Sashe 32
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddyn su Ice ya dawo daga tafiya,Asiya tana ganin wulakanci ta koma banza a gidan yanzu badan Danbature ba da sai dai da kanta ta bar gidan,Amma shi ya tsaya Mata ya hanata tafiya komai shi ke Mata tare da danginta.
Saddiqa uwar masifa kwalar Sadiya taci akan zasu sa Mata Sunan banzan da suka saba sawa mutane,Saddiqa tace wlh duk tsinanniyar data Sa min suna sai mun kwashi masifa da ita,sunana Saddiqa dashi ubana ya yanka min rago Dan Haka Banga wata Yar katuwa ko Dan Kato daya Isa ya lakaba min suna ba.
Da kyar aka kwaci Sadiya hannun Saddiqa, ba a Gama hucewa ba sai ga Mum Ice tare da kawarta Linda suna busa hayakin wiwi zasu Shiga mota.
Baki Saddiqa ta bude da sauri ta Sha gabansu tace ba tsari Sam Bai Dace ba,tabar ma baza ku Sha a daki ba sai a cikin gida, bazai yuwu a lalata Mana tarbiya ba..kau...Linda ta wanketa da Mari,Nan take ta fashe da kuka da karfi tare da Kara bude Muryarta duk har masu gadi suna ji daga na Fadi gaskiya ki Bari matar me gidan ta mareni ba Ke ba Yar karere me gashin arna,mutanen gidan duk suka yo waje har Danbature ya leko ta saman window dinsa,shi wlh Dadi ma yaji da Allah ya kawo Saddiqa Yar kunan bakin wake,marar tsoro da zata dinga fadar gaskiya ko a mutu ko ayi Rai.
Shi kanshi Dr who yau Saddiqa ta birgeshi dama an rasa me fadawa Mum dinsu gaskiya.
Saddiqa tace Yan shaye shaye,asha taba asha giya,kwayoyi ma ba a barsu ba,ga tsafi da bibiyar maza wlh aji tsoron Allah duk ranar da duniya ta juya muku baya hmh...Meena kanwar su Ice ce tazo ta fara dukan Saddiqa,Saddiqa girman kauye Hankalinta kadan ne ta Kama Meena ta dinga masgarta kamar Allah ne ya Aiko ta.
Mum Ice tasa guards dinta suka kama Saddiqa Suka Mata jina jina, Ice ne yazo ya kwace ta Amma taji jiki.
Saddiqa tana kuka tace Ni gidanmu Zan tafi kauye yiiiii...Dr who sai dariya yake mata, Danbature kuwa tuni yayi tafiyarsa ya barsu tare da Dr who,Saddiqa ta gallawa Dr who Harara tare da cewa Kai Wai wani na gari ne? Lalatacce ta furta a hankali tayi gaba.
Tunda Danbature ya bar gidanmu Dana rakashi Bai sake dawowa ba sai Ana gobe Zan tare a gidansa ya kirani a waya Wai na hadashi da Anty,yace Driver zaizo ya dauke mu gobe daga Ni sai ita a kaini dakin miji,Attine tace na Kira frnds dina Mata kamar guda uku su rakani Suma, na fadawa schl mate dina Wanda muke shiri Yan gayu dasu,Washe gari da misalin takwas na dare Bayan munyi Sallar Isha mun Gama Shiri harda Safarau Yar Attine muka je gidan make up aka yi min ta gani ta fada har daurin dankwali nayi azabar kyau,muna dawowa kawayena sunzo tuni kowa ya shirya,motoci rantsatsu guda uku ne da suka zo daukan Amarya ciki harda Ayman Best frnd na Ango a motarsa aka sani,kayana kaf da nake bukata Attine tasa a mota suka Shiga muka tafi.
Ina ciki Attine sai Nasiha take min, gidan da mukaje sai da abin ya firgita mu,unguwar kanta abar a bada labari ce,Haka gidan gaba daya susucewa mukayi, ko a film bamu taba ganin gida hadadde irin wannan ba,ya tsaru karshe,Maaikata sai gyare gyare sukeyi a ko Ina kamshi kawai ke tashi, wannan gidan Attine ya min girma ai tsoro zanji na furta,Attine dariya take min wai Yar kauye ,Koda muka fito a mota bamu Shiga ba muka bige da kallon gida muna zagawa sai pics muke dauka iri iri da kawayena,duk inda muka je Sai munyi selfie, palon farko munyi pics ba adadi,Frnds sai santin gidan sukeyi.
Muna haurawa sama Bedroom dinsa sai Baki muka saki muna kallo kallo,Haka na zabi dakina Nima a sama,abin farin ciki harda lifter idan baka son bi ta steps.
Kitchen ba kala daya ba,Palo sunkai kala biyar,bedrooms gasu Nan ko wanne yaji Kaya,garden yasha grass carpet, swimming pool har biyu ko wanne tsarinsa daban, parking space motoci ne gasu Nan laba laba.
Sai da Ayman ya dinga magana su fito a maida su sai da kyar suka fita,Safarau taki daina daukan pics dariya Ayman yake ta faman yi ganin Amarya kamar ba Amarya ba sai harkokina nakeyi a gidan.
Bayan munyi Sallama sun tafi sun barni ko kewar su Attine banji ba sabo da gida ya tafi da Imani na,ba Bata lokaci na shirya kayana,akwatunan lefe na gasu Nan reras goma Sha hudu su Attine sun kallesu Sunyi kaca kaca da kayan,duk na gyara abina na Gama komai sannan na gyara kwalliyata tare da feshe jikina da turaruka na hau saman bed na nutsu na zauna tare da rufe kaina kamar Saliha.
Karar mota naji alamar ko Danbature ne yazo Bayan ya sheka karya ya fadawa Mum cewar ya tafi Kenya business Nan da 2wks zai dawo,Su Nanee ma duk sun yarda ya tafi Kenya yayi Haka ne Dan kar a neme shi a rasa Mum ta fara bibiyarsa, kamar Gaske yasa Ayman ya daukeshi yace ai tare zasu tafi da Ayman.
Farin ciki nake ji yau Wai nice a gidan Danbature ya sanni ya tuno Ni,Yana Sona gashi har Ina ma gidansa a matsayin Matarsa.
Ina cikin wannan tunani naji ya murda Handle ya shugo da sallama tare da Ayman, suka zauna,Ina kallonsa ta gyalena shara shara yayi kyau kamar yau aka daura aure yasha farar shadda me shegen kyau da tsada sai kamshi yake,Ayman yace kun Dade Kuna Raina min hankali Ashe Matarsa ce ke,gaskiya Man kayi Mana wayau auren bazata,Addua Ayman yasa mukayi Baki daya ya Mana fatan Alkhairi karshe yace a kiyaye Amarya Kar dangin miji su gano inda kike,kaima Ango kafi kowa sani Tam yayi waje suna dariya,Aliyu Bai ce komai ba yabi bayansa ya rakashi ya tafi gida sannan yasa masu aiki suka rufe gidan Bayan ya gargadesu ko waye yazo karsu Bari ya Shiga gidan Nan indai ba Matarsa ba ko shine suka ba da Izni ba,sannan karsu sake suyi maganarsu a gaban ko waye,duk Wanda yayi sabanin gargadinsa a bakin aikinsa,suka ce sunji sun Amince.
Ina jinsa ya shigo ya ajiye min leda tare da cewa ga abinci Nan ya juya yayi tafiyarsa abinsa,Farin ciki ya kamani Naga alamar bazai ko kwana a dakina ba.
Murna yakeyi Haka yayi wanka tare da Shirin baccinsa ya kwanta saman lafiyayyen bed dinsa,bacci ya gagareshi yanda yake ta faman tunanina Yana tuna rayuwarmu ta farko,First night dinmu yake tariyowa Yana tunawa ya kasa bacci,Yana so yazo wajena Bai son kuma ya zubar da ajinsa ko na disgashi gwara yaja mutuncinsa, da kyar ya samu bacci ya daukeshi yayin da Ni Kuma nake ta bacci na cikin kwanciyar hankali.
Ina cikin bacci naji kamar Abu na Bina a jikina a firgice na farka tare da kunna light katon kadangare na gani,Ihu na Shiga kwalawa na Gaza Addua ma na fito da gudu shi Kuma yaji Ihu na ya fito a hanya mukayi karo na fada jikinsa tare da kankameshi, lfy Yana tambayata jikina na rawa nace kadangare ne Kato a dakina, tsaki yaja tare da furta ke dai matsoraciya kawai muje na gani,muna Shiga ba kadangare ba alamunsa,Tsoro kika ji ba wani kadangare kiyi Addua ki kwanta,Ni dai na tabbatar Naga kadangare Amma an duba ko Ina babu,Haka na daure gudun kar yace so nake na kwanta tare dashi Haka na daure na kwanta,da kansa ya rufa min bargo ya kashe min light ya tafi,bamu Fi 15mnt ba na kasa bacci a tsorace nake kawai Naga tattabaru guda uku sun taho fafafafa kaina sun Fado kasan bed faf,da gudu na fito Ina uban Ihu,ya fito shima da sauri na wuce shi da gudu Yana rikeni Ina kwacewa jikina na Bari Ina karkarwa,nace bazan iya Zama a gidan Nan ba wlh,Tattabaru ne yanzu Suna ta fada su uku,yace Tattabaru Kuma? Da sauri Ina haki nace ae har koto sukeyi,mene koto Kuma? ya tambaya,nace Kiss suke ta yi,dariya ta kamashi yace to ke kuma matsoraciya ba sai kiyi kallo ba,muje na maidake,kafada na make wlh bazan koma ba,gobe ma kwashe kayana zanyi na canja dakin kwana sai dai na dawo dakinka.
A gaba ya sani yace muje ki kwanta to a dakina,da sauri na bishi muka Shiga dakinsa nace to idan nayi kwana Biyar a saman bed kana kasa,sai kaima kayi kwana Biyar a bed Ni Kuma Ina kasa, Harara ya zuba min dake dakinki ne ko? Zaki min iko kika dameni ma komawa dakinki zakiyi,Shuru nayi ba tausayi ya haye gadonsa harda bajewa Dan karma na Samu wuri,a kasa nayi Shimfida ya bani pillow daya na kwanta a tsorace nake,light ya kashe na daura Hannuna a saman bed dinsa na riko yatsan kafarsa Babba,mene Haka?ya tambaya,tsoro nakeji wlh idan nayi Haka kuma to bazan ji tsoron ba, a Haka mukayi bacci har ban San sanda na saki yatsan kafarsa ba.
Cikin dare naji karatun Qurani me dadi Yana tashi,a hankali na bude idona mamaki ya kamani ganin Danbature Yana sallar dare, farin ciki ya kamani Ashe Haka yake da addini ga ilmi gaskiya nayi Saar miji, Godiya nayiwa Allah tare da Mikewa Nima nayi Alwala nayi Nafeela rakaa biyu da adduoi na kwanta,shi Kam Yana ta yin Sallolinsa,sai da ya Dade sannan ya Gama adduoinsa ya kwanta tare da bacci.
Washe gari da Asuba Naga har Yana rakaatanil fijr,a gurguje na tashi Nima nayi brush,Alwala sannan na tayar da sallah,Ina kallo ya tafi masallaci da sauri dake Bayan gidanmu, sai da gari yayi haske ya dawo,lokacin na Gama nawa na gyara dakin ya dauki kamshi na kwanta bacci ya kwashe Ni.
Shima Bai Bata lokaci ba ya kwanta bacci Mai nauyi yayi gaba dashi.