← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 50

Sashe 8

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi kasa zai kwana Dole na kyaleshi na haye bed dina na kwanta bacci ya kwashe Ni,tsakar dare misalin 2am ya farka naji Yana ta kici kicin bude kofa,Ina kallonsa ya fita na bi bayansa a hankali ba tare da ya ganni ba,sai Naga ya nufi kofar waje zai bude ya fita, da sauri nayi gyaran murya tare da kamo hannunsa,Ganin haka sai ya saki Murmushin Jin dadi ya ganni don ya manta ma tare muke 1room baida tunanin da zai gane,sai ko ya biyo Ni da sauri ya rikeni kamar za a kwace Masa Ni,muka koma Bedroom,ganin idan har na koma bed nayi bacci zai fita sai na dawo kasa Nima kusa dashi na kwanta, Hannuna na sarke da nasa bacci ya kwashe Ni sannan shima yayi bacci again nasan shi mayen bacci ne.

Bamu farka ba sai da asuba na tashi nayi Alwala da sallah shi bacci yake Amma na tasheshi nayi nayi yayi sallah yaki yi sai hakura nayi dashi, baccinsa yake har 10am lokacin na Gama gyara gida neat ko Ina Yana kamshin turaren wuta, wanka nayi nasa sabuwar atamfa ta Yar dubu uku Tasha dinkin Yan burni Riga da skert sunmin daf daf sabo da aikin su ya Salman ne Yan gayu sune suka kaimin dinkin cikin birnin Gombe.

Ban iya dauri ba kawai nayi irin ture kaga tsiya powder kawai na shafa sai maroon jambaki, da kwalli abinka da fara sai nayi kyau sosai,gidan naji an kwankwasa na bude tare da lekawa sai Naga Ya Salman da kansa dauke da food flask kala biyu da na ruwan zafi, farin ciki ya kamani nace Ya Ina kwana, dariya ya Salman yayi ganin Ina tare da Mahaukaci Amma har wani cakarewa nakeyi haka Ina nishadi na ko a jikina,Lallai mace indai tace tana son Abu a kyaleta kawai.

Shugo Mana Yaya Hajiyarmu ce ta Aiko ka? Kin San Abbu yace baza a Baki ko ruwan tea ba a gidanmu Ni na siyo muku a bakin titi ga tea Nan wannan kuma doya da kwai ne, Zan na kawo Miki har na kwana uku, Kai Amma na gode ubangiji Allah ya Kara budi gaskiya bani da kamarka Kana ji Dani fa,Har Palo ya shugo ya zauna muna hira,yace Ina angon naki Wai? Nace sa Ido kazo kawai? muna dariya nace bacci yakeyi,Kai ya jinjina sannan yace an gaisheki masoyiya yanzu Wai Allah kika iya kwana dashi Fadila?

Dariya nayi nace kune fa kuke tsoronsa Amma wlh ba wani Mahaukaci bane,Hmm Haka dai kikace Amma mutumin da ya kusa halakamu kiyi dai a hankali,muna Haka sai ga Dan Bature ya fito ya tashi daga bacci kenan, Baki bude Ya Salman ke kallonsa yanda yayi uban kyau haskensa ya Kara fitowa, cike da mamaki yace Wai duk jiya kika canja shi Haka? Lallai Sister Kya so abinki Dole kema ki haukace wannan ko dai balarabene ko Bature a farar fata ma samun irinsa sai an tona.

Wani farin ciki ya kamani an yabi Dan Bature,ji yanda kike murna,sunansa Aliyu ko yace? Da sauri nace ae Mana Ina wani fari da Ido ,dariya Ya Salman yayi sannan yace Allah ya shiryeki wlh Baki da kunya yanzu Fadila a gabana.
Nace uhm Bari nazo ka Dan jirani,Dan Bature Yana tsaye jirana yakeyi naje,Yau ma Haka yayi Brush da kansa,na rufe idona na Masa wanka sosai ya Kara wani fresh,Ya Salman Yana jinmu a bayi muna ta gwagwa gwa Ina ta lallabashi ya tsaya.
Bayan mun fito muka wuce bedroom a gurguje na shiryashi na canja Masa shadda Milk color yayi mugun kyau,gashinsa na taje masa,flower dake gaban rigata ce ta tafi Masa da hankali ya fara Wasa da ita Ina taje Masa Suma naji hannunsa saman kirjina yaji laushi sai ya janye hannunsa da sauri.

Dariya ma ya bani yanda ya tsorata, Yana kamshi muka fito Palo wajen Ya Salman Wanda mamakina ya cika shi,ga bawan Allah ya dawo mutum jiya daya Nan gaba ya za a ganshi kenan?,kusa Dani Dan Bature ya zauna.
Yana nuna min flask na bashi abinci, Ya Salman ya min Sallama ya tafi abinsa Yana mamaki yaje gida da wurin Frnds ya dinga Basu labarin yanda Dan Bature ya koma.
Haka Hajiyarmu ta dinga mamaki Abbu kuwa Baki ya tabe tare da barin wajen.

Ni kuwa tea lafiyayye yasha Hadi na zuba Mana a cup daya idan na kurba na bashi ya kurba ga bread ga doya da kwai , Yayi Shuru abinsa Ina ta Masa surutu nace Kana da Yan uwa kuwa? Kallona yayi ya turo min lips gaba Sigar Shagwaba,Murmushi nayi tare da ja Masa hanci kadan Kara daure fuska yayi,Bayan mun koshi naje Ina wanke wanke ya bude kofa ya fice abinsa. Kyaleshi nayi ya fita kowa kallonsa yake a garin Ana mamakin kyau da canjawarsa kamar a sace shi,matasa har tsokanarsa sukeyi da Ango Ana mamaki wasu na dariya.
Shuru Shuru Bai dawo ba har magriba tayi Ina jiransa ban ganshi ba,gidanmu daya sani tun farko yaje kofar gidan ya zauna Yana jirana,ya manta gidan da nake yanzu,su Ya Musa Sunyi iya kokarinsu na ganin sun ganar dashi gidan da nake a matsayin Amaryarsa Amma yaki ma saurararsu,Amma da ance Fadila sai yayi ta kallon mutum Yana Murmushi, Ya Musa har gida yazo min yace to Amarya aiki ya ganki Ango ya Gaza gane gidansa munyi munyi ya gane ya kasa kizo ki tafi da abinki aiki ya ganki ai.

Hijab na sa muka fito da Musa Ana ta kallon Amaryar jiya a waje Ana gulma naje har inda Dan Bature yake Yana ganina ya mike zumbur Yana Dan Murmushinsa ya kankame Hannuna nace Ina ta nemanka muje gida,hannunsa cikin nawa muka Kama hanyar gidanmu Ina fada masa kaga dai gidanmu can ka gane ko,kicibus mukayi da Abbu zai je masallaci,har kasa nace Abbu Ina kwana Baki ya tabe yace shashashar banza Kinga da me hankali kika aura me zaisa a ga Amaryar da aka Kai jiya ta fito garari a titi, Baki na turo gaba, naja Hannun Dan Bature muka tafi gidanmu,Abbu ya wuce cike da takaicina Amma fa yayi mamaki gani Angon Haka ya wani mugun haduwa.

Bayan nayi sallar Magrib Yana kallona shima ya fara kwaikwayo na Wai Yana sallah Ina Kara gyara Masa Yana faman gwadawa,sai ya tafi tunani sai ya kasa tunawa,yau ma Haka Ya Salman ya kawo min kaza Gasashiya da yogurt sai gurasa taji Hadi su Muka ci da dare, Bayan munyi wanka munyi Shirin bacci na zauna da fitila a gabana na lallabashi na yanke Masa faratansa tas na kankare, yauma a kasa muka kwanta Ina gefensa Hannuna cikin nasa sabo da Kar ya tashi cikin dare yace zai fita.

Cikin dare aka fara ruwan sama me karfi munyi bacci window a bude sanyi ya ratsa dakinmu sosai, Jin sanyi Yana bacci Bai San ya matso kusa Dani bama hannunsa ya daura saman cikina yaji dumi dumi ya juyo tare da shigewa jikina sosai ya kwakwumeni ya Gama kanannadeni a jikinsa,Nima Jin dumi yasa na kara lafewa muna baccinmu a nutse cikin nutsuwa fuskarsa yake goga min a wuyana bamu farka ba yau sai da Rana ta fito munji dadin bacci.
a hankali na tashi,Ina zare jikina a nasa shima ya farka tar ya bude idonsa a kaina,sanye nake cikin kayan bacci Yar riga da wando shara shara,Surata ya Shiga karewa kallo kunya ce ta rufeni da sauri na dakko Hijab Dina na sa a jikina, Baki ya turo min ya jawo Hijab Dina yana kokarin dage min Hijab nufinsa na cire Baya sonsa, fuskewa nayi kawai na ja hannunsa Yana daga zaune, Mikewa yayi ya bini zuwa toilet gashi ban Isa yayi ko fitsari a gabana ba,sai ya turoni waje ya kulle kofarsa kamar me hankali abin Nan Yana daure min Kai.

Yau ma Haka yayi wanka da Brush da kansa yayi sosai,sai da ya fito ya kalleni fuskarsa ba rahma dake dama da wahala kaga dariyarsa sai Dole,Kirjinsa da surarsa tare da skin dinsa me sheki na tsaya kallo wani azababben kyau da yake karawa ga surarsa dirinsa hadden gaske ne ta ko Ina ya haru,Namiji ne na gaske.

Toilet na Shiga da ruwana cikin botikin karfe na wanka,ya bini da kallo Ina Shiga toilet ya biyo Ni ,sai da na tube na ganshi a ciki,Kara na saki kafin na dauko towel ya dauki soso na da sabulu Wai zai min wanka shima,towel na dauka Zan fita da gudu taku daya ya damko Ni tare da dawo Dani toilet din da karfi,Ina a tsaye ya kwace towel din a tsaye yake min wankan Ina zillewa, tsabar mugunta Haka ya dinga gurje min jiki da soso zafi sosai nake ji, har gashina ya wanke min Kuma ya iya Yana yi Yana tafiya tunaninsa daya saba,idan ya tuna sai yaci gaba,sai da ya Gama Dole sannan yayi waje abinsa ya koma Palo ya daklo Mai yanda na Masa jiya haka yayi ma kansa ya bude akwatinsa yayi Baja baja da kayan a tsakar daki ya zari farin yadi yasa abinsa,gashinsa ne kawai ya kasa tuna yanda na Masa jiya,sai da nayi brush da Alwala nazo na Karasa gyarashi, gabansa na tsaya wata Yar tsugul Dani Ina kulle Masa botin na riga,ba zato naji hannunsa a wuyana Yana taba kashin wuyana, wani shock nake ji a jikina wani dadi dadi, towel din ya sauke kasa ya daura hannunsa saman dukiyar fulanina, kunya ta kamani na jawo towel Dina a kasalance sabo da abinda yake min jikina ya mutu gashi abinda nake ji bama na so ya daina abinda yake min Amma Haka nayi karfin Hali na maida towel Dina, na juya Masa baya, ya fara kici kicin kwace Towel din nawa, ya Kara janyeshi ya jefar Yana min wani kallo kamar me hankali idonsa ya canja zuwa red kadan, abin ya daure min Kai,Haka ya fara latsasu kamar Yana Jin tsoro Ni Kam na Gama tafiya bazan iya hanashi ba,kafafuna sun Gaza daukana sai saman bed na fada,shi Kuma bazai hau bed ba,sai ya rike Hannuna ya jawoni na mike tsaye,da sauri na fada Kirjinsa na rungumeshi Ina sauke numfashi.
Chapter 8 · 0% Book details