← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 50

Sashe 24

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameen nace na Ina goge kwalla ta a boye Kar ya gane,tausayin kaina nakeji Bai gane komai ba,na rufe gidan muka tafi zamu Fara gaida me gari,Mutanen gari Majalisa majailisa kowa har Yara Ana ta tayani murnan ganin Danbature ya warke,ko Ina Zaka ji Yara Suna kwalawa Aliyu Kira Danbature... Danbature sai binmu sukeyi,manyan Kuma hannu kawai suke bashi suna gaisawa Ana Masa murnar warkewa, shi dai kallonsu yake a mahaukata Yana biye musu da Faraa kamar ya sansu ana gaisawa,Ni kuwa murna nake ya rufa min asiri banji kunya ba,duk inda muka je kawai kudi yake rabawa Yara da manya ba ji ba gani,wasu Kuma ya zuba min a jakata yace ungo kina bawa wasu.

Ta wajen Talle me Lemo muka bi Yana ganinmu ya mike tsaye yace jar uba Ashe da gaske ne me kudi ne Kuma ya warke,Kaga Danbature wlh da gaske ikon Allah,Dariya Danbature yayi Bai mikawa Talle hannu ba Talle ya fito daga rumfarsa sai gani mukayi ya cafki Hannun Dan Bature yayi gaisawar Dole dashi,Yana yashe Baki yaki sakin hannun Yana girgiza hannun Danbature Yana jero gaisuwa muna lfy,ya gida,ya aiki,ya birni,ya mutan birni,ya aiki,manyan naka kalau,Kuna lfy kun samemu lfy, Danbature yace lfy ya gaji da amsawa gashi yaki sakin hannunsa,gashi tafin hannun Talle duk kaushi,da kyar Ice ya janye hannunsa ta karfi,Talle yace oh hannu kamar adduga haka Kuna Jin dadinku,kudi ya bashi da Dan yawa, Talle sai Godiya yake harda cewa Lallai Dole ka kasa ni a wajenta. Lemo ya zuba a Leda da yawan gaske yace za a Aiko muku dashi gida,nace ka barshi baza mu cinye maka jari ba.

Gidan me gari muka je,Me gari ya dinga mamaki da murna,nace shine ya bamu gidan da muka zauna,Nan Danbature ya dinga zuba Godiya kamar gaske ya bawa me gari Dubu Dari kyauta.Me gari kamar zai haukace sabo da murna.
Bayan Nan Munje wajen Wanda ya bamu kayan abinci,Wanda yayi min kayan daki sosai ya musu kyauta ta ban girma,sai Addua da murna suke Mana,Ya Mahamood na nuna Masa nace shi ya biya Sadaki,shima Dubu dari biyu ya bashi,sannan yace ya bashi takardunsa zai canja Masa wajen aiki a Gombe,Haka nace Ya Salman farko aure shi ya dinga kawo abinci lokacin da iyayena suka gujeni,Shima ya bashi nasa,Ya Musa Haka,sannan duk ya karbi takardunsu, harda wasu kannen ya Mahmood yaran Kawu Usman da kawu Salisu mutum shida ya karbi takardunsa da suka Gama degree yace aiki a Gombe city inshallah, Kawu Salisu ma sunsha kyauta,matansu gulma ta koma ciki,Haka Kakanninmu,danginmu kaf sunci arzikin Danbature harda mutanen gari.
Ni tsoro ma naji irin kudin daya kashe ya wuce tunanin me tunani,ko na hanashi sai yace ba ruwana.sai dare muka dawo gida.

Ya Salman ya shirya Mana liyafa Gasashiyar kaza,Yan Shila,lemuka,fresh yo,ga chips hadadde.
Saman katifar ya kwanta Yana huce gajiya Bayan yayi sallar Isha a masallaci tare dasu Ya Salman har Hira suka danyi ba laifi.

Ina wajen Hajiyarmu muna ta Hira ta uwa da yarta, shi kuwa tuni yaci duk abinda Ya Salman ya kawo,ya kwanta Yana Hutawa sannan ya fita waje inda Suke taruwa ya zauna cikinsu Ana Hira jefi jefi yake Sa Baki,Bayan ya gaji 10pm kowa yana gida,ba yanda Ya Musa Basu yi dashi ba kan ya Shiga toilet dinsu yayi wanka yace bazai yi ba,Wai kunya yake ji gidan surukansa ne,dariya sukayi sun zata gaske yake yi,Ni kuwa nasan kawai fada yayi.

Da dare nayi Shirin bacci dakin Hajiyarmu tace in Banda haukarki Fadila ai wajen mijinki zakije ki Taya shi kwana,shi kadai a daki ba kowa ai bazai ji Dadi ba,ga su Ya Salman Suma ba dashi zasu kwana ba, nace kyaleshi Ni a Nan Zan kwana,Hajiyarmu ta dinga masifa ta koreni Dole nasa hijab na tafi dakin Anty itama tace can Zan tafi ta koreni da gorinta iri iri.
Na Dade a tsakar gida to ya zanyi Ni Kam,Zama nayi a tsakar gidan kawai sai ga Aliyu ya fito ya gaji shi kadai kamar maye, a waje ya ganni yace an koroki ko? Ke karamar kwakwalwa gareki kamar Baki sanni ba ai da sai ki zo ki fada min sai ayi wata dabarar, taso mu tafi,Mikewa nayi nabi bayansa yace muje zamu je yawo sai mu rage dare a waje can wurin 12am mu dawo sai ki kwana a zaune a kasa,ni Kuma Ina saman katifata tunda ke kika Jaja min masifa Allah ya gani kina matar wani Zaki sa Allah ya konani.

Haka muka je can waje ga sanyi anayi muna zaune kowa yayi Shuru shi waya kawai yake latsawa.
Mun Dade nace zaman Nan bashi da amfani kawai mu koma gida,muna komawa gida kowa ya kulle kofarsa Shuru gidan,hanyar dakin Hajiyarmu na bi yace bakya Jin magana ke ko?na dawo na bi bayansa Yana zuwa ya fada saman katifa ya kwanta.
Nima na kwanta can karshen dakin a kasa saman carpet.
Tunawa nayi da rayuwarmu ta baya yanda Muke kwana Shimfida daya,da Romancing dinmu na wani Feeling nake ji,Shaawarsa ta darsu a Raina sai mutsu mutsu nakeyi na kasa bacci na tsurawa bayansa Ido ji nake kamar na kwanta a bayansa na rungumeshi,a Raina nace Kuma ace ba Kaya a jikinmu Wai da naji Dadi,tsaki naja kadan na Kara juyawa baya,shi Kuma ya juyo ya tsurawa bayana ido,Yana tunani yanda ake cewa Ni Matarsa ce,duk da Hijab din dake jikina Bai Hana shape dina fitowa ba Nan ya Kare min kallo,ji yake kamar ya sanni tin da,Kuma ma me yasa idan Ana cewa Mijina nane yake Jin wani farin ciki da nishadi, Wani birgeshi yaji nayi,tunani yayi matar aure ce yayi sauri ya sake juya baya can.

Can dai yaji tunanina yaki barin zuciyarsa sannan ga wani Abu dake Masa yawo a zuciya abin yayi Masa yawa,can abinsa ya ciyoshi a hankali ba tare da ya juyo ba yace kika Ce Ni mijinki ne dai ko? Ina jinsa na juyo Ina kallon bayansa nace ae Mana da can ba Amma yanzu na gano Ni ba matarka bace, ba Kai bane Sam,yanzu na gane Kuna da banbanci,Haushi yaji sosai yace to me yasa Yan garinku kowa ya sanni,Kuma ma ai ke kika fada da kanki Yar rainin hankali makaryaciyace Dame ke tuntuni?

Nace ae ai dama Ni watarana nakan tsokani mutum na Shimfida masa karyata,yace to karya kike to nine Nan tunda kowa ya tabbatar nine kawai dai ban San me yasa ban tuna komai ba,Amma na fara ji ajiki na nine,Hmm ai nace na gano fa ba Kai bane,takaici ya kamashi yace to a nemoshi ya sakeki tunda baida mutunci.
Nace Nima abinda nake so kenan da Zan ganshi ya sawwake min kawai ko na Samu na auri wani,idan ya sakeki wa zai aureki nufinki? Nace samari ne Dani fa a schl fa da yawa.
Tsaki yaja kawai yayi Shuru abinsa Yana faman tunani shine ko dai ba shine ba har bacci ya dauke mu.

Mum Ice Bata San Ina Dan nata ya tafi ba ta Gama bincike ance Yana Abuja,bakin ciki kamar ya kasheta yanzu ya zatayi ga allurar zata yi expired gobe idan har ba ayi Masa aikinta ya rushe.ta gigice ga wayoyinsa basa tafiya.
Ni kuwa murna nakeyi Dole sai Bayan 3days zamu dawo lokacin Maganin Allura baida Amfani.

Washe gari da Asuba ya farka ya fita ba tare da na sani ba yaje masallaci tare dasu Abbu sai ladan yace liman baida lfy sai yau Abbu ya jasu sallah dama watarana shi ke jan sallar idan Liman bai samu damar zuwa ba,Aliyu yace Bari yaja sallar kawai,yau kowa yaji sabuwar Qiria na tashi a speaker kamar Shureim na Saudiya, Ni kaina karatun ne ya tasheni na rasa Muryar waye aka samu Haka kwaro a iya karatun Qurani,su Hajiyarmu ma da mutanen garin Ana ta tunanin waye wannan Haka sai Wanda suka je masallacin su suka tabbatar wa mutane cewar Danbature ne Mijin Fadila,lokacin Ina dakin Hajiyarmu ya Salman suka bamu labari Mijin Fadila ne yaja sallah yau,na dinga mamaki dama Ashe da ilminsa Lallai.
Bayan ya dawo ya samu bana dakin yayi kwanciyarsa yaci gaba da baccinsa Bai tashi ba sai 11am, Brush yayi ya wanke fuskarsa da sabulu a jikin fanfom gidanmu kamar wani mace,shi dai bazai Shiga toilet ba,muna kallonsa ya Gama,lokacin aka kawo Masa tea,doya da kwai da egg into egg,baisha tea ba kawai doyar yaci da kwai yasha ruwa faro ya Gama komai, Ni kuwa ban sake bi takansa ba suna tare dasu Ya Salman abinsu,nayi wankana na shirya tsab komai nayi naci kwalliya sosai kyau dai nayi matuka,atamfa nasa Light blue Riga da skert ya kamani cif Ni,lokacin 12pm ya Kira Driver dinsa Wanda suka kawomu jiya sun dawo daukanmu, nace zamu tafi Amma Zan dawo Ni kadai,Hajiyarmu tace yaushe zamu zo aga gidan naku na Lagos,gabana ya Fadi na kirkiro karya nace ai iyayensa har yanzu Basu San da auren ba,da kyar idan zasu yarda sai dai a Taya mu da Addua Amma har yau Ina a matsayin Yar aiki a gidan daga Ni sai shi muka sani.

Hajiyarmu da Abbu sukace Allah ya kyauta,Anty kuwa sai cewa tayi Allah kiyaye Kar su sa ya sakoki cab kice aikin banza ne Ashe kina ruwa.
Shuru na Mata ya fito yace muje,nace Zamu tafi har Mota suka rakamu Bayan Danbature ya musu bulala da kudade.
Da gudu matakan tsaro daya ya bude min kofa na Shiga daya Kuma ya bude wa Danbature ta daya side din ya Shiga muka musu sallama Ina daga musu hannu muka bar garin,sai da Naga mun bar kauye naja ajiyar zuciya Ina godewa Allah da Danbature da ya taimakeni ya rufa min asiri na tsira da mutuncina.
Tunda muke a mota yake ta faman kallona nayi kyau da yawa,Abubuwa da yawa yake tunani a kaina,Ina kallonsa ta gefen Ido na.

yau kwanakin allurar Anty Maryam hudu lokacin yinta ya wuce tuni,tana ta faman Jin haushi ta gama Tara masifarta sai Danta ya dawo Aliyu zata ci ubansa zaiyi tafiya ya kasa sanar Mata tana uwarsa wacce ta haifeshi sai wajen Asiya zata ji labarin Yana Abuja,Bata San Abujan ma karyace daga Ni sai shi muka San inda muke.
Chapter 24 · 0% Book details