← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 50

Sashe 37

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawai kwanciya yayi saman bed tare da manne min a jikina,ya fara shehekar kuka shima da Wasa Sautin nasa ya zarta nawa,idan na Kara vol sai ya Kara shima idan na canja salo shima ya canja ban San sanda Dariya ta kwace min ba Ina goge hawayena,jikinsa ya janyoni shima Yana dariyar farin ciki ganin ya bani dariya, harshensa yasa Yana lashe min hawayena, Yana shafa jikina Ni kaina rigarsa na cire Masa muna murzar juna da zafi zafi kafin kace me wasan ya canja salo saida muka shayar da junanmu madarar dadi sannan mukayi wanka muka kyashe cikin Kaya na alfarma,kyan Dana yi ba a magana cikin Gown hadaddiya da kadan ta haura mazaunai na.
Cinyoyina lukuta lukuta suna sheki da walwali, cikin wasu arnayen kana Nan Kaya ya shirya Wanda idan ka kalleshi sai ka sake,kishinsa naji zai fita Yan Matan gidansu dangi su kalle min shi ko Matan gari.

Tagumi nayi a gefen bed Ina zaune,kusa Dani ya zauna tare da cire min hannayen danayi tagumi dasu,yace Mene Haka kuma Darling? Hawaye ne ya kwararo min,Wanda shima ji yake kamar yayi kuka sabo da abinda yake ji a ransa kamar zamu rabu gaba daya.

A hankali yace Wai ya kike so nayi da Raina ne? Kin San fa matsalata kin San komai, maimakon ki kwantar min da hankali sai dai ki Kara daga min shi,so kike na zauna Mum ta gano shike Nan na Shiga uku,kin San ta wlh zata iya tsine min,Ina so na rabu da mahaifiyata lfy sannan Daddy shima Haka ke dai kin San komai,Nima ba so nake na rabu dake ba,kullum fa zanzo na ganki,sannan maybe ma Kullum ki ganni a schl dinku,kiyi hakuri muyi manage kafin komai ya Zama normal,da ace bana sonki bazan shirya hakan har ki tare ba,Ina matukar kaunarki,Ina sonki Babyna ya furta Yana shafa gefen fuskata,Kinga na siyo Miki sabuwar waya me tsada iPhone,ga laptop ma sabuwa,kalla kiga duk kayane Nan iri iri na siyo Miki,Kuma zamuyi ta waya ba adadi ga video call duk kullum zamuna yi kafin nazo da yamma,ba abinda zai Raba mu,ga Yan aiki Nan Mata biyu maza biyu sai ki Kira daya Nan part din ta dinga tayaki Zama da kwana Kuna Hira yanda baza kiji tsoro ba ok? Kai na daga Masa alamar ae.

Zanyi missing naki abincina karki manta da yamma 5pm Zan na zuwa Ina cin me Dadi wajenki,karki manta ko mene kafin ki aikata ki fada min a waya,karki Bari asan muna da alaka,idan asirina ya Tonu Mum wlh tsine min zatayi yanzu ma gaf take da tsine min,ki dinga Taya Ni Addua kullum kina yi Mana,ki dage da Addini na sanki da addini ba matsala,karatun boko ma ki dage,sannan yau din Nan dake Zan tafi Zan saukeki kusa da gidanmu Bayan na Shiga sai kema kije gidan wurin Nanee kice gaisheta kika zo,idan kinje kice daga kauye kika zo wajen Attine kika biyo ku gaisa,pls ki Kara kwantarwa da Nanee hankali,kije wajen Mum kice kin kawo Mata mijinki Zan hadaki da wani Wanda Zaki Kai Mata a shine Mijin naki,lokacin hankalinta zai kwanta baza ta dinga bincike na ba,yanzu ma nasan Ni take jira na koma taci ubana,kwanciyar hankalina kawai kuje da wani a matsayin shine Mijin naki,idan kin fito ki hau taxi ki tafi gida shima Mijin aro yayi nasa waje.
Acting zakiyi sosai yanda zamu sata a rudu, pls Kar a samu matsala.

Hmm to ai ya kamata duk Yan gidanku na nuna musu shi a matsayin shine Mijina na kawoshi su gaisa ba Mum kadai ba yanda zasu rage sa Ido,sannan bazance daga kauye nake ba,an Gama biki a kauye a Lagos muke zaune dashi Dan cirani ne na aureshi.
Dariya yayi tare da cewa Good Idea tashi ki shirya mu tafi.

Cikin atamfa da katon Hijab na shirya irin shigar matar me karamin karfi nayi na fito muna dariya,Nan ya bugawa Wanda Zan Maida a matsayin Mijin nawa, waya ya kira yace Sa'ad dauki taxi kawai mu hadu a kusa da gidanmu,kayi Shiga kalar me rufin asiri Kai ba talaka ba bakuma me kudi ba.
Kashe kayan wuta mukayi muka fita da kansa yakeyi Driving Ina gaban mota hannunsa cikin nawa,sai da ya tsaya ya siya min tsarabar da Zan bawa Nanee,Asiya,da Mum.
Mun kusa da gidansu ya tsaya yace na fita sai ga Saad da Taxi Kyakyawan guy ne shima ga iya wanka,na Shiga Bayan mota da tsarabata a Leda katuwa,shi kuma Saad muka gaisa ya shige gaban mota.
Danbaturena yace ku fara zuwa Ni a karshe zanzo lokacin da zaku tafi Zan shigo,zanyi muku muzurai tare da wulakanci kawai kamar a film zamuyi kun gane,Saad yace an wuce wajen,Nan muka yi gaba,shi Kuma ya dauke hanya ya tafi wajen Ayman closefrnd nasa.

Kofar gidan muka tsaya,Masu gadi sun sanni ba Bata lokaci suka bude Mana muka Shiga Bayan min gaisa dasu nace ga Mijina Saad suka gaisa tare da tayani murna.
Text din Danbature ne ya shigo wayata na duba,Yar Balarabiyata karfa ki zake ko kallonsa karkiyi wlh I'm so Jealous, tunaninki nakeyi kina fadar wani ne mijinki ba Ni ba.
Murmushi nayi na Masa reply da Hmm Never Mind My Husband it's just a game kafi kowa sanin yanda nake tsare maka darajar aurenka a kaina tun ban San Zan sake ganinka ba.

Text ya turawa Saad yace karka kallarmin Mata Malam dake shima abokinsu ne sama sama Babu Wanda ya sanshi a family na Ice,dariya Saad yayi Amma a ransa wani birgeshi nakeyi,gaskiya Ice ya samu mace ta nunawa,sai yaji dama da gaske shine Mijin wannan Kyakyawa Fadila.
Anya kuwa bazai San ya zaiyi Mum tasan zancen ba tasa Ice ya sakeni shi Kuma ya aureni.
Shawarar da yake tayi kenan a ransa kafin Saddiqa ta yanke Masa tunani da sallamarta ban santa ba,itama Bata sanni ba,Amma gaskiya itama Saddiqa Kyakyawa ce ba laifi.
Ta kalleni tace Kai tunda nazo garin Nan Banga ta gari ba sai ku,ke gaki da Hijab har kasa,shi Kuma yasha shadda da hula kamar a Kano state,yau Naga mutanen kwarai na gari a Lagos wlh sai kin Zama kawata Dole ma tana tafi da hannunta.
Dariya ta bani kawai na wuceta nace muje Saad muyi sauri,Har Saddiqa ta biyo bayanmu tace sai na rakaki Nima,wajen wa kika zo a gidan Nan?.

AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

71-75

Official

By
AsmaBaffa

Raliya Nura Lawal,Nomah zinatu,Maman Ameer,Zeenarp Deenawah,Hadiza Hussaini, Binta Nadada.ga page dinku fans.

Murmushi na sakarwa Saddiqa sabo da mate dina ce ba wata Babba bace nace nayi aiki a gidan Nan ne naje nayi aure yanzu ma Mijina na kawo musu su gaisa,Eyya gashi kuwa Kyakyawa kinyi Dace Allah Sanya Alkhairi.
Ameen nace Muka fara Shiga part din Nanee, Tana Main Palo duk ta rame tayi duhu ga dai kwalliya Tasha Amma kana kallonta kasan tana cikin matsala,Tausayinta ya kamani, da matukar murna ta karbe mu,kafin kace me an cika Mana gabanmu da kayan ci da Sha,abin haushi Saad sai Zama yake kusa Dani kamar zai shige jikina abin nasa ya fara Bata min Rai dannewa kawai nake yi.
Nanee ga Mijina na kawo Muku muna Nan Lagos a zaune Yana Dan kasuwanci,Allah sarki gaskiya kinyi Dace cewar Nanee,Yar Hira mukayi sama sama sannan muka shige Bedroom daga Ni sai Nanee ta daukeni kamar yarta ta bani labarin halin da take ciki, naji Tausayinta abin yafi da yawa gaba gaba yake,na Shiga Bata hakuri tare da kwantar Mata da hankali komai zai wuce,ko ba komai ta rage jin radadi sannan na Mata Nasiha sosai sabo da taji kwarin gwiwa, nace komai da kika gani Nanee me wucewa ne,duniyar nawa take? Komai yazo Dole zaiyi karshe,ki daina damun kanki.
Murmushi tayi tace dadina dake Hankali Fadila naso ace Dana Ice ne ya aureki ya Samu mace irinki ai mutum ya dace.

Muna ta Hira da ita sosai kafin nace Bari zamu tafi zanje na gaisar dasu Mum watarana Zan dawo na Miki yini Ni kadai tunda Ina gari,Allah ya kaimu Fadila Nima zanzo gidan naki watarana, ok Allah ya kaimu na Bata turarukan Da Aliyu ya siya yace na bata taji dadi kuwa tana Godiya duk da cewa ba wasu masu tsada bane sabo da a masu rufin asiri muka je musu.
Saddiqa tana wajen Saad sai surutu take Masa Ina Fitowa muka tafi part din Karimatu, tayi mamakin ya akayi na Samu miji me kyau Haka Kuma baiyi kalar talaka ba Sam,Bata San Wanda na aura Babu irinshi a Nigeria ba,da ace tasan Danbature ne Mijina Lallai da sai ta Suma,Saad ko Kama yatsan Danbature baiyi ba a haduwa Amma sabo da ta rainani mamaki takeyi sabo da talaka sai talaka,me kudi sai me kudi, sama sama ta karbe mu ko ruwa Bata bamu ba,na Bata tsaraba sai tabe Baki da tayi tace ajiye shi can kujera na dauka.
Ajiye Mata nayi mukayi Mata sallama,Saad yace sai part din Mum din Ice ko? Kai kawai na daga Masa Sam bana son shige min da yake gaf da jikina.
Part din Aunty Maryam muka Shiga da Sallama,a zabure ta mike zumbur,Nan muka iske Murja,Hanna da Hanifa sunzo part din da yaransu suna hira, wuri muka samu tare da Zama muka gaisa tare dasu Hanifa na sansu a pics nace kunzo ke Nan? Hmm ae wlh kece mewa Nanee girki kwanakin baya ko?
Ae nace da Faraa Ina daukan yaransu daya Bayan daya Ina musu Wasa nace Mum ga Mijina na kawo Muku ku gaisa,Da faraa Su Hanna suka gaisa tare da yi Mana Allah Sanya Alkhairi,Aunty Maryam ta Shiga rudani gaskiya yau ta tabbatar bokaye makaryata ne,ga zahiri yarinya ta kawo Mijinta,ta daina zargin Fadila, Saad kuwa a zuciyarsa sai sake sake yakeyi Taya zai Rusa wannan aure shi yazo ya aureni.
Sabo da murna Mum har da dariya Ana janmu da Hira,nace Mijina fruits yake siyarwa a kasuwa shine muke zaune a Lagos,Baki ta washe tare da cewa yayi kyau,gashi Ice baya Nan Amma yau zai dawo shima,kamar gaske na tabe Baki tare da tambaya waye ma Ice tace Dana Aliyu ko kin manta shi, Ohhhhh na tuna shi yanzu, na share zancen sabo da na Gama ganeta wayo ta hada min ta gani ko Ina da alaka dashi.
Chapter 37 · 0% Book details