sai dai yayi tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya siyo musu martaba da kima a idanun duniya baki
aya.

Isowar su
ar Shuwa da Ramatu, da Sauban ne ya dawo da Babangida daga cikin hayyacinshi.

Wawo na fitowa Babangida ya ja hannun Mustapha suka shiga ciki.

Malama na kwance amman idanunta biyu.

"Sannu Malama ya
arfin jikin naki?"
Kai ta
aga da hannunta halamar da sau
i.

Babangida tsoro ya shigeshi yace.

"Yaya Sa'a Malama bata magana ne?"
"Da tana yi ai da tayi.

Kai da kake son ma ta mutu ka huta?

Saboda fasi
ar matarka ta gudu tabi namiji shine dalilin da zaka fice a asibitinnan babu ko sallama ga mahaifiyarka kwance babu lafiya silarka.

Ita dai wannan soyayya da Malama take nuna maka bata da wani amfani ma tunda ka kasa tsaya mata a lokacin da bata da lafiya "
Kallonta Babangida yayi.

Ya dubi Malama Babba da take
aga ma Sa'a hannu akan tayi shiru.

"Lafiyanki
alau kuwa Sa'a da irin wa
annan maganganun da kike fesarwa a gabana.

In a gaban Yayane kin isa
ago kaima bare har ki dinga wannan kalami haka?

Dame kuke so mutum yaji ne.

Babangida inya tsaya a kanku shine samun lafiyarne koka sai akayi Yaya?

Duk lalacewar Sabuwa ai matarshi ce Uwar manyan yaranshi dole.

Sannan kufa sani Sauban ne zai auri Mardiyya fa"
Shiru Babangida yayi yana nazari.

A yanzu ne yake jin in sama da
asa ha
ewa zata yi bazai bari Sauban ya auri Mardiyya ba.

A yaune ya gano zata rayune cikin
unci da tsangwama
ila har a wajen Sauban
in.

Yafi taje waje ta auri bare ba Sauban ba.

"Kayi ha
uri Kawu Manga bazan sake ba."
Ya jiyo muryar Sa'a tana ba da ha
uri.

Kawu manga yace.

"Babangida muje daga waje in ganku tukunna"
A baya suka bishi zuwa waje.

Sauban na zaune a kusa da Mardiyya suna hirarsu cike da girmama juna.

Kuka ma take yi shi kuwa ya rage murya sai aikin rarrashinta yake yi.

Ganin futowar Babangida ne yasa su
ar Shuwa da Ramatu suka tashi.

Gaishe da Kawu manga suka yi tare da tambayar mai jiki.
ar Shuwa ta
aura da cewa.

"Ashe da abubuwan da muka tashi kenan.

Naji labarin Mamansu Mardiyya ta tafi wajen khalid tunda Baban Mardiyya ya
i sakinta"
"Ke baki da hankali ne kinsan abunda kike fa
a kuwa?'
Matsowa yayi gabanta cikin zafin nama kamar zai kifa mata mari.

Take fa har hawaye ya taru akan fuskarshi.

Kawu Manga ne yayi saurin ri
eshi ya dawo baya.
ar Shuwa ba
aramin mamakin yadda Babangida ya birkice tayi ba.

Duk da zuchiyarta a cike take da farin cikin tayi nasara akan Sabuwa, sai da taji kishin yadda Babangida kishin Sabuwa ya baiyana
arara a abinda ya aikata mata kuma taji ciwon hakan.

"Assha Babangida ashe dai baka dena halinka na dukan mata ba wai?

Ke kuma Aisha menene wannan wacce iriyar magana kike furtawa haka ke haka ta fa
a miki wajenshi zata je?"
A zuchiyarta tayi murmushin mugunta ta kuma samun wata dama.

A zahiri sai ta sau fuskar tausayi tare da cewa.

"Ayi ha
uri Kawu manga amman yadda Sabuwa take da Khalid ba zata ta
a iya rayuwa babu shi ba.

Shima Baban Mardiyya baisan tsakanin su bane nice nasan komai shi yasa nace haka amman ayi ha
uri tunda maganar tayi zafi"
Idanu Babangida ya rufe yana jin juwa tare da wani yaji a idanunshi.

Allah yasa ma su Mardiyya tuni sunyi gaba da a gabansu za'ayi wannan abun.

Mustapha da yasan ha
anin irin kishin Babangida babu shiri ya ri
eshi dan ya fuskanci yana cikin mawuyacin hali.

Kawu manga yayi kasa
e yana kallonta kafin yace.

"Allah ya kyauta ku shige kuje kuyi abinda ya kawo ku.

Kai kuma kuzo mu tafi"
Har suka shiga mota babu wanda yayi magana.

Wawo da yaga tahowarsu Kawu manga ya bu
e mishi mota sai yaga ya shige motar Mustapha.

Karasowa bakin motar yayi.

"Wawo ku ku tafi wajen nema.

Zamu je wani wajennne da su Babangida."
"To shikenan yaran ma dasu za'a tafi ko su fito in ajjiyesu a can gida?"
Kawu manga yace.

"A_a barsu tare da ubansu kai dai jeka Allah yayi albarka"
Saida suka hau titi kafin Kawu Manga yace.

"Mu je can wajen nashi a asibitin Dan ba ace an barku ku ka
ai kunje za'a iya yin
atacciya."
Har aka iso babban asibiti Babangida bai bu
e idanunshi ba saida Mustapha ya dafa kafa
arshi kana ya bu
e idanunshi da suka zama tamkar garwashi ko kuma tasshi dan ja.

Sakkowa yayi ya yafuto Malama ta futo.

"Mardiyya ku jiramu muna zuwa ko?"
Ya fa
a yana gyara ri
on da yaima Malama.

Da tambaya aka kawosu har bakin ofishin Khalid.

An kuma ci sa'a ma yananan.

Izinin shiga aka basu suna shiga Malama ta saki hannun Babanta ta isa wajen Dr Khalid tana dariya halamun ta sanshi tayi sabo dashi.

Tsawar da Babangida ya dako mata ne yasa ta dawo da sauri ta ri
e hannunshi da suke ta rawa.

Illahirin jikin Babangida rawa yake yi.

Kenan yaranshi ma sun sam Khalid kenan.

To Sabuwa ko dai tana shigo da Khalid gidanshi ne ya kwana ma shi bai sani ba.

Shima yana can yana lalata yaran mutane, ko yana tare da daduronshi?'
"Yaro kaine Khalid tsohon saurayin Sabuwa ko?"
Kawu Manga ya tambayeshi.

"Baba nine ku zauna ga kujeru"
Yayi maganar ko a jikinshi.

Mustapha da Kawu Manga ne suka zauna.

Babangida na tsaye jikinshi na rawa.

Wai yau shine suka tawo wajen saurayin matarshi nemanta.

Wannan tashin hankali da yawa yake.

Kawu Manga ya yi ma Khalid bayanin zuwansu kab.

Babu shiri ya cire gilashin dake idanunshi cikin nuna damuwa yace.

"Guduwa Sabuwan tayi?

Wallahi Allah bansan inda take ba kuma bama waya da'ita Baba ka yarda dani da Sabuwa na hannuna ko bazan bayar da'ita ba zan sanar muku tana hannuna ko dan ku samu nutsuwa"
Ai sai ji suka yi Babangida yayi kukan kura ya
ale jikin Khalid ya hau naushin bakinshi dan ba
in ciki.

Khalid shima ingarma ne kuma ba baya ba wajen karfi sannan a kule yake da Babangida da kuma fa
an da sukayi kwanaki har Babangida ya samu galaba a kanshi.

Dambe da zagine ya kaure a ofishin.
Chapter 20 · 0% Book details