Sashe 27
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana yin sallama ko Addua baiyi ba ya juyo yace to wace ta tambayeni sunana na gaskiya kika sa nayi ta tunani iri iri har sai da na tuno sunana na fada Miki sannan da Daddy, lokacin ban San me kike nufi ba Amma yanzu na tuna an daura Mana,har na koma jikin bishiya nayi bacci Ana daura auren kin tuna?.
Kuma sannan na tuna sanda za a kaiki gidan miji a matsayin Amaryata ban sani ba na bi bayanki cikin Yan Kai Amarya,abinda yanzu na gagara tunawa munyi kwanciyar aure ko bamuyi ba Dan Allah ki tuna min kece Nan.
Fuska na hade sosai Amma a Raina murnar da nake baza ta misaltu ba, bafa Ni bace Malam ka gane ba Kaine Mijina ba. Yawwa Ina agogona da Zobe na? Nawa ne Nan Agogon Daddy ne ya siya min shi,ring Kuma na Mum dina nane Ina matukar sonsu,ki bani abina.
Ni ban San wani kayanka a hannuna ba na fada ma Kai ba Mijina bane ban Sanka ba sam,hararata yayi kawai yayi Shuru Nima na kyaleshi,na kwanta saman bed Dina name jinya.
Saida Doctor yazo duba shi kawai sai yace Wannan Yar jinyar Bata aikin komai ayi Mata fada Bata kula dani,yanzu ma shi yayi komai da kansa.
Cikin harshen turanci Doctor ya juyo kaina masifa yake kamar zai Ari bakin wani.
An baka abinci? Ice yace tun jiya taki bani abinci yunwa zata karasani, Da kansa Doctor ya Kira Johanna ta kawo abinci lafiyayyu ta ajiye, Takurawa Doctor yayi yace na bashi a Baki,
Ina turo Baki na mike Ina cika Ina batsewa, Lazy girl Doctor ya furta Yana barin room din.
Abincin na dauka na zauna gefen Bed din nasa,shi Kuma Yana saman bed din a zaune ya Kara wani narkewa,zan Fara bashi abincin yace a samin pillow a tallafemin baya na,dariya saura kadan ta kwace min na daure ta,yanda yayi Maganar kamar yaron yaye.
Pillow na jawo na sa Masa a Bayan,ya jingina ya kwanta,abincin na Shiga bashi Yana ci kuwa Yana Kare min kallo,akwai abubuwan da har yanzu Bai Gama tunawa ba lokacin da yayi Ciwon tunani yake yawan yi Dole shi sai ya tuna.
Kansa ya dafe Yana faman tunani,idonsa har ja yake sabo da daukan zafin da kansa yakeyi idan zai tuna Abu,tausayi ya bani sosai nace ka daina takurawa kanka da tunani Ni ba nice wacce aka daura ma aure da ita ba.
Bai kulani ba Yana ta sheka tunaninsa,Hawaye ne suka biyo ta idonsa tare da gangarowa zuwa kumatunsa,tausayi ya bani sosai kun San so da kauna bazan iya jure kallonsa haka ba duk da ban San me ya tuna ba again.
Ya Dade kafin ya saita kansa ya dawo normal,a hankali nace me ka tuna? Yace Mum ta ce zata kashe Daddy sabo da taci gadonsa,lokacin da take shirya abin naji ta shine tasa akayi min Allurar da hankalina zai Bata,har ga Allah Bata yi Don na haukace na bar gida ba,Amma Ni kaina ban San yaushe na fito nazo Gombe ba har nazo kauyenku ban sani ba.
Ni kuwa nasan tsafin da Anty ta masane ya daukeshi ya jefoshi Gombe,
Katse min tunanina yayi da idan har ban dauki mataki ba to Mum tabbas ta kusa kashe Daddy.
Yanzu dukiyar Daddy kaf da takardun komai nasa ya damkawa Mum su, sabo gani yake so take Masa na tsakani da Allah, sannan tana bin wasu mazan Yara kana na tana biyansu kudi,tasan nasan komai shi yasa take kokarin Hana ni lafiyar da Zan tona asirinta,nasan dama Ni ba wani so na take da yawa ba,tafi son Meenal sai Dr who.
Bayan na warke na bar garinku na sanar Mata zanje a duba lafiyata a London shine ta hada Baki da Doctor aka yi min wata Allura daga Nan na sake manta komai Bayan warkewa ta daga kauyenku, Akan Ina fada Mata gaskiya ta tsaneni.
Hawaye nakeyi sosai Jin irin tuggun Anty Maryam Akan dukiya tana cutar da danta gashi zata kashe Danta Akan aikin banza,Ashe ban sani ba har mijinta munanan halayenta Sunyi yawa,Nima Haka na kwashe abinda naji na tsafin da zata yi Masa na bashi labari,na fada Masa kudirin Karimatu ma,sannan na sanar Masa Dalilin da yasa na matsa Masa ya kaini garinmu Dan na kubutar dashi Kar ayi Masa wannan Allura.
Murmushi Naga ya fara yi Yana wani Jin Dadi yace to Zaki ce Kuma bakya so na ba nine mijinki ba? Fuska na hade nace to ai ba karya na fada ba kawai taimakonka nayi,to me yasa Dana farfado naga hanunki cikin nawa?
Banza na Masa.
Mazewa yayi yace to danzo ki gyara Nan,banyi tunanin komai ba naje kawai naji ya fisgoni jikinsa na fada, da sauri na mike na Bata Rai ina harararsa, Hannuna ya riko na fara kokarin kwacewa kokawa muka fara tsakaninmu kici kici,da hannunsa daya me lafiya yake ta wujijjigani Yana bani wahala,da kyar na kwaci kaina,kallona yayi yace Baki ma da karfi,banza nayi dashi,Bai hakura ba yace Johanna zata rakaki shopping da ganin gari Ina warkewa gida zamu tafi na sanarwa da kowa Ina da aure,nace akwai matsala karka fada ka Bari sai Nan gaba, Ashe kin yarda nine Mijin naki? Nace ko kadan Allah ya kiyaye min Zama matar mugu.
Murmushi yayi kawai yace kwana Nan Zan mallake Miki zuciya, dariya nayi a Raina tun yaushe ya Gama Mallake min zuciyar, yace ke na gane ki Mahaukaci Aliyu kike so na da can,ba Ni Aliyu lafiyayye na yanzu ba ko? Murmushi na saki nace Danbature nake so ni ba Kai ba gwara da ka gano gaskiya da kanka ka daina kulani yafiye maka alkhairi.
Mun kwashe sati biyu a Hospital kullum takura min yakeyi Dole nice Matarsa,Ni kuma naki karbar Zancen Dole ya gaji ya kyaleni.
Anty Maryam tun tana neman Ice har ta hakura kawai tana jira ta ganshi idan ya dawo, Kuma ta tabbatar muna tare da danta tunda Nima ban dawo ta ganni ba.
Sai Bayan Sallah ba time .
AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕
46-50
Official
By
AsmaBaffa
Happy Sallah Fans Allah nuna Mana ta Gaba da Rai da lfy....
Kwance yake saman bed din jinyarsa sati biyu muna asibitin Alhmdllh ya warke ba abinda baya yi da hannunsa, Doctor yace ba zai sallamemu yanzu ba sai ya Kara warwarewa,Sosai muke Hira dashi amma Yana min Maganar aurenmu zance Masa ba Ni bace,yayi yayi naki yarda har ya gaji ya kyaleni.
Babu inda muke zuwa daga wanka sai ci mu koshi sai Sallah shi yasa muka Kara wani kyau,haske da kiba,sai sheki mukeyi.
Zaune nake saman bed dina dake room din, farce nake yankewa,Yana kwance Yana aikin karanta magazine lokaci zuwa lokaci Yana satar kallo na,Ban kula ba dake da sabuwar razor nake yanke farcen sai na yanke Hannuna jini ya fito shuu,Ahsh...na furta tare da rike yatsan,da sauri ya kalleni ya tabbatar yankewa nayi,amma bai ce ko sannu ba bare ya mike ya taimaka min, sai ma cewa yayi maganinki kenan ance ki Bari a kaiki a yanke Miki kin wani sa razor ke me kika iya? Murmushi nayi Ina danne yatsan da tissue Ina tuna sanda nake yanke Masa farce lokacin Yana kauyenmu, Haka idan yaji ciwo damuwa nake sai me chemist ya dubashi.
Matsawa Doctor yayi kan ya sallamemu Nigeria zamu tafi,Sam naji bana so mu koma sabo da yanda hankalina ya kwanta kullum muna kusa da juna Babu sauran tunani, Likita ya sallamemu wani Hotel hadadde ya Kama Mana kowa room dinsa daban,baya ko leko ni Nima Haka,Amma abin ya dameni bana sa shi a idona,Abinci kuwa kullum baya yankewa abinda nake so shi nake karba,yau kwanan mu Uku ya kwankwasa min kofa Ina budewa ba zato na ganshi tsaye jikin kofa yayi azabar kyau cikin kana Nan Kaya,kasa dauke idona nayi a kansa shima Ni yake kallo ganin kamar Zan fassara shi sai ya dauke kansa yace ki shirya zamu fita jibi zamu tafi Nigeria Yana Gama fadin Haka ya juya abinsa cikin takunsa na birgewa.
Na fito a wanka kenan wata ta kawo min Kaya kanana hadaddun gaske na mutunci Amma fa na Yan gayu ne sosai,yanda nayi kyau ba a magana nayi rolling Dan gyale,ka rantse balarabiya ce.
Tunda ya shigo Room din Danbature ya kasa dauke idonsa da kallona,baya so na fita da kayan Sunyi min kyau da yawa Amma baya so ya fada min tunda yaga na Gama rainashi Bai Isa Dani ba shi yasa yayi Shuru yace muje kawai.
Ni kaina ganinsa cikin bacin Rai zuciyata ta kasa sukuni bana son ganinsa cikin bacin Rai duk da cewa ban San Dalilin fushin nasa ba, Shopping mall ya kaini iri iri yace nayi tsaraba,Kaya kadan na zaba,da kansa ya zabo min kayan bacci,kana Nan Kaya,,dogayen riguna,Riga da skert ,,inner wears, cosmetics,jelweries,takalma,bags Haka ya kwasar min Kaya kamar hauka, shima ya siyi kalar nasa kadan.
Bayan mun huta washe gari muka sake shiri ya kaini yawo wuri wuri gwanin Sha'awa da birgewa,sai cikin dare muka koma Hotel.
Washe gari ya sake kaini yawo Amma duk abinda mukeyi sai magana ta kama dole mukeyi dashi Sam baya saurarata da wani Hira,Wanda bana Jin dadin hakan ko ba komai na Kara sabawa da shi a Hospital.
Da yamma lis jirginmu ya daga zuwa Nigeria,wani bakin ciki nakeji marar misaltuwa,nasan yanzu ganinsa ma wahala zai min,nafi so mu dawwama tare hawayena na share da sauri Dan kar ma ya kamani.
Cikin dare muka sauka kasa Nigeria Wanda ji nake kamar Ana hura min wuta a zuciyata.
Driver dinsa ne yazo da mota daya ya dauke mu zuwa gida,kowa Yana bacci ba Wanda yasan na dawo,sabo da Ni kadai Driver ya kawo gida,Danbature an wuce dashi guest House dinsa ba gida ya dawo ba sabo da Kar gane mu.
A Daren Nanee kawai ita tasan na dawo,wanka nayi kawai na kwanta baccin gajiya,duk da cewar nayi bacci a jirgi.