Sashe 11
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Me machine da ya Kai Dan Bature Gombe city na Nemo na tambayeshi labarin abinda ya gani Aiko ya bani labari karshe yace naji da turaci ya ambaci a kaishi airport Kuma da Alama ba Dan kasar Nan bane Don yaren da yeke Babu shi a kasar Nan kalar fatarsa ma ta nuna, Hawaye ya ziraro min nasan ma har abada bazan sake ganinsa ba ya kamata na hakura Amma zuciyata ta kasa hakan kawai naci gaba da kaiwa rabbil kuwwati Wal jabarut kukana,na Kara kwashe a kalla 5mnths Amma na kasa hakura anyi fadan anyi nasihar an gaji an kyaleni Haka. Inda Allah ya taimakeni ya bar agogonsa na diamond me tsadar gaske da kyau,ga zoben azurfarsa me kyau,chain din sarka na Samu na zura ta cikin zoben ya Zama kamar sarka me zobe nasa a wuyana da ita nake kwana Ina tashi,Haka agogonsa duk da yayi min yawa Haka na daurashi a Hannuna ya zauna dadas yayi min Masifar kyau kowa sai ya kalli Hannuna.
Attine yar Uwar Hajiyarmu wacce ke Zama a kudu can bangaren Iyamurai itace tazo gida tare da yarta budurwa Safarau,sunzo gidanmu taga halin da nake ciki tace Hadiza me zai Hana na tafi da Fadila can kudu ta samu salama sannan zata samu aiki tana kula da kanta,yanzu Kinga Safarau a Company na arna take aiki tana goge goge da shara da kin bar Fadila sai na kaita aiki ko wani Company ko gida ko office din wasu tana Dan aiki suna biya da tsada musamman idan mutum ya iya aikin ga Tsafta.
Baki na tabe nace me zanyi a kudu Ina da aurena,Hajiyarmu tace to da surutun da mutanen garin Nan sukeyi ai gwara ki koma can ko banza ma huta da munafunci, Hajiyarmu ta shawarci Abbu,shi Kuma yace a dawo lfy Ni da zagin da take jawo min ai gwara ta tafi can tazo Mana da yawo,Anty ma tace da mun huta wlh.
Ya Salman na kaiwa Kara Amma Nasiha ya min gwara na tafi Amma na rike mutuncina da igiyar da take kaina,ya dinga min Nasiha Kar na bijirewa Hajiyarmu again kaucewa Umarnin iyaye Yana kawo matsala,ba a son Raina ba ranar da Attine zata tafi tare da yarta Safarau na shirya da akwatita katuwa na bisu munyi sallama da iyaye Yan uwa da abokan azirki,Ya Salman ba,Musa,Mahmood har Tasha suka rakamu tare da bani dubu ashirin cash,ba tare da na San wannan state zamuje a Nigeria ba.
Gani nake kamar Watarana Dan Bature zaizo nemana kauye har sallahu na Bari idan ya dawo Zan siyi waya acan Zan na Kiran gida mu gaisa idan ya dawo a sanar min.
Ban San birni ba sai da yawo a Shiga a fita bare kudu,Haka muka je Tasha naji tace Lagos Baki na hangame nace Lagos kuma Hawaye ya zubo min shike Nan Dan Bature bazai ganni ba har abada Ina zai ganni Ina gari kamar Lagos,Attine kuwa haushi nake bata sai masifa take min muka Shiga mota katuwa doguwa, ita ta biya kudin da komai muna tsakiyar arna karfe 4 na yamma motar mu ta hau titi.
Tafiya muke ba ji ba gani Safarau sai dariya take min yanda nake ta sheka bacci,ita Kuma wayarta tecno take dannawa tana chart,tasa earpiece a kunnenta kujerarmu kusa muke a jere Attine Kuma tana gabanmu tana sheka bacci,Safarau tace Fadila ungo sa kunne daya na sa daya muyi kallon Nigerian film a wayata,kafada na make nace A'a ke nifa da nayi komai arayuwata Wanda ba addini ba gwara nayi tunanin Mijina yafiye min komai nishadi.
Attine ce ta zuba min rankwashi shashasha kina wahalar da kanki akan mutumin da ya rigada ya manta dake Bai sanki ba marar zuciya, Jin tace Danbature ya manta Dani wani kukan rashinsa ya taso min na fashe da kuka, Baki Safarau ta rike tace ke kuwa Fadila wanne balain kaddara ce ta afka Miki ta soyayya? Allah ya yaye Miki,kukana nakeyi har bacci ya sake kwasheni ban farka ba sai da mota ta tsaya za ayi sallah masu fitsari da siyen abinci ma suyi,sallah mukayi Attine ta siya Mana kaza da yogurt har gurasa,mota taci gaba da tafiya muna cin abincinmu har muka Gama.
Sai da gari ya waye 11am muka Isa Lagos lokacin Ana shara ruwan sama Amma Haka mutane ke harkokinsu abin ya bani mamaki sabanin mu Arewa idan Ana ruwa to ba me fitowa, Attine ba ruwanta ta tare Mana taxi Muka Shiga sai Unguwarsu ta talakawa Wanda Hausawa Yan ci rani da talakawan Hausawa da Kuma arna talakawa Yan bariki etc Nan muka nufa,wani gida me bene sama da kasa duk da cewa tsoho ne ya kwararrabe Amma dai Yan haya ne sama wasu yare ne Yoruba kasan Kuma na Attine ne ta kama haya.amma ciki yasha gyara.
Palo ne sai daki biyu da toilet sai kitchen ba laifi akwai rufin asiri na talaka, gidan muka gyara fes sannan Attine ta dafa Mana jallof din taliya da kifi muka koshi sannan muka kwanta baccin gajiya.
Sai yamma lis muka tashi wanka mukayi da sallah sannan muka daura abincin dare Ni da Safarau tuwon shinkafa miyar alaiyahu mukayi me dadin gaske ko Attine ta jinjina mana, Attine tana da kirki ba laifi ga son Dan uwa Bata so taga Dan uwanta cikin damuwa, Haka take koya min aiki da kayan Yan gayu sabo da Kar naje aiki gidan masu kudi na kasa komai,har girke girke na Yan gayu take koya min,waya tecno Yar dubu ashirin da biyar ta siya min Nan Safarau ta dage wurin koya min yanda ake Amfani da har browsing yanda ko girki Zan iya koyar Abubuwa ta YouTube etc, tace Bari na bude Miki Facebook da WhatsApp Kya dinga rage tunanin da kike na masifa,Baki na tabe nace tunda dai kin koya min Google da YouTube ya Isa bana fatan muamula da kowa idan ba Mijina Zan gani ba,Dariya Safarau tayi tace to Allah ya shiryeki nace Ameen.
Satina uku a Lagos nayi kyau da kiba hasken fatata ya dawo har nafi sanda nake kauye haduwa lokacin da Dan Bature Yana Nan,Attine sai Jin dadi takeyi tana fadawa Hajiyarmu kasancewar kusan kullum Attine sai ta Sa min katin waya nayi waya da Yan gidanmu.
Ni kaina Ina Jin dadin zama.watana daya Safarau ta koma can Company inda take aiki a wani reception Ana biyanta.
Attine kuwa Yar kasuwa ce tana Saro irin su Maggi,Omo,katin waya etc tana siyarwa sannan itama tana aikin kula da wata dattijuwa Igbo wacce danta Hamshakin me kudi Ne,kullum Ni kadai ce a gida,yan kudu ba Zama Mata da maza neman kudi,Ni nake aikin gida sannan na dafa abinda nake so,Lallai cimar mu danan da kudu ba daya ba,su Dole sai anci dadi iya talaucin mutum sai yaci Mai kyau Lallai Dole sufi mu girma da komai.
Attine ce ta dawo nayi Mata sannu da zuwa,da Murmushi ta amsa min tace kina Nan ke daya ko sai tunani,a hankali nace ai na rage Auntynmu,da dai yafi sauki ki taimakawa kanki,me kika dafa Mana? Pounded yam with egusi soup,to Bari naci na huta sai mu fita yawon zaga gari kema kina ganin duniya,dake Attine kyakyawace itama Yar gayu ta waye sosai,dama na fada duk danginmu kyawawane masu hasken fata.
Hmm da kin bar fitar Nan Antynmu komai baya gaba na Ni dama Danbature na Zan gani,fada Attine ta fara min ke Baki da hankali Naga Alama so kike ki kashe kanki akan wani banza Wanda Bai sanki bama yanzu, Idan Attine tace Danbature ya manta Ni Bai sanni ba shine ke matukar daga min hankali kamar Ana zuba min garwashi a zuciyata,kukan tausayin kaina na shigayi sosai har sai da ta tausaya min ta lallasheni,tace Fadila kiyi hakuri kamar yanda kike da addini ga sallah da yawan adduoi ina so ki fawwalawa Allah lamarin kici gaba da Addua sai kiga Allah ya kawo Miki canjinsa ko ya hada ki dashi again ba abinda yafi karfin Allah.
Sai kikaga ya dawo ya daukeki,inye ya kaga Fadila ga Dan baturenta ku santalo yaranku kyawawa,ban sanda na fashe da dariya ba tare da share hawayena na Kara gyara zama, nace Auntynmu sai fa kiga ya dawo ko watarana? Attine a ranta tana mamakina tace kwarai ma kuwa,nace Alhmdllh Antynmu ya kamata ki Nemo min wurin aiki na fara zuwa sabo da nayi sauri na Tara kudin da Zan gyara kaina sannan da yanda Zan kashewa kaina kudi kafin Danbature na ya dawo Kar ya dawo ya iske banci gaba ba banyi kyau ba,Dariya Attine tayi tana ganin shirmena zalla.
A fili tace inshallah kin kusa tafiya aiki kema sai dai kizo wajena da yawo Kinga Safarau a Company nasu har Wurin kwanan aiki ne dasu 24hrs ba hutu Amma akwai samun kudi kema Nemo Miki inda Zaki samu kudi nakeyi inda baza ki Sha wahala ba.
Murmushi nayi nace Allah yasa.
Bayan sati biyu zazzabi me zafi ya kamani Attine ta kaini asibiti hankali tashe,Bayan gwaje gwajensu ya nuna Hawan jini ne kadan,jini na ya hau kadan,Doctor yace ya kamata idan akwai abinda ke damuna na rage na daina damuwa sannan ya rubuta Mana Magunguna Attine ta siyo min,Bayan na warke Ras,yanda na Kara dagewa da Addua naji sauki a Raina yanzu gani da damuwa Amma Bata damuna sosai sabo da Qurani Dana rike ya Zama abokina dare da Rana,Kar nazo Danbature ya dawo ya iske bani da lfy ai abin baiyi ba Sam shi yasa na dage na rage sabo da Danbature ya sameni lfy lfy muci soyayyarmu.
Tunanina Kullum yanda muke romancing juna,muci abinci tare, wanki tare,unguwa tare,ko Ina muna tare.
Yau kwana biyar kenan kullum sai Attine ta fita Dani yawon zaga gari gaskiya Lagos ta hadu domin wani yankin ko a Abuja baza a Sami wuri me kyau Haka ba,sai ko turai shima ba ko Ina ba.
AsmaBaffa
AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕
11-15
Official
By
AsmaBaffa
Hajara Atiku sallama (laver),
Zahrau Abubakar Dambuwa
Sadiya Abubakar Dambuwa.
Ina kaunarku wajen Sharhi ga page dinku fans na kwarai.