← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 50

Sashe 18

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudun tsiya ya kaini wani katafaren Hospital yace miciji ya sareni Nan take aka bani agajin gaggawa na treatment, suka bani gado sannan Driver Yoruba ya Kira Number ta Nanee ya sanar Mata,ya sanarwa Attine,sai ga Attine tana kuka tazo, lokacin Ina bacci sai ga Nanee da zugar motarta biyu itama Nan ta biya kudin magani da komai,sai dare na farka Naga Nanee da Attine Sunyi tagumi.

Attine tace garin Yaya Fadila na Basu labari harda kuka na,Nanee tace ai ke kika jama kanki na fada Miki kar ki kulashi, Attine tace Ice dinne Haka dama yake? Nanee tace ita ta tsokaneshi, kuka na fashe dashi nace Ni na fasa aikin wlh tafiya wajen Attine zanyi,Nanee tana dariya tace bazai sake faruwa ba kiyi hakuri,Attine tace saida na Baki lbr ai halinki ya jawo,Bayan an sallameni Nabi Nanee muka koma gidan Bayan Attine ta ja min kunne sosai na fita hanyar kowa.

Washe gari Haka na fito zan tafi schl na Kara ganinsa yayi Shirin fita cikin wasu kana Nan Kaya Yan gaske kamar Bature, Ina so na kalleshi naji sanyi a Raina Amma na kasa sabo da tsoro nayi tafiyata sum sum na fice,da mota ya fito yau shike driving tun Bai kusantoni ba na fada can kofar gidan wasu na bashi hanyar Amma sai ya tsaya da mota ya cuno min wasu karnuka suka yo kaina kamar zasu ci babu, tsoro yasa na watsar da hand bag Dita na take da matsiyacin gudu na fige dankwalina na jefar karnuka biyu suka rufa min baya, Allah ne ya kawo Dr who ya Hangoni ya fito da mota Ina kukan masifa ko gama tsayawa baiyi ba na afka motar sa.

Da kyar ya rike dariyarsa yace sannu me aure Mijin nakine? Harararsa nayi nace malam jeka dauko min mayafina da dankwalina Ina matar wanka ka rainani,Yana dariya ya fita ya dauko min har jakata ya dawo har schl ya kaini.

AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

26-30

Official

By
AsmaBaffa

HADIZA MUKHTAR,MOM INTEESAR,STYLISH ANGEL,AUNTY SUMEE,FATEEMAH ZAHRA.
ga page naku 👍🏻😍

12PM na bar lecture na dawo gida, Nanee na tambaya me Zan dafa tace na Masa pounded yam da miyar kwai, sai farfesun Kaji,sannan na hada juice kala biyu,Ice baya son abinci barkatai yaci wannan yaci wancan,ban dau dogon lokaci ba na Gama tare da gyara kitchen,na fito Ina shirya Dinning Naga Ice da tafiyarsa ta Izza,tunaninsa Ina schl, ko kallo ban isheshi ba ya wuce, wani sonsa ya taso min na bishi da kallo tare da share guntun hawayena na tausayin kaina.

Wurin Nanee ya wuce Ni Kuma na koma room dina na fada saman bed sai da naci kuka na sannan nayi wanka na sake sabon shiri cikin doguwar rigar material,nayi rolling mayafina cikin mutunci da Kamala,na dauki hand Bag Dita tare da fesa turare kadan na fito zanyiwa Nanee sallama na gansu saman Dining ita da Ice suna ta kwasar girki na me dadin tsiya.
Cike da damuwa na duka kasa kusa da ita nace Nanee Zan koma schl, Murmushi tayi tace to kinci abinci dai ko,karya na Mata nace naci Amma damuwa baza ta Bari na ci ba.
Tace to a dawo lfy ta Miko min dubu biyu ki Kara kudin taxi nace A'a akwai canjin dazu sun isheni Har gobe Nanee,

Aransa Yana ji yace shi Kam tunda ga kan danginsa zuwa Yan aiki Bai taba ji a gidan an bawa mutum kudi yaki karba ba,har ma yace akwai ragowa sun Isa Haka, sai yau da yaji a bakin wannan baiwar Allah me kiransa da mijinta.

Ina ta kallonsa na shagala Ba tare da ya kalleni ba naji yace an dameni da kallo fa, Mikewa nayi kamar kwai ya fashe min a ciki na tafi schl.

Da dare Nanee ta sameni har dakina tace Fadila? Nace naam ki daina kallon Ice a mijinki,karki nuna ma kin San me kama dashi,wlh Baki San gidan Nanba sai Nan gaba,uwarsa Bata kaunar talaka,idan taji kina shige Masa ko wani Zancen mijinki duk da ba gaskiya bane,zata Sa a koreki a gidan Nan,ke zata iya salwantar da rayuwarki ki rike kome a ranki ba ruwanki,a gidan Nan Ni ba kowa bace kin ma gani da idonki,kudin kashewa,sutura da komai yanzu ba me gidan ke min ba Ice shine ke min kome nake so.

Ki San me kike ki dawo hayyacinki, Kaina kasa nace Inshallah Nanee bazai sake faruwa ba,tace Good kallo me tsayi karki Masa baya so Kuma uwarsa idan ta fara Jin jita jita ke zakiyi kuka da kanki.
Inshaallah na gode,ta fita na zube a kasa na rushe da kuka, ganin za a jini na wanke fuskata nasa Hijab nayi waje can Garden na Samu inda ba kowa na saki kuka na,idan na tuna Wai Dan Bature Bai sanni ba sai na Kara fashewa da Kuka me Sauti,na Kara barkewa da kuka,na kwanta a kan grass carpet na tuna yanda nake matukar sonsa,Kara tsagewa nayi da kuka na dinga burburwa Ina birgimata da Shure Shure kamar Zan mutu.

Tsawa naji an buga min ba shiri Jin Muryar Dana sani Ice ne nayi duf lokaci daya,ban ko kalleshi ba na tsaida hawayena,na goge fuskata na juya na kifa cikina nayi kwanciyata, kafin kace me bacci yayi awon gaba Dani a wajen.

Wajen Nanee ya wuce yace Yar aikinta mahaukaciya Nanee tace ban son sharri fa,yace yanzu na Gama tabbatarwa ya dinga Bata labarin yanda na dinga kuka da burbuwa,Nanee tace to meke damunta?Baki ya tabe yace harfa ihu da burbuwa takeyi aljanu ne da ita.
Nanee tace kyaleta na gaji da matsalarta.

Na tsawon kwashe 3wks a gidan na Dan Saba Amma bama muamula da kowa yau jumaa yaune Kuma ake hallara a wani Palo hadadden kamar wani hole yasha alatu Bayan an sakko daga masallaci kaf gidan manya da Yara zasu hadu a palo,ko wanne da Yar aikinsu daya me dafa musu abinci tana kawo musu abinda suke so,Nanee da Ice tare da Yan uwanta da yayanta nice me kawo musu ko me suke bukata, duk part me dafa abincinsu days zata zauna a Palon.
Nima na Gama dafa duk abinda Nanee tace Ina da lecture Amma ba yanda zanyi Dole tace na hakura ba a tsallake ranar jumaa.
Duk mukamunka sai ka zauna a gida a wannan Palo,Daddy ya koma kasar wajensa business,Hajjo kakarsu taci kwalliya tana Palo da masu Mata tausa da me girkinta,Haka Karimatu da Maryam Amarya ko wanne da iyalansa.
Ice ne kadai ke bangaren Asiya Wanda uwarsa sai haushi take ji an rabata da danta,Yan Matan dangi kaf da maza suna Nan an hallara,Naja Cilla tace yau akwai labari me zafi yau kuma zamu bawa Fadila suna Nickname, Ina gefen Nanee nayi Shuru, Ice Yana can baya kan lumtsumemiyar 3seater Yana latsa waya.
Ni tsoronsu ma nake ji duk sun Sa min Ido,wata Jamila Ana ce Mata jummala tace tunda tace Ya Ice ne mijinta Sunanta matar Ice ko ya kukace, Yar lalle tace Dalla matsa ai iyayi gareta Wai ita ta waye,Hajjo ta tabe Baki tace tana bangaren Asiya ai Dole ta gaji iyayi.
Shehu Niga yace Allah tana Kama da budurwata Kuluwa ta kauye na fada muku gani kuke karya nake,Ni dama zata aureni,sai tafi raf raf da dariya,Ina jinsu suna ci min mutunci.

Karimatu tace Kai kun cika Mana kunne kufa Yan iska ne,Salihu Boy kaninta yace Aunty masifa munyi Shuru Nan suka ce heee suna dariya,Nanee tace kawo Mana juice sharesu, na mike Wata a ciki Ana ce Mata Shekara tace Ashe akwai Dan shape inye Nan ma sai dariya,Raina yayi matukar baci na kasa hakuri nace ke dakata kucaka da igiya har uku a kaina ta aure,karki Kara kalamai irin wannan wani Ina da shape salon wannan kartan mazan su dinga kallon tsaraicina suna hadiyar yawu suna kissima Abu a ransu zuciyarsa na darsa musu bad Abu a kaina.

Chakwas tace iyye waye saanki a Nan wlh sai muyi Miki dukan tsiya,na kalleta naja tsaki nace Wanda Bai fasa ba Baya kaunar Allah,karku ga nazo aiki gidanku wlh na fiku gata da asali halak nake nema, Iyye cewar Karimatu da suke Ce Mata Umma ta fara zazzaga min masifa da cin mutunci,nace kija mutuncinki Umma Dan Nima na gaji Masifar Nan Dan uwata data haifeni ta fiki balai,muguwar Masifaffiya ce babata da anan gidan take da tuni ta Cinna muku wuta kun Kone kurmus, hhhhhh aka dauki dariya kowa Yana kyakyatawa har Nanee sabo da yarinta da kuruciya Dana nuna, Ice Yana ji Bai San sanda dariya ta kwace Masa ba,Dr who harda rike ciki yace in Banda kuruciyarki Fadila Kya Fadi mummunan halin ummanki,Kinga yanzu kowa yasan Mum naki da halinta.

Tunani nayi Naga Haka ne ai nace to ai dai tana da kirkinta Kuma ma...ma ai Abbu dina baya so na har wajen Yan Hisba na Kai kararsa amma Hajiyarmu sabo da kyan halinta itace take so na,Nan ma sai dariya Chakwas tace Abu ya lalace babanki kika iya kaiwa kara,? Na Galla mata Harara to ai da dalili malama Dan kawai Ina bin Mahaukaci akace zai min ciki sai dariya kyalkyalkyal kowa dake Palon har Anty Amarya da Bata dariya yau tayi,Hajjo tace wannan yarinya kuce kawai masifa aka dauko Mana gida ba na gari bane.

da sauri nace A'a ai mahaukacin na aura na Kai Babanmu Kara Dole aka aura min mahaukacina aka bamu gida aro, Umma tace uhm Kuma ya kukayi rayuwa na zauna nace hmm ai Ina sonsa, nice Nan nake Masa wanka da komai na sa Masa Kaya,ke in kin ganmu abin Sha'awa, baya magana, Shehu Niga yace Dan Allah fa nace Allah da zaku ji labarin sai kun tausaya min kunyi kuka sabo da tausayi, Cilla tace mun shirya maza Gama aikinki ki bamu musha nace to.
Chapter 18 · 0% Book details