Sashe 30
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakura nayi na maida Masa BBC dinsa na kyaleshi,ya Dade a Haka bamuyi magana ba ya mike ya fita abinsa ya tafi , Attine tana dawowa na Bata labari,tace Yana sonki wlh farin ciki ya cika min zuciya,ki Shirya da dare mu fita Mana mu zaga gari cewar Attine,Kin manta yace in na fita Bai yafe ba, ba sai ki tambayeshi ba ai ya Baki number ya kike Abu kamar sakarai kina nesanta kanki dashi har ya gaji ki fara fita a ransa.
Haka Bayan nayi Magrib na saka number din da ya bani,sai da tayi ringing har sau uku Bai daga ba,sai Kira nagani ya kirani back, ya akayi ya furta,mamaki ya kamani dama Yana da number ta, unguwa zamu je da Attine anjima.
Ashe kin yarda Ni mijinki ne? Share zancen nayi nace naje ka amince? Wani Murmushin farin ciki yayi sannan yace karfe nawa zaku fita? 8pm na bashi amsa alright ba damuwa kuje.wayar na datse na fara shiri.
8pm muka fito zamu Shiga Taxi kenan wata dalleliyar mota tayi parking a gabanmu,Driver Danbature na gani yace Hajiya Oga yace nazo na kaiku duk inda zaku je, mu baza mu Shiga ba na bashi amsa,Attine tace ke wanne Shirme ne Haka? Dalla Shiga muje, Bayan mota muka Shiga tare da lafewa ac na watso Mana raba,har wani gadara da ji da Kai nakeyi, duk inda zamuje Haka ya kaimu har gidajen kawayen Attine yawo harda Wanda ma bana kirki ba munyi ganin mota Free.
Abinda ya bani mamaki yanzu duk ranar da zanje lecture sai dai kawai Naga Driver yazo yace Oga Ice ya turoshi,ashe time Table namu ya karba, kafin kace me na Zama babbar yarinya a mota kala kala ake kaini schl na Alfarma.yau ma Driver na zuwa nace ya na ganka da bakar motar Nan Bayan jiya na fada Masa Fara nake so ban son wannan bakar,Nan take na dakko wayata na kirashi bugu daya ya dauka cike da Muryar bacci Alama bacci yakeyi.
Pls Ni farar motar Nan Marcedes Benz nake so ba wannan Ba,karfin Hali ya furta a ransa Lallai wasu Basu iya samu ba,idan baza ki hau ba ki tafi a taxi, to Ni bazan Shiga ba ya dawo ma da motarka, banyi zaton zai amince ba,Nan take ya Kira Driver yace yazo ya dauki Farar ya kaini a ita.haka kuwa akayi Nan da Nan sai ga Driver da farar ya dawo ya kaini schl,tabara nakeyi iri iri Kuma Yana biye min Bai taba nuna gajiyawarsa.
Waya mukeyi da Ya Salman yake bani labari Danbature yazo last weak duk Wanda ya karbi takardunsu sun samu Babban aiki a cikin garin Gombe, sannan ya siya musu Dalla dallan motoci na zuwa aiki dake Basu da Nisa da cikin garin, Ya bawa Abbu jari me kauri da kudin gyaran gida.
Murna nakeyi son Danbature ya Kara kamani Nan na bawa Attine labari itama Murna tayi sosai tace wannan Mijin aure ne kinyi Dace samun irinsu sai an tona,mazan yanzu macen ma da ya suke Mata abin kirki bare danginta,wani ma da ya aureka sai ya koma yiwa danginka kallon banza.
Yau satina uku da komawa gidan Attine ban sake ganin Danbature ba,Wanda hakan ya jefani a damuwa,sai dai ko yaushe Driver dinsa ke kaini inda nake so, kwance nake saman 3seater Ina Danna waya,Attine Bata gida knocking naji na bude,kamshinsa ya bige Ni zuciyata tayi wani sanyi gefe na matsa na bashi hanya ba tare dana kalleshi ba,ledojine a hannunsa manya sunkai hudu na Shopping mall,Ajiyewa yayi ya zauna Yana nuna alamun ya gaji,Ina yini na gaidashi lfy Alhmdllh kawai yace Yana Bina da mayen kallonsa Wanda ke rikita ni.
Ruwa da lemo tare da farfesun kaji na kawo Masa na ajiye tire a gabansa,a ransa dama yunwa yake ji,a hankali yace wannan ai ba abinci bane,Allah yasa Pounded yam da miyar kwai Tasha Naman rago,kawo Masa nayi ya bude ya gani,Murmushi yayi kadan tare da furta da kin San da wannan Zaki bani wani Kaji.
Murmushi nayi Nima kadan tare da serving dinsa.
Ya Shiga ci sosai yayi missing girki na Ina gefe Ina satar kallonsa Ina Jin wani Dadi a Raina.
Bayan ya Gama lemon kawai yake kurba Yana lumshe ido, bude kayan ki gani,siyo Miki nayi Kar Allah ya kamani bana kula da matata, ledojin na Shiga dubawa kayane na sawa iri iri masu tsadar gaske, cosmetics,da inner wears,takalma da bags masu tsada, wata karamar Leda ya Miko min Atamfa super,lace da shadda tare da kudi dubu Hamsim yace na wannan matar ne da naji kina ce Mata Anty ance Yar uwarku ce, sabo da farin ciki kasa dannewa nayi na dinga washe Baki shi Kuma farin ciki ya kamashi na Yaba kyautarsa.
Dubu dari ya Miko min gashi in Zaki siya Abu,Kai na girgiza nace a'a,yace an kusa kaiki Gidana gwara ma ki karba,gabana ya Fadi ko shine Dalilin da ya kaishi kauyenmu again, Ya Salman yace ka samo musu aiki da sauransu mun gode...katseni yayi da Ina ruwanki wlh na fada Miki kima shirya Zan tona asiri kwanan Nan kowa a gidanmu zai San tsakaninmu.
Tsoro ya kamani nace Dan Allah kayi hakuri sai Nan gaba,ko gidanka kake so na tare to muyi a sirri pls,Mikewa yayi yace ki shirya Zan ballo ruwa kwana nan yayi waje abinsa.
Attine tana dawowa na kwashe komai na fada Mata,To sai me? Ke tsoronsu kike ji? In kina Haka sai Naga ma kamar ba kece kike damuwa da Danbature ba kamar Zaki kashe kanki a kansa,ga dama ta samu kin tsaya Shirme ko so kike ya auri wata ko ayi Masa Mata a danginsa,idan Zaki mike ma ki mike ki daina tsoro ki daura a niyar kula da mijinki,abinda ya faru ya rigada ya faru tunda har yanzu Yana sonki to karki yi Wasa da damarki,gyaran jiki zamu Fara Miki yanzu na Yan birni sannan mu koma kauye a kawoki dakinki kamar kowa gobe zamu fita akwai kawata me gyaran jiki.
Ni dai Jin Attine kawai nakeyi tsoro ya Gama kamani nasan tawa ta kare kawai sabo da Ni Naga abinda na gani bangaren Mum Ice,inda Bata kaunar wani ya rabe ta da jininta ace Ni danta guda ya aureni Ina Yar talakata talak.
Attine ce ta katse min tunani da idan Zaki mike da Addua ma ki mike sannan ki cire tsoron banza a ranki ki daina tunanin komai ki rike mijinki wlh ba Zama zaiyi baiyi aure ba an fada Miki jiranki zai tayi kina Masa Shirme Yana gajiya zai ajiyeki gefe ya auri wata ko Uwarsa ta kawo Masa wata Kuma ki Raina kanki kinsan dai Babansa Mijin tace ne sai abinda Anty Maryam tace dashi, kin zauna kina harkar kauyanci,Ni wlh yanda Naga kina sonsa Haka nayi tunanin duk yanda Zaki ki fara juyashi kin sani,Amma har yau an kasa wuce wajen haba.
Haka Attine ta dinga fada sosai Ina jinta.
Tunda Danbature ya koma gida ya kasa fita a motarsa yana ciki yana aikin tunanin yanda zai bullowa lamarin Zama tare Dani,yasan Mum dinsa baza ta yarda ba sannan idan Daddy ma ya yarda a banza tunda tafi karfinsa ita ke juyashi sai abinda tace,kakarsu kuma ba wata ta kirki bace,shi Kuma yana son Zama da matarsa ga Mum Kuma da tsafe tsafen masifa,ya Dade yana tunaninsa ya kasa samun Mafita gashi ya Gama tsantsara gidansa da zai zauna Kuma ga aure Yana bukata,sannan ga masoyiyarsa ta hakika ya samu tana sonsa ba Dan komai nasa ba Dan Allah wacce ta zauna dashi lokacin da ba kowa zai rabeshi ba,shi Taya zai iya biyan Fadila ma abinda tayi masa.
Fitowa yayi a fusace da sauri Hadi da kwarin gwiwar tinkarar Mahaifiyarsa ya fada Mata ko a mutu ko ayi Rai,fuuuuu yake tafiya cikin Takama Yana Shiga palonta yaji tana waya da bokanta tace ko wace matar tasa kawai a kashe min shegiya,yaron Nan Yana tarayya da ita komai nawa rushewa zaiyi, jikinsa ne yayi sanyi ya juyo baya a hankali ya dawo yace to shike Nan na fasa nuna matar ma kawai Addua zamu dage muyi zamanmu a boye suje su karata.
Kwana biyu in Banda tunanina ba abinda Danbature keyi,ya kasa sukuni gaba daya Yana tuna rayuwarmu a kauye lokacin Yana Mahaukaci,yanda nake kula dashi,bacci ma baya iya yinsa sosai,gani yakeyi wani zai iya kwace Masa Ni,kyawuna yake tunawa da yanda nake komai nawa a nutse,bacci ne ya kwasheshi da yamma lis,Bai farka ba sai 8pm wanka yayi tare da sallar Magrib da Isha,dazu cikin bacci ya tuna kwanciyar mu ta aure tun a kauye first night, dariya ya dinga yi Yana tuna irin dadin da yaji a hakan ma da Bai iya komai ba,kasa daurewa yayi ya mike zumbur kamar sabon kamu tare da zarar key din motarsa ya fito da sauri, Shehu Niga Yana Masa magana Amma ko saurarsa baiyi ba ya fada motarsa ya fita a dari Bai tsaya ko Ina ba sai gidanmu.
Attine yau tana sallar Isha tace bacci take ji ta wuce dakinta ta kwanta,Ni kadai ce a Palo da takardun karatuna a gabana Ina kallon Nigerian film,kwance nake saman carpet daga Ni sai Yar guntuwar Vest da wando 3qtr ya min Masifar kyau kamar wata balarabiya gashina na sakeshi rabi ya rufe min fuska so sexy.
Knocking naji tunanina mutanen Attine ne,Mikewa nayi na bude ba zato naji kamshinsa kafin nayi motsi yayi sama Dani kamar wata Baby ya daukeni,tare Dani ya zauna saman kujera,mene Haka idan Aunty ta fito fa?na furta Ina kallon kyawunsa, Ni da matata so what Dan ta gani, wajenta nazo ma fa Kira min ita za muyi maganar Kai min Amaryata.
Tunawa nayi da hudubar Attine kawai na mike na Shiga kitchen na kawo Masa kayan ci da Sha,Motsi nayi idonsa na kaina,duk inda na motsa,kunya duk ta kamani, bedroom na Shiga tare da Kiran Attine tazo,Waye da Daren Nan, Danbature ne fa,Au kice mijinki ne har yau Danbature kike fada Masa kema Allah shiryeki jeki Ina zuwa.