← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 50

Sashe 42

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajjo Maman Daddy har yau itama tana gadon asibiti Bata motsi sabo da Haka itama likitoci suna ta faman kula da ita,lauyan Mum Yana wajenta Yana Mata tambayoyi ta yanda zaiji dadin kareta,yayin da lauyan Nanee ma Yana wajenta, Karimatu kuwa sabo da Bata da mutunci masifa tayiwa Lauyan nata har ta fusata shi yace ya fasa yi Mata aiki yayi tafiyarsa.
Lauyan Mum yace Da kika Shiga me yasa aka kamaki da wuka? Sannan yaranki ma sun furta a kotu cewar kina furuncin halaka mijinki me yasa?
Kuka Mum takeyi cike da Nadama tace tabbas na Fadi Haka da dama sannan sunji a waya Ina magana da boka na Amma harga Allah na kasa aikata Masa hakan.

Dama Ni gani nakeyi kudi sune kadai Jin dadin duniya shi yasa nake burin mallakarsu har nayi tunanin kashe Daddy Amma wlh na gwada hakan Amma na kasa,wukar Kuma a kasa na ganta kusa da Daddy na dauka sabo da na rude har mutane suka kamani, Sannan Ni Kishiyata Nanee ita ta fito daga toilet sannan sai ga Karimatu ta ukun ms ta fito ta Bayan labile tana Salati,to Ni an kamani da wuka,Nanee tana toilet mijinmu ma ko kulata bayayi ta Zama Yar aikinsa,Karimatu ta fito a Bayan labile wa zaka ce ita tayi kisa? Dole ace nice tunda Ni aka gani da wuka.

Haka suka dinga maga na da lauya sannan ya tafi,Ice kuwa ko ta kan Mum baya bi Yana bangaren Nanee dinsa Wanda hakan yasa Mum cikin bacin rai Amma tasan laifinta ne babu Wanda zai damu da uwa irinta,sabo da Haka gaba daya ta samu kayan tsafe tsafenta ta tarwatsa su ta zubar da komai ta tuba ga Allah ta daina Shan komai,ta daina Abubuwa Marasa kyau zata gyara rayuwarta,Haka taje wurin bokanta ta Basu makudan kudade kan a karya duk wani tsafin da ta yiwa Daddy da sauransu,dama Imaninsu kudi Nan suka lalata komai,Daddy Yana bacci ya farka yaji jikinsa Fresh kamar an cire Masa nauyi,Nan take hankalinsa ya saitu ya dawo normal,Haka ragowar ma Ice ya bar jikinsa,Dr who kuwa kakarin Amai ya fara yi kafin kace me ya fara sheka uban Amai duk Aman nasa wani baki ne a ciki tare da wasu tarkace sai da ya amayar dasu tas sannan ya dawo garau.
Nanee kuwa burburwa ta fara da Shure Shure karshe bacci ya kwashe ta,Haka Karimatu ma taji canji a jikinta.

Babu Wanda ya gane tsafin Mum ne sai Dr who kadai da yayi aman tarkace a toilet sannan yaji lafiyar jikinsa ta canja Bai San Kuma na me Mum tayi Masa ba wannan amsa sai daga bakinta.
Daddy Yana kwance har yau Bai nuna ya warke ba,muma kuma da muka sani bamu fadawa kowa ba,ko yaushe aka Shiga kotu Yana Jin labarin yanda aka Kare har yau wacce tayi kisan yake so ta fada da kanta Amma har an Shiga kotu sau Uku Babu labari,an kasa gano gaskiya a cikin Matan,Haka bincike har yaran gida da makwafta Amma Babu labari,Daddy ya yanke Hukuncin Shiga kotu na hudu zai halicci zaman yasan wacce tayi hakan zata ganshi taji tsoro ta bayyana kanta.

Danbaturena duk ya Shiga damuwa sabo da ba hutu ba Zama kullum suna kan case din,sai wahala yake akan Nanee ganin itace baiwar Allah, Karimatu kuwa Bata ma da me kareta kawai tambayoyi take Shiga ana Mata tana amsawa,an kwashe fin wata guda Ana tafka Sharia Amma ba labari.
Gone ne za a Shiga kotu na hudu ko wanne bangare a shirye suke.

Ni kuwa tunda Sharia tayi karfi Danbature baya Zama ko kwana baya yi a gida daga asibiti wurin Hajjo da Daddy sai wajen lauyoyi kullum a gurguje yake zuwa yaci abinci da wanka ya fita Haka Ina kwantar Masa da hankali ganin ya tashi hankalinsa da yawa tsoro kawai yake ji Kar ace Mum dinsa ce ko Nanee,ga fargabar Daddy Kar ya mutu,Dr who da sauran kannensu da Mata da maza Sam family din ba kwanciyar hankali,Mum ta rame ta canja kamanni,duk wanka da kwalliya Babu an daina a birkice take Bata da aiki sai kuka da tuba ga Allah, ga yaranta kaf ba Wanda yake ko sauraronta,Karimatu kuwa duk Wanda ya ganta zai rantse Yar aikin gidan ce yanda ta lalace ta fita a hayyacinta,sabo da son Kai kaf danginta da suka rage a gidan cewa tayi su tafi garinsu su zauna kafin a Gama case din aga abinda Hali zaiyi sai su dawo su Kam suka ce wlh baza su tafi ba,ai butulci ne, sun taso tun suna Yara an rikesu da amana Amma suyiwa Daddy Haka suna Nan a gidan Dole dasu za a Fara a Gama suna Nan daram musamman Saddiqa itace tafi zakewa tayiwa Karimatu rashin kunya karshe ma ta kwashe kayanta daga part din ta koma part din Nanee me gaskiya.

Yau kotu ta cika makil kowa dake family ya halacci wajen,yaune Kuma Danbature yace nazo kotu Nima yau zai bayyana aurenmu ya tanadi shedunsa duk da Bai fada min Shirin nasa ba nasan Dole da Yan uwa na zasu zo,ta wani bangaren Kuma Ina murna sosai wani bangaren Kuma tsoro nake ji kawai, kowa ya hallara Naga Aliyu yazo kusa Dani ya zauna Yan gidansu sai kallonmu suke da mamaki wasu suna kus kus.

Alkali ya shigo ya zauna tare da gabatar da sharia lauyoyi suka dinga tambayoyinsu Ana Basu amsa karshe kowa kansa ya kulle an rasa Wanda yayi laifin cikin Matan,Alkali yace to yau rantsuwa za ayi kawai,cikin kowacce ya duri ruwa za a rantse da Qurani, Daddy ne ya shigo cikin Shiga ta alfarma security suna take Masa baya,mamaki da murna ta kama yaransa Mata da maza har matayen nasa,Ni da Saddiqa ne kawai bamuyi mamaki ba Tunda mun San ya warke tuntuni.

Alkali yace Alhmdllh ga megidan ya samu lafiya shi zai warware komai,Nan take Daddy ya tsaya a cikin inda ake tsayawa a koti idan za ayi maka tambayoyi, ya fara magana da cewar yau na godewa Allah da ya bani lfy, wannan duk matana ne,Alkali yace muna jinka Alhaji yiwa kotu bayanin komai.

Daddy ya kalli matansa da yaransa Dana Yan uwa ya bada tarihinsa kaf da sannan yace duk cikin matana kowacce nasan halayenta,nasan me nakeyi wani abun kawai Shuru nakeyi Amma tunaninsu ban ma San me nakeyi ba kawai Business ya min yawa, bance bani da laifi ba Ina da laifi Nima Suma suna da nasu.
Karimatu kece uwar gida Amma nasan halinki na masifa da iya tuggu tare da rashin Imani ga sata da kike min nasan ki ba tun yau ba Amma duk munanan halinki nasan baza ki iya yunkurin kashe ni ba,sabo da kina Sona matatace tun saurayi da Budurwa shedan kika biyewa kudi da Jin Dadi yasa kika canja halayenki sabo da son duniya.

Asiya damo sarkin hakuri,na aikata kuskure na kin Baki hakkinki da Allah ya gindaya Mana,na zalunce ki da yawa Kuma kinyi hakuri da halina kin jure tsawon shekaru,halayenki masu kyau ne Asiya Ni kaina ban San ya akayi nayi Miki hakan ba ban sani ba sai yanzu na gane kurena,kiyi hakuri ki yafe min duk abubuwan Dana yi Miki Ni kaina bada sani na ba, ban San nayiba Wanda bazai wuce sharrin sihiri ba na Maryam Amaryata.
Kuka Nanee takeyi tare da durkushewa a wajen tana kuka wiwi,Daddy yace nayi mamakinki Asiya da kece kika iya zuwa kaina da wuka kika shammaceni na fara bacci kika caka min,nayi mamaki na Baki lokaci Naga kalar imaninki Zaki iya fadar gaskiya Amma sai kika so kanki kika kasa fada sai kike karya ma harda yiwa Maryam sharri cewar itace sabo da Ana kallon Maryam itace Bata gari ba.

Banga laifinki ba bakin cikin Dana cusa Miki ne kin Dade kina Tarawa a ranki dama ance duk me hakuri idan ya tashi daukan mataki to bana Wasa yakeyi ba,laifi nane Asiya shi yasa,me girma me Sharia Asiya itace tayi yunkurin kasheni lokacin taje wajena na koreta cikin zagi da cin mutunci Wanda a ranar na wulankatata da yawa wuka kawai ta dakko a kitchen bacci ya fara Daukana ta caka min a gefen cikina,Wanda lokacin Maryam ta taho zata zo wajena kenan sai Asiya ta shige toilet.

Maryam tana zuwa ta rude tana kuka ta dauki wukar a hannunta tun Ina ganewa har na sume a wajen,lokacin Kuma Karimatu itama tazo kenan ta shigo taga abin ya faru shine ta buya a Bayan labile, kaji yanda abin ya faru,Amma sai Asiya ta kasa fada tace Mum ce sabo da wukar a hannunta take,Baki kyauta ba Asiya kin bani mamaki Amma nayi Miki Uzuri kuma na yafe Miki sabo da laifi nane.
Na dawo gareki Maryam Ina da labarinki kaf kece shaye shaye,tsafe tsafe.da sauri Maryam tace Zanyi bayani wlh Zan tonawa kaina asiri cewar Mum tana kuka.
Da farko ina Rokon gafararka Daddyn Yara wlh da bansan rayuwa ba sai yanzu kasancewar karancin ilmin addinin musulunci da ban samu ba a kasar mu,sannan da sharrin shedan ya Sa tunda na taso Ina shaye shaye na kasa dainawa,kuma a Haka kake so na ka aureni,sabo da kudi na aureka Amma sai daga baya na gane Ina sonka tsakani da Allah,lokacin Dana ke harkar tsafe tsafe nayi tunanin kasheka tun da dadewa sai Zan aikata sai na fasa naji bazan iya kashe ka ba Wanda burina kenan Amma ban iya ba,sai dai kawai tsafin da nake maka Wanda nice nasa ka tsani Asiya sannan ka rage son Karimatu sai Ni kadai sai abinda nake so kakeyi,sannan bana kaunar talaka da talauci duk yaran Dana Haifa sun sani musamman Aliyu,nayi maka tsafin da ka mallakamin duk takardun abinda ka mallaka,sannan nasan na fara harkar neman mazan banza Yara kana na masu kwadayin kudi Ina Basu suna biya min bukatata sabo da Kai Sam baka Zama kullum kana yawace yawacen Business Kuma baka tafiya da matanka,baka da lokacin bamu hakkin aure yanda ya Dace shi ya jawo na fara Haka sabo da Ina da karfin Sha'awa, Amma ban Dade ba na daina tun da dadewa ya rage daga shaye shaye sai tsafi,har ta Kai Aliyu ya San komai yace zai tona min asiri ya fada maka.
Chapter 42 · 0% Book details