Sashe 10
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar bakin ciki a wajena,ranar da bazan manta da ita ba a rayuwata bamu farka ba sai da Rana ta fito ya fara farkawa a matukar gigice ganin mace kusa dashi a kwance,dakin da yake ciki ya kalla yace what....da karfi Wanda yayi sanadiyar farkawata a bacci,nace lfy Dan Baturena? Dake Haka nake ce Masa,wani yare naji Yana yi Wanda ban San wanne yare bane sai Kuma naji ya koma turanci, Who are u? Who the Hell are u?, ya shako wuyana ya fesa min mari,ga dakin mun kulle ko Ina duhu, sai Kuma naji yayi Hausa uban waye ke, wacce kazama ce ke da Zaki kwanta a jikina? Mum? Mum, where am i? Ya Kara shako Ni ya jijjigani da karfi a Ina nake Nan dakikiya? wani tsoronsa ya kamani da Alama ya warke nace a Dingawa kake kauyen Gombe state Nigeria, Kuma Ni matarkace kafin na rufe Baki ya zuba min Mari matata kazamarki nonsense kin San ko Ni waye? Karuwan banza Ni Aliyu Hydar oh..God fuck u ya kalli kayan jikinsa ya kalli dakin baya ganewa sabo da duhu,,nace ciwon hauka kayi na aureka Dan na taimaka maka wlh Ina sonka,karka min Haka karka gujeni,ka tsaya na baka labari a Mahaukaci kazo garin Nan,da farko ba sonka nakeyi ba tausayinka Dan na taimakeka yasa na aure ka,Babu wahalar da ban Sha ba akanka har sonka ya kamani hannunsa na ruko....
Maruka ya Kara zuba min har uku ya Sa kafa yayi ball Dani na nayi taka taka na bigi jikin bed ji kake gwaf,kaina ya fashe ,jini ya zubo ta hancina gashi mun rufe ko Ina duhu kamar dare bana ganinsa baya ganin fuskata ko kadan ya bude kofa kamar zai jijjigeta ya fice da sauri Yana kiran Dad da Mum tare da wasu mutanensa Kuma sai wani yare yakeyi Wanda ban San na wanne kasa bane.
Koda ya fita ba Ba mutane a garin kasancewar yanzu gari ya waye wani me machine ya tambaya ya kaishi cikin garin Gombe city,ya kaishi kuwa Yana sauka ya tare wani a hanya tare da tambayarsa Dan Allah ya ara Masa waya ya bashi ya Kira Mum dinsa Yana wani irin yare Wanda kamar na kasar waje ne, Nan take 30mnt sai ga Motocin sojoji sun zo Dalla Dalla guda biyu da gudu suka bude Masa mota ya Shiga tare da kamewa a Bayan mota Nan ya mikawa me machine dubu goma cash, me machine ya dinga ihu da tsalle abinda naira hamsin suke Kai mutane yau gashi da 10k, wannan motoci Basu tsaya ko Ina wani katafaren Hotel Yana ta masifa da turanci da Hausa ko yarensa,a hotel ya dinga wanka Yana darje jikinsa da Bakinsa yafi awa a toilet Yana kakale kakalensa dinsa ga masifa Yana ta yi da yarensa da Kuma turanci watarana Kuma yayi Hausa,Kaya na Alfarma kana Nan Kaya ya saka sun hadu kamar yanzu ya sauka daga London abin kallo ne ga waya har an siyo Masa iPhone tafkekiyar da sai wane da wane, takalminsa wow sai Wanda ya gani idan ba saninsa kayi ba baza ka gane Dan Bature ba sabo da ya gaji da haduwa, sai Airport ya shige jirgi sannan ya Kira Dad dinsa yace Dad London Zan wuce a duba lfy ta na huta sai na dawo Nigeria pls Dad,wata aljana ce ta sace ni can wani daji I'm 100% sured Aljanna ce Dad,Bayan sun Gama waya jirgi ya Lula sararin samaniya abinka da masu hannu da shuni kudi Kare magana idan da kudi yanzu zakayi komai a wuce wajen.
Fuskata ta kumbura sumtum,ga Baki ya fashe,ga hanci jini da kyar na lallaba na mike nayi wanka na Dan gyara kaina,Ina rusa kuka Hawaye ya gagara tsayawa,takaicina ba dukan ba kawai sonsa da ya rigada ya dagargaza min zuciya,bazan iya rayuwa Babu Dan Bature ba,gashi abin haushin sanda yake da hankalin Bai ga kalata ba Bai San fuskata ba bare ya ganeni watarana, sallah kawai nayi na kaiwa Allah kukana tare da karatun Qurani, Yini nayi Ina kuka a daki nayi tunanin komawa gida na tuna furuncin Abbu Kar na soma zuwa inda yake da matsala akan aurena.
Me machine kuwa tunda ya dawo ya baza labarin a kauye Yana fada Dan Bature ya warke ya bar garin Nan Ashe Hamshakin me kudine zance har yaje gidanmu,Ya Salman yazo ya buga min kofa.
Idona a kumbure jajir nazo na bude kofa da sauri tunanina Mijina na ne da sauri na bude cike da farin ciki baya laifi a wajena,Ni Akan Ya warke ya rabu Dani gwara ya zauna da cutar haukarsa mu dawwama tare ,Ina ganin Ya Salman ne na rushe da kuka tare da fadawa jikinsa, tausayina ya rufe shi tabbas abinda yaji a gari gaskiya ne, Kuma abinda ake gudu shi ya faru,cikin gidan ya Jani tare da zaunar Dani gefensa, ya rasa ma ta Ina zai fara,ina kuka na bashi labarin abinda ya faru kaf ya tausaya min,Ya Salman yace hope dai kwanciyar aure Bata hadaku ba, Ina Hawaye nace sau daya ne Yaya Kuma jiya ne a Daren da yayi bacci ya warke ya dawo hankalinsa.
Yaya Wlh Ina sonsa na Shiga uku ya zanyi da rayuwata wlh Ina sonsa Don Allah Yaya nasan kana Sona ka Nemo min shi idan ban ganshi ba mutuwa zanyi, kafafun Ya Salman na rike na dira gwiwoyina a kasa Ina gunjin kuka Ina rokonsa,Nasiha ya Shiga yi min Amma Sam bana jinta burina kawai Naga Danbature na ya dawo gareni,kafin kace me zance ya baza gari mutane suka dinga turuwar zuwa gidan da nake Ana min jaje wasu suna Allah ya Kara dama ai an fada Mata taki ji, wasu Kuma sun tausaya min ganin halin da nake ciki kamar mahaukaciya na koma.Anty Amarya da tazo shewa tayi tare da shekewa da dariya tace Rana dubu ta barawo Rana daya Tak tame Kaya,yarinyar har Kara kika Kai ubanki mahaifinki wajen Yan Hisba Akan ya zaba Miki miji ke so ya rufe Miki Ido, yau wa gari ya waya? Shuru nayi ta Gama ta tafi tana dariya.
Hajiyarmu itama kuka take na tausayin yarta ga Abbu ya tabbatar Kar na doso gidansa shima yaji labari,Anty Amarya sai Murna take tana Kara yayatawa a gari, Haka Matan su Kawu Salisu da yaransu Mata Banda Mahmood sai gulmata sukeyi Ana Allah ya Kara.
Talle me lemo labarin na zuwa Masa ya raba lemonsa kaf kyauta sabo da murna Yana Allah Kara yanzu sai kuma Nan gaba a hakura a dawo a aureni Dole uwar naki.
Bayan kwana biyu Ni kadai nake kwana a gidan Ina Addua da kuka Ya Salman,Musa da Mahmood kullum a gidana suke yini anan muke cin abinci tare suna debe min kewa suna min Nasiha da tayani Addua,duk na rame nayi duhu kamar ba Ni ba.
Bani da aiki sai tunanin Mijina Wanda kullum kayan sawarsa da ya Bari nake Shimfidawa Ina kwanciya a Kai,Haka kuma na dinga gasa kaina har na warke sumul, Ya Salman da Whot card suke zuwa mu yini muna buga game suna ebe min kewa.
Yauma muna yin game din ban San sanda na koma tunanin Baturena ba yanda mukayi rayuwa tare nake matukar kaunarsa kuka na fara Wanda ban San na fara ba sai sheshekar kukana suka ji Wanda sun rigada sun Saba da hakan, Ya Mahmood yace Sister mene haka Kuma again? Katin Yana Hannuna na jikesu da Hawaye na daga kaina sama Ina kuka nace Ina sonsa ya zanyi Ina kaunarsa na Kara rushewa da kuka duk suka tsaya suna saurarena cike da tausayi sukayi jumgum jumgum.
Ya Mahmood ne ya katse shurun yace ya kamata kawai muje mu roki Abbu ta koma gaban Hajiyarmu sabo da zatafi samun nutsuwa,sannan tunda result dinta ya fito Kuma sunyi kyau sai mu kaita ko college ne tayi karatu ko ta rage tension.
A hankali Ina share hawayena nace bazan iya karatu ba a halin da nake ciki bazan iya komai ba face sallah da Addua Allah ya hadani da Mijina karku Bata kudinku.
To Amma ai Zaki koma gida kici gaba da Zama ko? Ae idan Abbu ya yarda ba.
Bayan kwana biyu Suka roki Abbu da kyar ya hakura na dawo gida shima saida manyan gari da su Kawu suka Sa Baki sannan ya yarda na tattaro kayana na kulle gidan mukaje har gidan me gari na bashi key mukayi Masa godiyar aron gida da ya bamu kyauta.
Bayan na dawo Gaban iyayena Babu abinda suka sassauta a gareni yanda suke min da Haka ma yanzu,ga tunanin Mijina,na rame na fige nayi duhu kamar ba Ni ba, Bayan na kwashe wata uku a gida jahilcin mutan kauye suka fara maganganu ya kamata na manta da auren dake kaina nayi aure Nan gaba dama ba a sani ba ko ba sunansa Aliyu ba kawai aka daura akayi Masa waliyai.
Bana fita ko Ina kullum Ina gida Ina kiyaye igiyoyin aurena na tabbatar sunansa Aliyu kenan tunda naji ya fada da kansa Bayan ya dawo hayyacinsa,kullum burina na zauna ko na kwanta nayi ta tunano rayuwata tare da mijina watarana nayi dariya watarana kuka, nayi tunanin saduwata dashi daya Zan samu cikinsa da nayi murna Amma Ya Salman ya kaini har asibiti Babu ciki a tare dani banji dadi ba naso zanga Dana jinin abin kaunata Danbature.