← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 50

Sashe 4

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bature na kalla Ina Murmushi nace cire Kaya n ka canja,kafada ya make alamar yaki, nace sanyi zai maka illa Ashe kana Jin magana,rigarsa na daga zan cire Masa ya zuba min uban yakushi saida ya dauke min fata, haushi naji sosai na bude kofar nace to fitar Mana a gida,kawai sai Naga ya fita kuwa yayi tafiyarsa cikin ruwan Nan ga duhu ya dauki hanya sosai.

Gidan na rufe na maidawa Ya Salman kayansa na koma na kwanta da kyar bacci ya daukeni Ina tunanin Bature yanzu Yana can ruwa Yana zaneshi. da Asuba na tashi nayi Alwala da sallah sannan na fara tasbihi da sauran azkhar har Rana ta fito gashi dama Abbu ya hanani zuwa makaranta talla kawai nake fita sabo da na duba Bature ko ya kwana lfy? Da wuri na Taya Hajiyarmu girki shayi muke Sha lafiyayye da kosai sai bread,sannan ga Koko da dumamen tuwo,Bayan na sake yin brush nayi wanka na fes na sa doguwar rigar atamfa ta me kyau nayi acuci da gashina tare da yafa Dan gyale na,sabo da kallo a waya yanzu mutan kauye ma sun waye ba a wuce su a iya wanka da kwalliya sabo da kallace kallace a waya, Kuma da yawa Yan makaranta basu fiye kauyanci da yawa ba, suna wayewa bare gidanmu da muke da Dan rufin asiri daga mazan har ni daban muke ga kyau.

Hajiyarmu ce ta kalleni ta tabe Baki ga kyau har kyau ba miji,yau Kuma tallan goron da wuri za a tafi haka? Anya ba akwai wata tsiyar da Zaki shuka ba nasan halinki Fadila, Murmushi nayi nace nafi so na siyar da wuri kafin mazan su tafi gona kin San tsofaffi da gona, Hmm to ya Naga kina wani nishadi ke da kullum fuska ba rahma Kuma sai wani zumudi kike Bayan tallan idan Zaki je kamar Zaki mareni Haka kike tafiya.

Shuru nayi Mata ta Kara tabe Baki tace dauki ki tafi tuku tuku mugun ice a Haka kamar saliha,Ni dai Shuru nayi na dauki talla na na fita Bayan na Shiga dakin Abbu na gaishe shi Yana muzurai Ni dai na fice abina,ko wajen tsofaffin banje ba,na fara duba gari ko zanga Bature Amma ban ganshi ba,hankalina ya tashi sosai na Shiga zagaye kauyen nan, har kusa da wani Rafi da mutane ke wanki ga bishiyoyi da ciyayi Kore Shar ga sanyin Niima a wajen,na duba ko Ina Banga kowa ba na juya hankali na tashe na fara tafiya naji an ja min gyalena kadan,a tsorace na juyo sai nayi tozali da Bature,kasa kallonsa nayi sabo da tsananin baiwarsa da kwarjini ga wani kyau me tafiya da imanin Dan Adam.

Ajiyar zuciya na sauke a hankali wani farin ciki ya cika ni, nishadi ya kamani gashi lfy Lau,juyawa yayi ya fara atishawar mura sosai,kayan jikinsa Sunyi dirty,hannunsa naji me matukar laushi cikin nawa ya rike Ni wani zirrrrr naji jini na ya amsa,Har gindin bishiya ya Jani sannan ya zauna Nima ya min nuni da na zauna,Zama nayi nace Ina kwana Bature? Bai ce komai ba ko kallona baiyi ba,na durkusa nace Ina kwana? Ya ka tashi? Ice ko dai lfy kake? Ya ruwa jiya Kuma sai kasha dukan ruwa gashi mura ta cafkeka Bature Kai dama ba kwari ba kamar fiigaggiyar kazar turawa kake.

Kallona yayi kawai ya hade fuska,nace Allah baka hakuri me yayi zafi Ni Fadila,da gani Amma Kai Masifaffe ne ko irin Hajiyarmu,wlh ka kiyayi kanka mutan gari zasu tsaneka tam ga Hajiyarmu abinda ya jawo Mata baking jini kenan har mu yaranta aka tsanemi.
Ido kawai ya zuba min Yana kallona nace ae ka kalleni da kyau Kai ba a Isa a Gaya ma gaskiya ba sai kana fushi Haka ake rayuwar duniya fisabilillah kace baza a fada ma gaskiya ba to ya kake so ayi maka Kai kaki magana kamar jariri.

Yanzu kaci abinci ko da yunwa ka zauna? Shuru ba magana,Maganar kurame nayi Masa kaci abinci? Kai ya girgiza min Alamar baici komai ba,nace to na ganoka kurma ne kai Ashe? Bari na Nemo ma abinci karka biyo Ni ka jirani a Nan.

Zama yayi kuwa Bai bini ba na ajiye farantin goro na a gabansa Ina cewa ga ajiyata Nan ka jire min Kar ka Bari wani ya dauka, nayi tafiyata abina.
Da sauri naje na damu Mahmood da Ya Salman sai sun bani dari biyar zan siya wani Abu,Ya Salman yace me Zaki siya? Nace sirri ne idan zaku bani ku bani,Mahmood ne ya zaro dari biyar ya bani Ina Godiya na fyalla da gudu,na koma gida ba tare da kowa ya ganni ba na dauki cup me murfi,na Shiga dakin Salman na dauki kayan sawar da ya bani jiya na sawa Bature,da gudu na arce muka ci karo da Abbu Dan karma ya min magana na Kara karfin gudu na a tamanin fiiiiit na wuce shi, Ina jinsa yace Zaki dawo ne.

Table din me shayi na na tsaya nace ayi min hadin kauri na dari,Bread na Hamsim,naje na siyo pure water biyu,na siyo tooth paste da brush sababbi na dawo inda na barshi me zan gani Yara sun taru a gabansa suna ta kallonsa suna tsokanarsa ga goro na Sunyi kaca kaca dashi a wajen suna iba suna watsawa kogin, ragowar Kuma suka gatsa su Yanda bazai siyu ba.

Da masifa na koresu,suna tafiya cikin sanyi na nace yanzu kana gani suka lalata min Kaya Haka? yau duka Hajiyarmu zata min,Bai kulani ba, haka na bude brush na matsa toothpaste ina Masa Zancen kurame ya taso kusa da rafin, na gwada Masa yanda zaiyi abin mamaki sai ya make kafada ya ballo abin bishiya yayi Masa kamar aswaki ya fara goge Bakinsa dashi, Haba shi yasa naga hakoransa neat kullum Ashe aswaki yake yi,a gabana ya goge ko Ina har halshensa can ciki, fushi nayi yaki karbar nawa yayi brush,kamar ya sani sai ya jefar da Aswakin ya Miko min hannu na bashi Brush din yayi abinsa kuwa,sannan na bashi pure water daya ya kuskure bakinsa, brush din na wanke na maida su leda, Ina Murmushi na sake Mika Masa kayan Ya Salman nayi Masa alamar ya sa harda Boxers, da kyar na rokeshi ya karba ya zaga Bayan bishiya ya saka kuwa Normal sun Masa kyau da yake yafi Ya Salman Dan kauri sai ya cika kayan tab yayi Masifar kyau kamar wanka yayi abinka da farar fata.

Kayan daya cire harda singlet da boxers nasa designers na kwashe na linkesu na zuba a Leda,agogon dake daure a hannunsa nake kallo na Diamond me kyau da tsadar gaske da wata azurfa zobe me kyau.

Tea din na bude nasan ba iya Sha zaiyi da kansa ba Haka na zage da kaina na dinga bashi da bread ya shanye tas,ya fisge ruwan dake Hannuna pure water saida ya ji min ciwo kadan a fatar Hannuna ya karce ni, shanye abinsa yayi sannan na mike na tafi gida, shi Kuma a Nan gindin bishiyar yayi kwanciyarsa bacci me karfi ya kwashe shi.

Munafukai yaran Kawu Salisu Dana Usman har sun ganni duk abinda nakeyi suna sa min Ido,tuni suka dinga yada Ni a gari har Zancen ya koma kunnen Abbu da Yan gidanmu,Bulala Abbu ya tanada Yana jira na dawo,mutanen gari Ana ta surutu Ina iskanci da Mahaukaci Dan na ganshi Kyakyawa iskanci na harda mahaukata nakeyi.

Babu Wanda ya nuna min a fuska har na Shiga gida,Ina tunanin me Hajiyarmu zata yi min ba goro Babu kudin goro,ina rabe rabe na Shiga gida,Hajiyarmu tace au Ashe ma kin siyar har nace Zaki gane kurenki nawa kika siyar kawo a irga kudin Lallai kina so nayi Miki kayan kitchen me kyau idan auren yazo inye watarana kirkinki yawa ne dashi.

Ina Ina na fara nace Uhm...wlh ba laifina bane Dan Bature na bawa jira ya bar Yara suka kwashe,Dan meeeeee kikace? Hajiyarmu ta tambaya tana turo min kunnenta daya tare da karkace wuyanta, Bature na Bata amsa kafin na rufe Baki ta gasa min mari, ta hada kaina da bango ta gwara min guf tuni na kwalla ihu ina neman agaji,Abbu ne ya shigo da Bulala ya kulle dakin ya Shiga tafkata Yana dama taraki nakeyi abin kunyar da kike jawo min ya isheni gwara na hallaka ki da Hannuna, bulalansa sai da suka karairaye a jikina yayi min jina jina,fuskata da jikina sun kumbura Sunyi shatin bulala, Hajiyarmu tana Kara Mata Malam.
Anty ta sheke da dariya tace yarinya anga me kyau Oh duniya yanzu ba a soyayya Dan Allah.

Haka mazan gidan harda Mahmood suka ce Suma sun daina kulani tunda bana Jin magana Ina Bata musu Sunan family bana jin magana,Ya Salman yace kin San Halin Abbu da Hajiyarmu idan kinwa kanki gata to ki daina kula wannan Mahaukacin wlh matukar Baki daina ba Babu mu ba Ke,a hankali nace ai kuwa wlh sai dai a kasheni Kuma kowa ma ya daina kula Ni din Amma bazan fasa taimakonsa ba.
Haka kika ce? Cewar Ya Salman nace ae sai dai kuyi hakuri,Baki bude yace to muma ba ruwanmu dake,nace ae kowa yayi harkarsa, Hajiyarmu ce ta Kara kwarfeni da Mari ta harbo Ni tsakar gida Ina kuka .

Sai Dana kwashe kwana uku Ina jinya ko fita banayi,Amma duk da Haka tunanin Bature nake ko Yana Raina so nake kawai na warke na Nemo shi.

Abbu Kuma sunyi meeting da Yan uwansa za ayi min aure Nan da sati Uku da Wani dan uwanmu Dattijo ne ma Talle, Talle yace Yana so na a bashi ai kuwa Abbu yace an Gama ayi shiri Amma Kar a Bari na sani sai dai naji kawai an daura,Akan Haka Ya Salman yace gaskiya baza ayi min Haka ba,Amma Abbu ya zazzageshi Dole ya kyalesu.
Chapter 4 · 0% Book details