Sashe 13
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace wannan agogon a Ina na sameshi dake su babu boye boye nace na Mijina ne,tace zoben fa?nace shima Haka,tace Jesus yanzu kamata Haka Ina da aure?nace ae amma Mijin bama tare,tayi tunanin sakina yayi tace eyya sorry eh? Nace thank u.
Ta fadawa Dad da Mum tare da Emmanuela suka min jaje,tun daga lokacin suke Jin tausayina, suka ce a schl Ina na tsaya? Na nuna musu takardu na na ssce ,Ma tace zata sani a University makarantar kudi, na dinga murna na bugawa Attine waya na fada Mata taji dadi,Haka Yan gidanmu Ya Salman yafi kowa Murna.
Bayan na kwashe wata guda gidan Ma mun Saba dasu sosai,turanci na ya karu na fara kwarewa,ga albashina farko da aka min transfer naje na cire dake duk sati daya ko biyu Ina zuwa gidan Attine,Haka na Kai Mata albashina nace na Bata 20k na dauki dubu goma,da kyar ta karba sai da taga Raina ya baci ta karba.
Safarau ma Ina Kai Mata ziyara itama tazo min gidan Ma sau biyu,Bayan sati daya Ma ta kawo min Admission da komai anyi min registration a Health education zanyi Degree na Shekara uku,na fara zuwa schl ba,driver ke kaini ya dakko Ni, Emmanuela da Amaka suka ce ya kamata na waye na dinga matsewa cikin kana Nan Kaya,nace mu addininmu sai Miji ake sawa ko a gida,Haka suka suyo min Kaya kana na iri iri Amma bana sawa ganin Haka sai suka dinka min su atamfa da materials laces,shadda Riga da skert da dogayen riguna tare da mayafai na sirara masu kyau,takalma da jaka iri iri, idan kun ganni kamar bani ba,tsofaffin Kaya na Attine na kaiwa ta San yanda zata yi dasu.
Karatu da aikina nakeyi lfy lfy ya rage min tunani da yawa sosai na Kara girma,kiba skin Dina tayi fresh sai sheki nakeyi kullum kamar wata Amarya haka nake, ga Saloon Ina yawan zuwa Ana wanke min gashi na,lokacin dasu Amaka suka ga gashina haukacewa sukayi, Ma ta dinga mamaki kamar gashin Baturiya.
Yanzu tuni na dawo saman Benen Ma a Nan ta bani daki kusa Dana yaranta komai akwai kayan kwalliya iri iri,gashi Hawa biyu ne,Ma da mijinta a saman karshe yaranta a hawan farko.
Mun Gama girki munci mun Sha nayi Shirin kwanciya Bayan na Gama karatuna na mike jikin window na dake kallon gidajen waje kullum sai na leka na kalli unguwar da tsaruwarta.
Yau ma labile na zuge Ina tsaye da tea cup a Hannuna Ina kurba wani gida nake ta kallo nesa da mu sosai kaf unguwar Babu kamarsa a kyau duk da kyan na Ma ba komai bane Akan wancen gidan,wani daki na gani an kunna Kwan lantarki taram ya gauraye da haske,wata Yar aiki ce Naga ta wuce da plate, ta sake dawowa ta wuce tare da wata mace dattijuwa fara kamar Baturiya ban fiye gani tar tar ba Tunda da Nisa,Yar aikin ta sake ficewa Matar na gani ta saka jajayen kaya wani yadi kamar dodon tsafi Haka ta dawo Fuskarta ta rufe tana motsa bakinta da Alama magana takeyi,sai Naga ta Zama kamar horro ta Bace bat,tsoro ya kamani Bayan 30mnt sai na ganta wukil ta dawo inda take da wata tukunyar shirka a hannunta,ta ajiye tare da cire Kaya ta canja nata na farko ta kashe wuta duf sannan ta bar dakin,steal Ina tsaye bul Naga a dakin an Kara kunna light wannan namijine fari tar shima kamar Bature Amma Banga fuskarsa ba ya juya baya rigarsa ya cire gabana ya Fadi exertly jikin Danbaturena sai dai wannan yafi fari da mirjewar skin kamar ka tabashi jini ya fito,ko Dan Danbature a kauye muke ne ga Ciwon hauka shi yasa,ga wani uban gashi a kansa Wanda yasha askin irin shegun turawan Nan mawaka ko Yan film kyau iya kyau,gashin Nan Baki,shi ba gajere ba, ba Kuma dogo can ba,ba rammame ba ba siriri ba, so nake kawai ya juyo Naga fuskarsa, na bude kofata ta baya dama akwai corido Dan nafi kallonsa sosai na tsaya a Nan,barin wajen yayi ba tare da ya juyo fuskarsa ba ko yasan da wata tana kallonsa ba, ya Dade Nima Mayyar naki tafiya,sai gashi ya dawo sanye da rigar wanka fara Kal da Alama wanka yayi,jikin window dinsa ya tsaya shima dake facing nawa Amma Sam kasa yake kallo Bai kallo saitin gidanmu ba,
Gani nayi kamar Danbature ne ke min gizo nace Kai wannan idan ma ban samu Danbature ya dawo ba to Naga Mijin aure,Dole ne ma ya aureni tunda suna Kama, Dole na San yanda zanyi na Kulla alaka dashi, Kuma sai Naga Danbature na kamar yafi wannan kyau da komai,sannan ya fishi kira da cikar zati har ma kwarjini da komaima.
Da karfi na kwalla tare da Mika Hannuna Ina tsalle nace Danbature......Baturena .....kaiiiiii.....Dan fari ....juyo.....Nan...gani .....kalleni......Kai......Malam.....nice Fadila......dolene ka aureni......gaba daya dake dare ne duk kusan layin wasu da dama sunji Ni, amma ba wasu Hausawa Basu san me nake cewa ba,shi kanshi Wanda nakeyi dominsa Bai ji ba gani nayi ma an kawo Masa lemo Yana kurba Yana shafa sumarsa, dagowa yayi kadan sai da na firgita da kyansa, wannan ai Danbature yafi shi, Amma suna mugun Kama, wata budurwa na gani itama zukekiyar gaske fara tas tazo ta rungumeshi ta baya.
A fili nace na Shiga uku kaga tsinanniya Karuwa,Anya wannan ko dai Matarsa ce wash na dafe kirjina, kishinta naji na Kara kwallawa da karfi Ina nunata da yatsa kee....Mayya....matsa daga jikinsa....Mijina..nane....Arniya.....Arniya....Allah ya tsine Miki na Kara tsalle kamar zararriya na Dane karfen jikin corridor din nace Mayya....ke...uwarki Ina Mata dakuwa kuwa Allah yasa karaf ta hango,ban hakura ba nace karbi Nan ungo na Kara Mata zagi da tafin Hannuna Ambola dakuwa.
Kirjinta ta dafe kamar taga Aljana tayiwa Namijin nuni da ya kalli Aljanna a sama can gidan,ai kuwa ya kallo wajena gabana yayi mugun bugawa daram kamar Danbature,Amma Ina wannan ya take Danbaturena kyan fata sabo da hutu ya ratsashi,na tabbatar da Danbature ne ya samu hutu Haka to ya ninka wannan komai,to me ma zai kawo shi Lagos.
Haka na dake na nuna shi da yatsa sannan na sarke yatsuna kana Nan biyu maanar aure, Ido ya zaro,kiss nayi Masa ta iska sannan na hura Masa ta iska, dariya ta kamashi sai yayi Alama shima ya cafke ya lika a zuciyarsa dariya na kyalkyale da ita na tafa Masa sannan na daga Masa Babban yatsa irin Good. Tunawa nayi Ina da aure fa sai na fara istigifari.
Budurwarce ta dinga kwasa dariya tana ganin haukata gani Yar yarinya tace kawai irin Yan iskan yaran Nan ne kawai yayan masu kudi fasikai,shima Haka yayi tunani sai Naga sun koma ciki matar ta fice shi Kuma ya gyara labilensa tare da kashe light alamar ya kwanta.
Ban taba samun jindadi irin wannan ba Tunda nake a duniya sai lokacin da muke tare da Danbature na,fes nayi bacci na tashi,inayin sallah da azkhar na Kara lekawa ta kofar dake dakina ta baya ko zanga me kama da Danbature Amma ban ganshi ba gani nayi ma an rufe window din ruf,jiki ba laka na wuce kitchen inda na iske Ma ta fara aikin,na gaisheta muka ci gaba da aikinmu Ina ta faman tunanin Danbature da mutumin jiya me kama dashi.
Bayan na Gama komai nayi Shirin schl na wuce,su Ma da yaranta duk sun wuce Office Suma ba zama.karatuna nakeyi sosai.
Yau ma dai dai lokacin jiya da dare Naga me kama da Mijina ya sake fitowa Yana Shan iska direct window na yake ta faman kallo,katsam na sake Nima fitowa, hannu na daga Masa shima ya dago min Yana Murmushi,Alama ya min wai na sakko na zagayo gidansu,kafada na makale nace sai dai shi yazo, katuwar paper ta Zane ya dakko ya min rubutu da Babban Baki Ur Name pls? Nima na rubuta na nuna Masa ya karanta Fadila.
Hausa girl ko? Ya sake nuna min,Nima nace ae Ashe kana Jin Hausa? Yace ae Babanmu bahaushe ne mun zauna a Kano,Adamawa, jigawa duk gidanmu kowa najin Hausa nace to yayi kyau.
A Haka muka dinga Hira sosai cike da nishadi Ina magana da me kama da Mijina.
Yau mun kwashe kusan sati Uku kullum sai munyi Hira da wannan mutumin Wanda yace min sunansa Doctor who ake ce Masa,kowa na tambaya Dr Who za a nuna min shi da gidansu.
Sosai muka Saba da juna, Amma dare daya ya nuna min manufarsa Yana so yayi xxx Dani shi manemin matane tun daga lokacin naji bana sonsa na tsaneshi, ba wani boye boye yazo wajena har gidan Ijeoma ya fada min halayensa da niyyarsa a kaina,zuwansa wajena biyar tunda Naga ba mutumin kirki bane na daina saurararsa Amma Kuma sai suna matukar Kama da Danbature.
Ijeoma tayi mamakin alakata da yaron masu kudi Haka Wanda Babu kamarsu a Lagos, ji akeyi dasu kowa yasan da zamansu.
Yau Sunday kowa Yana gida yau Amaka zata kawo Mana saurayinta Dan Rivers Wanda tare sukayi karatu a turai Kuma shi zata aura,sosai aka shirya Masa liyafa,matashin Igbo me kudi gurjeje dashi katon Arne, yazo Ni nayi serving Nasa abinci Wanda sai kallo na yakeyi kamar maye,Silvester sunansa Ma tabar Palon,Emmanuella Bata nan,Amaka ta mike tace Bari ta dakko wayarta zata Kira Emmanuella tazo taga mijinta,Yana ganin Haka ya matso kusa Dani Yana fada min wai yanzu Ni yake so nafi matar da zai Aura Amaka kyau,Amaka karaf a kunnenta da ihu ta karaso tare da rufe Ni da duka Evil hausa girl, Silvester da sauri ya bar gidanta, Amaka tace zamu hadu da Kai I will kill u.