← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 50

Sashe 39

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gurguje ya tashi wayarsa na ruri muna dubawa muka ga Sunan Mum ne ke yawo a screen din,Sai ga Kiran Nanee ma suna goslow, har zai daga nayi sauri na rike Masa hannu a nutse nace karka daga tashi muje ka shirya kaje gida ko wani abun ya faru,idan ka daga Mum zata iya tracking location namu,a gurguje na jashi toilet tare mukayi wanka da sallar Isha sannan ya maida kayansa da yazo dasu gudun kar ya canja Mum tace bada su ya fita ba,Har mota na rakashi Ina Masa Addua Yana kissing dina mun Dade a Haka kafin na lallabashi ya Shiga mota ya tafi,lokacin na dawo cikin Palo sannan na Kira Binto tazo tayani Zama.

Danbaturena kuwa sai da ya kusa da gidansu sannan ya tsaya tare da Kiran Mum tana dagawa yaji ruwan balai kazo Ina nemanka,hankalinsa ya tashi tunaninsa Mum ta gane inda muke zaune,Nanee ya Kira tana dagawa yaji tana ta faman kuka tana Aliyu kazo akwai matsala a gidan nan, gani Nan kawai ya iya furtawa ya datse Kiran tare da kunna hancin motarsa cikin gidansu da sauri.

Saddiqa ya iske tana ta faman zirga zirga a tsakar gidan tana tamke bakinta tana Kai kawo,tana Ganin Aliyu ta Karasa wajensa da sauri tace Sauri kake? akwai matsala ta furta tare da fashewa da Kuka, da sauri yace lafiya ke Kuma? Saddiqa ta sake fashewa da Kuka,cikin Aliyu ya duri ruwa,hantarsa ta kada yayi zaton mutuwa akayi a gidan, da karaji yace mene ki fada min meke faruwa? Saddiqa tana shesheka tace Shehu Niga ne ya kwace min Naira Hamsin dina Kuma gobe Zan siyi Aya me sugar da ita,wani bakin ciki Aliyu yaji,tsaki yaja ya wuce abinsa ya zata Maganar kirki zata yi Wai Aya me sugar.

Shehu Niga ne shima ya shararo da gudu Yana a taimakemu jama'a, kan Aliyu ya kulle,kwakwalwarsa ta juya to ta Ina zai Fara,,ga Mum,Asiya Kuma na kuka,Shawara ya yanke kawai ya fara zuwa sashen Daddy yaga meke faruwa Don yafi zargin ko abin ya Hado da Daddy nasu tunda yaji Nanee na kuka.

HADIN KAI FANS Kuna birgeni Ina sonku.

AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

76-80

Official

By
AsmaBaffa

Amatullah,Agas,Aisha Zubairu,Maimuna,Aysha Ad, Ummu Haneefer,Bibaabdulhamidnuhu & Zeemama. Ina Godiya da Sharhi page dinku ne.

Fans afwa kwana biyu bana replying Sharhi naku Ina busy ne karku gaji akwai Kuma Wanda nasu yasa waiting ban gani ba,Kar kuga nayiwa wasu ku banyi ba bangani bane ayi min afwa.

Part din Daddy ya Isa da sauri tun kafin ya Shiga yaji Hayaniyar Karimatu tana mun Shiga uku ta kashe Mana miji,yasan Daddy ake nufi ,Yana karasawa yaga Wuka a hannu Mum dinsa da jini a jikinta,Asiya na jikin gawar Daddy tana Rusa kuka,Karimatu ihu da balai take faman yi Yayin da wacce ta aikata aikin Mum tana rike da wuka a hannunta tana karkarwa jikinta yayi sanyi ta kasa motsi.
A wajen Aliyu ya durkushe tare da fashewa da Kuka ganin Daddy kwance cikin jini,Mum kuwa rantse rantse ta fara yi ba ita ta kashe Daddy ba,Son wlh ku yarda Dani wallahi bani na kashe shi ba,wlh shugowa nayi na tadda Wuka a kasa Daddy kuma a kwance shine na dauki wukar sai ga Asiya ta fito daga Toilet din Daddy,Bayan Nan Karimatu ta fito Allah ne shedata wallahi bani bace.
A matukar fusace Ahleef yace kece Mum dama kin ce sai kin kashe Daddy sabo da Neman duniya,Wallahi ko me Zaki ce bazan yarda ba kuma kamar yanda kika yiwa Daddy indai Ina Raye sai an bi hakkin Daddy an yanke Miki hukunci dai dai da abinda kika aikata.

Alhmdllh Aliyu ta cucemu wlh gwara mu talauce mu zauna da mijinmu Akan ya mutu gashi kinyi Mana aiki yiiiiiii Karimatu ta fashe da kuka,Asiya Kuma tana kan Daddy Tana Rusa Kuka, kafin kace me gida ya cika dam,Yan jarida,makwafta,Yan uwa,kowa ya sheda Mum itace ta kashe Daddy da hannunta,Yan jarida,Yan Sanda sun yiwa gidan tsinke,Asibiti aka tafi da Daddy, Likitoci suka rufar masa,Anyi gwaje gwajensu an gano Daddy Bai rasu ba,Nan aka samu manyan Likitoci suka Masa aiki me kyau,kowa zuciyarsa Babu dadi sabo da Daddy Yana tsakanin rayuwa da mutuwa,Likitoci sun tabbatar bazai tashi yanzu ba,Kuma ko yaushe zai iya mutuwa idan ba wani ikon Allah ba,wukar da Mum ta Burma Masa ta Shiga da yawa, Mum Kuma tuni Police sun tasa keyarta an kulleta kafin ayi bincike,Dr who da yaran gida kowa har su Shekara dake kauye kuka sukeyi ba ji ba gani,Daddy da yake komai nasu,Babban jigo,Mai tallafa musu zai tafi ya barsu,Hajjo kuwa Hawaye baya karewa Hawan jininta ya tashi itama tana Asibiti kwance Ana Bata kulawa ta sankame, Asiya itace karfin jinyar Daddy.

Ni kuwa ban San me ya faru ba,Naga dai Aliyu ko waya Bai kirani ba,na gwada kiransa a kashe wayoyinsa,Hankalina ya tashi,washe gari 5pm Ina faman jiransa yazo Gidana na Gama tsara kwalliyata na hadu karshe Amma Shuru Bai zo ba,Hankalina ya Kara tashi,Ina zaune Amma hankali na baya jikina ko kadan.
Ina tunaninsa naji Karar motarsa,farin ciki ya kamani Amma nace bazan nuna ba sai na nuna Masa ya Bata min Rai, Door bell naji na mike a nutse kafin nayi motsi naji mutum gwaraf ya Fado jikina,Ido muka hada Hawaye male male a fuskar Danbature Hankalina yayi mummunar faduwa da sauri nace lfy? Me ya faru,Mum ce tace ka sakeni? A wajen ya durkushe yaci gaba da kukansa Yana fada min Daddy,Mum ta kashe Daddy Fadila yau,Salati na saki nace da me? Wuka ya furta, kaina ya daure na Kara tsanar Mum.

Innalillahi wa inna ilayhirrajun Nima na zauna a wajen kawai,a hankali Yana goge hawayensa yace Bai mutu ba Amma likitoci sunce ba Lallai ya rayu ba,Ina Mum din to? Na tambaya, police sun tafi da ita zasuyi bincike a kanta ya bani amsa.
Taimaka Masa nayi ya mike tsaye na jashi Bedroom dinmu sannan na kwantar dashi saman bed ya Dan huta Ni Kuma na shiga kitchen,abincin Dana shirya Mana na kwaso na kawo Bedroom sannan na jashi toilet, da kaina nayi Masa wanka na shiryashi muka fito tare da gabatar da Sallar Magrib da isha muka yiwa Daddy Addua sosai,kafin Nan na zauna a saman bed Zan bashi abinci yace ya koshi,bazan iya cin komai ba Fadila zuciyata tana wajen Daddy, bana so Daddy ya rasu ba tare da ya yafewa mahaifiyata ba abinda take Masa na fili Dana boye,bana son Mum ta mutu ta wuce wuta a lahira,tausayi ya bani na kwantar dashi saman cinyata tare da karo Karfin ac, a hankali Ina shafa Masa sumarsa zuwa wuyansa da,Ina shafa hancinsa da girarsa me gashi cike da sanyayyar murya nace ka kwantar da hankalinka Danbaturena inshallah Daddy zai warke bazai mutu ba,kuma Mum zata shiryu har Daddy ya yafe Mata ma,damuwa Babu abinda zata maka,kawai Addua zamu dage da yi Masa kayi hakuri muci abincin Nan ko kadan ne Amma idan ka kwanta baka ci komai ba,Kuma nasan rabonka da abinci tun jiya da ka bar gidan Nan.

Lallashinsa na dinga yi kamar Zan yi kuka sannan na samu ya karbi abincin Ina bashi Yana ci Nima Ina ci,kadan yaci yace ya koshi,sabo da Nima Ina damuwa ban iya cin na kirki ba,na kaiwa Masu aiki nace su cinye shi.
Yana kwance a jikina Ina kwantar Masa da hankali har Allah ya taimakeni yayi bacci sannan na gyara Masa kwanciya naje nayi wanka da Shirin bacci Nima na kwanta gefensa bacci yayi gaba Dani,cikin dare ya farka tare da Zama kawai a saman bed Yana ta aikin tunani da hawaye, Yana Haka na farka na ganshi,da sauri na tashi tare da furta haba Honey kamar baka San kaddara ba,da tunanin da kakeyi kana Bata time tashi muyi Alwala kawai mu Kai kukanmu wajen Allah, Dole nayi Haka Baby Baki San me nake ji bane,na sani Mana tashi Ni dai muyi Nafeela kawai bazan jure ganinka cikin wannan halin ba,Bai min musu ba mukayi Alwala tare da Fara Nafilfili,mun Dade sosai kafin muka kwanta bacci yayi gaba damu,bamu farka ba sai da Asuba,muna sallah yace shi asibiti zai tafi ya gano jikin Daddy Kar ko ya mutu Bai sani ba.

Yanzu da Asuba zaka tafi? Karfa ka manta idan mutuwa ce baza ka iya hanawa ba ko kaje ko baka je ba Dan Allah ka kwanta ka samu bacci ko kadan ne jiya fa kusan bakayi bacci ba kwana kayi kana bugawa Dr who waya ya jikin Daddy.
Da kyar na lallabashi muka kwanta bacci ya dauke mu me karfi, bamu farka ba sai 10am, a gurguje naje na shirya Karin safe shi kuma Yana wanka,Bayan na Gama shi Kuma ya shirya cikin jallabiya me tsada fara yayi mugun kyau, ko turare Bai sa ba duk son turarensa,da kaina na fesa Masa sannan na kaishi Dining ya zauna nayi serving Nasa nace yi hakuri kaci Bari na shirya tunda an kama Mum sai na bika Hospital Amma ka ajiyeni a bakin gate Bayan ka Shiga Nima Zan Shiga kawai zance a radio naji labarin nazo dubiya.

Murmushi yayi Wanda tun shekaran jiya ban ga Murmushinsa ba,Dadi naji na wuce nayi wanka na shirya cikin lace me Masifar kyau da tsada,ban daura dankwali ba kawai gyale na yafa na zari Handbag dina sannan na dauko basket din Dana shirya abinci iri iri Wanda ya Dace aci da safe Zan Kai asibiti.
Yayi mamaki Kuma yaji Dadi na Kara birgeshi,Sona yaji ya Kara shigarsa yanda nake damuwa da damuwarsa data iyayensa tare da duk Wanda ya shafeshi.

Hannuna ya jawo na dawo ya zaunar Dani saman cinyarsa tare da kissing din Wuyana ya furta yar Balarabiya ta Baki ci komai ba,nace Ni kaina banjin yunwa Dan Baturena baya cikin Jin Dadi,fuska ya Kwabe kamar zaiyi kuka da Shagwaba shima yace gaskiya sai kinci abinci daga Hospital schl fa Zaki wuce, Hawaye ne ya Dan zubo min nace Allah hankalina ya tashi yanda kake damuwa gashi Ina tunano Daddy Yana bani tausayi.
Chapter 39 · 0% Book details