Sashe 23
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motoci a Gombe rantsatsun gaske biyu da securities suna binmu a baya,Wai baya Shiga kauye ba tare da tsaro ba,mutanen kauye suna da matsala aje a dakeshi a banza,sai na tuna sanda su Ya Musa suka Masa duka Yana Mahaukaci lokacin.
Har kauyenmu Ina nuna musu hanya.
Readers anan za a yita fa.
AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕
36-40
Official
By
AsmaBaffa
Page dina ne Asmabaffa🤣 Allah ya ji kan Baffa Ameen.
Motocin kawai ake bi da kallo a kauyen Ana tunanin ko wani Senotor ne,ga tint ba a iya ganin kowa na cikin motar, a hankali ya kalleni yaga Ina ta washe Baki, Baki ya tabe na kalleshi nace na gode Dan Albarka Murmushi yayi kawai ba shiri,nace zaka ji Ana ce maka Danbature Dan Allah ka rufa min asiri kace Kaine kawai,ka yarda a Kaine Mijin nawa,idan ba Haka ba Ina cikin tozarta a kauyen Nan,ko me sukace kace are hane, ko kaji na fada Dan Allah kace hakane kawai,Bai ce komai ba kawai na dinga rokonsa Amma Bai ce zaiyi ba baice bazaiyi ba,Haka na hakura jiki na yayi sanyi nasan idan yace ba shine ba dariya za Amin ayi ta gulma.
A kofar gidanmu nace ayi parking,Bayan mun tsaya na hango Ya Salman,Mahmood,da Musa a majalasarsu da suka Saba zama sunyi kyau da kiba,da sauri na fita a motar,Ya Salman na Kira tun kafin na Karasa.
Suka juyo gaba daya suka ga wata balarabiya da kyar suka gane nice,Ina karasawa na Mikawa Ya Salman hannu muka tafa,yace ko waya babu? Nace surprise na muku,Musa yace kin ganki kuwa haduwa,Mahmood yace da alama an manta da Danbature tunda Baki Kara Mana zancenba ko a waya ga kiba da kyau,wannan ya nuna tunaninsa ya Kare,nace hmm da bako muke fa Bari na kirashi,Motar na koma nace ya fito,yau shigar Wani Yard yayi me tsadar gaske,fadar kyansa Bata Baki ne, kafin kace me Mutane da Yara sun Fara cika wajen ganin Fadila da motoci harda securities.
DanBature ya zuro kafara daya daga mota Bayan an bude Masa Kofa,takalminsa kawai ya Isheka kallo,kamshinsa ya feso a garin,fitowa yayi daga motar kowa yace wlh Bature ne daga kasar waje,wasu suka Fara Fadila tazo tare da Bature,wasu suce ai kasar waje taje watakil suka taho tare,Amma da suka kalleshi sosai sai sukace mijinta ne Danbature Mahaukaci ya warke,ta Nemo mijinta.
Gari ya dauka ko Ina, Danbature kallonsu kawai yake yana Jin duk me ake cewa,to Wai shi yaushe yayi Ciwon hauka ne? Ya Salman gaba dayansu da murna suka tarbi Danbature suna Alhmdllh ya warke,sannu ya jiki? Fadila ya akayi ya warke? Nace ai tunda ya bar garin Nan ya warke gidansu ya koma,Ni Kuma a Lagos naje gidansu a Yar aiki me dafa Masa abinci sai muka hadu muka sake jonewa,yanzu yace muzo yana son yaga dangin Matarsa da garinmu.
Sukace Alhmdllh gaskiya munji Dadi,Danbature Yana gefe yayi galala kawai Yana ji Yana tunani shi ya za ace yayi aure,kawai Shuru yayi yace in sun gaji sa gane gaskiya.
Cikin gidanmu muka Shiga har Danbature Yana gaba kamar yasan gidan,na matsa kusa dashi muka jera Dan ace gaskiyane maganata.
Hajiyarmu ce taji kamshi ya bude gida,tana daga daki take kwallawa da karfi tare da masifa Kai Musa turaren da Hajiya Yabi ta kawo min tsarabar Makkah ka sace min ko,sai da na gargadeka to ka dawo dashi ko naci mut.....Sallama Danbature yayi cikin kasa da murya, kunya duk ta kamamu har su Ya Salman Sabo da yanda Hajiyarmu ke faman zazzago masifa daga dakinta, Sallamarma da fada ta amsa,Dan Palon da Abbu ke karbar Baki muka bude yasha gyara kuwa Yana kamshin turaren wuta gashi carpet ne me kyau kawai a ciki,sai wata makekiyar katifa sabuwa ga tudu ga Fadi Tasha bedsheet,Dan Bature ya zauna gefen katifar, ya Salman ya Kira Hajiyarmu,Anty kuwa tana dakin Abbu suna tare,Ya Musa ya kirawosu.
tuni nayi waje zanga Hajiyarmu,tana ganina tace Fadila kece kika dawo Haka? tana murna sosai muka gaisa sannan nace tazo da bako nazo,Abbu da Anty sun fito suka ganni,da kyar suka gane ni,Abbu Fadila ce fa da bako muke,Nan na tsuguna na gaidasu, Anty ta rasa ma Ina kanta yake ko me zata ce ma ba Baki.
Suna Shiga Abbu,Anty,da Hajiyarmu numfashinsu daukewa yayi na wucin gadi da suka gane Danbature Haka,Abbu a fili yace Lallai yanzu kake Danbature ba da ba,ikon Allah cewar Anty,Hajiyarmu tace Kai Dan Nan yaushe ka warke Haka? Abbu yace Sannu da jiki kasha jiki, Anty kuwa ganin Danbature me kudi haka tace oh ai mun Sha fama da Kai,har na tuna sanda muke tallafa maka da abinci, oh sai da jarin Zobo na da kunun Zaki ya karye a kanka,Haka Fadila take zuwa ta kwashi na dari uku taje ta tarairayeka kamar jariri ta baka ka zuke.
Allah sarki ai ansha fama ka godewa Allah ka rugurguza jarin bayin Allah da dama, Yaron Nan Talle me Lemo kankanarsa kullum ba yankewa, Abbu ya kafe Danbature da Ido yace to yaro Wai ya akayi ne Fadila yi Mana bayani Yata Ina kika tsinto abinki? Yanda na bawa su Ya Salman labarin karya Haka na sake bada labari.
Abbu yace Allah me iko Yar Nan a kansa kika kaini Kara wajen Yan Hisba oh...yiiii Abbu ya fashe da kuka yaga kudi Wai Dan a tallafa masa,Shi dai Danbature kansa ya kulle Haka kawai a dinga kala Masa cutar Hauka,Ba yanda zaice su yarda kawai sai ya karbi taimakona ya sauka kasa sosai ya gaishe da Abbu dasu Hajiyarmu kamar gaske,Dadi ya kamani, yace Alhmdllh na gode kwarai da kulawarku a kaina na warke yanzu Kuma Allah ya hadani da wife dina nazo dama na ganku ne na kawo gaisuwa.
Anty tace ba komai wlh sannu da kokari ai kasha jiki,Hajiyarmu tace jarin goro da yarinyar Nan ta karya min a kanka ya baci,Dan kudina ta bankada pillow ta dauke ta siyo maka kayan dadi,kunya ta Kara kamamu yanda iyayenmu ke zubar da mutuncinsu gaban suriki, Ya Salman tuni Sunyi waje sai gasu da lemo kala uku harda Maltina,Ruwan roba.
Hajiyarmu tace gashi tuwon shinkafa mukayi miyar kubewa danya ban sani ba ko baya ci,Murmushi nayi nace ai wannan da kike gani saukin Kai gareshi zai ci.
Haka na kawo Masa tuwo Nima na ebo nawa,baya son ci Amma sabo da Kar suji Haushi na dinga Masa signa da Ido da kyar ya daure yaci kadan, yace to in kin Gama mu wuce ko? Abbu yace Haba Haba kawai ku kwana gobe sai ku tafi Amma kuzo yau ku koma yau bazai yiwu ba sai Gobe,kamar yayi kuka Haka yaji.
Abbu mamaki ya hana zuciyarsa sukuni tunda ya fita waje yaga motoci da Sojoji, Anty da Hajiyarmu suka leko suka Sha kallo, Allahu Akbar kaga kudi inda suke ,kudi na inda suke cewar Hajiyarmu yaro kamar shi yayi kansa,nayi dacen suruki,Anty bakin ciki tuni ya cika Mata zuciya Yar kishiyarta ta samu me kudi,Hajiyarmu ta kalla shekeke tace ke mene bakiwa mahaukacin ba? Kin manta Sanda kike cewa karta zuba Masa abinci a kwanonki me kyau sai dai ta dauki tsohuwar langa wacce ta farfashe tayi kwatsa kwatsa shine yanzu anga kudi ko? Hajiyarmu sarkin fada Nan suka fara musayar yawu sai da Ya Salman yazo ya musu fada,Ina dakin da Danbature yake muna Jin fadansu rangadadau kunya duk ta rufe ni,Abbu ma Yana ji muna tare ya mike ya fita Yana kaci abinci Aliyu kaji,tunda Danbature ya shugo baiyi ko digon Murmushi ba sai sau daya da zai gaishe da iyayena.
Su Ya Salman ma ganin ba wata magana yake ba sai Izzar tsiya sukayi waje abinsu,Ya Mahmood yace cuta ma fa tana tarar da Hali,ko sanda yake da tabin kai karku manta haka yake,baya magana sosai sannan baya wata dariya sai in Fadila ya gani itama ba sosai yake Mata ba.
Shuru yayi Yana ta faman tunani shi yaga ta kansa har yaushe yayi Ciwon hauka aka Masa aure karya ne bashi bane da sauri ya kautar da tunaninsa cewar karya ne kawai dai zai taimaka a bar kauyen a Haka.
Abincin fa?nace Masa kadan ya kalleni yace kin san Ni bana cin tuwo ko dazu ma karfin Hali nayi naci, a gida Kuma Haka nake bawai ko wani abu ba, ledoji bakake na ebo a jaka ta na shirya su tuwon da aka kawo Masa na kwashe rabi a leda,miyar ma Haka na daure nayi Leda cikin Leda yanda baza bule ba na bude Yar jakata ta kayan sawa na saka a ciki na zuge idan min fita sai na jefar.
Na zauna gefe naci nawa,na kwashe kwaninkan na maida musu kaf,sai Murna Hajiyarmu take ta bude kwanonsa tace yaci Ashe Kai gaskiya baida kyankyami,waya yayiwa securities kawai su koma cikin garin Gombe gobe sai su dawo,shi ya zaiyi ance sai ya kwana, shi ya jawowa kansa daya biyo Ni yazo kauyen.
Da yamma Abbu yace sai mu fito mu zaga dangin iyaye,ba yanda ya iya Bayan munyi Sallar laasar muka fito, sai da muka Isa can Bayan gari daga Ni sai shi da ruwan roba a hannunsa yace jira Kuma ki juya bayanki fitsari zanyi,nace da ka Shiga toilet tun a gida yace bazan iya ba ko wanka bazan yi ba har mu tafi gobe, Shuru nayi kawai na juya bayana yayi fitsarinsa da tsarki yace muje.
Muna tafiya Ina Masa labarin irin yanda mukayi rayuwa da Danbature na Yana mahaukacinsa Ina nuna Masa wuraren da yake Zama da yanda yake komai,nayi hakane Dan ya tuna Amma saima dariya da yake kwasa watarana kuma yaji tausayina,Gidan da me gari ya bamu mukayi rayuwar aure na kaishi Ya Salman na Kira a waya nace ya karbo min aron key wajen Mai gari zamu dauki wasu Kaya, Aiko cikin sa'a ya bayar na bude gidan duk yayi kura komai namu Yana Nan inda yake nace ga gidanmu da muka zauna dashi kalli komai Yana Nan,muka Shiga na nuna Masa ko Ina,Yana mamakin rayuwa da Mahaukaci.
Shuru Aliyu Bai ko San munyi rayuwa a gidan ba,yace na jinjina Miki da kika iya kula dashi Haka,Allah ya dawo Miki dashi Kuma Allah yasa ya soki shima kamar yanda kike sonsa,Allah yasa ya Miki son da yafi Wanda kike Masa.