← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 50

Sashe 17

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dago da kansa yayi ya kalli Nanee yayi Murmushi kadan yace da shagwaba Nanee pls Mana,ba shiri na kwala ihu nace Yeee wlh Allah Danbature nane,na rantse da Allah shine Mijina,na dira tsalle na dirga a gabansa na tareshi na tallafi kumatunsa da tafin Hannuna na saita fuska ta a tasa na tsura Masa Ido na sakeshi naja baya farin ciki ya mamayeni,nace Nanee wlh na San wannan Mijina ne Aliyu sunansa tun Yana mahaukacinsa,sanda yayi Ciwon hauka aka daura Mana aure a kauyenmu mun kwashe wata 9 muna tare Allah shine.

Nanee tace ke...ta daka min tsawa Ashe Baki da hankali?yaushe wannan ya taba Ciwon hauka wlh na rantse Miki Bai taba barin gida ba ta sanadiyyar hauka ba face kasar waje da yake Dan zuwa,tabbas sunansa Aliyu Hydar Amma bamu sanshi da Ciwon hauka ba,sai wani kika sani,wannan Bai taba aure ba.

Dr who yace na Dade Ina zargin ke mara hankali ce a cikin masu hankali wlh tun sanda kike min magana ta window yau na tabbatar Baki da hankali wannan Zaki ce ya aureki Dan son Abin duniya,ihun danayi yasa Yan Mata da samarin gidan dake kusa shigowa inda muke sai ji nayi hhhhh sun kece min da dariya sunce anga kyau da kudi za ace mijinki ne ta Ina? Lallai Yar Nan Makira ce,oh wato anga banza ko? Naja Cilla tace mun San mutan kauye da wayo muma daga can muke,dariya ake ta yi min shi Kuma Wanda nace Danbature ya daskare a tsaye Rai bace ji yake kamar ya kashe Ni sabo da haushin na taba Masa fuska ya tsani mace ta rabe shi.
Idonsa yayi jajir Nan take ,Murmushin takaici yayi dimple dinsa ya lotsa nace Yeee...gashi ..gashi...billahillazi la ila ha Illa huwa Danbature nane,ka tuna ta kauyen Dingawa can Gombe wacce ka Mara lokacin hankalinka ya dawo jikinka kayi tafiyarka bayan ka min duka? Galala ya tsaya Yana kallona,na washe Baki nace pls ka tuna time din wani me machine ya kaika birnin Gombe motoci da sojoji suka daukeka?

Mamaki ya kamashi ya harde hannayensa a kirji Yana kallona shifa Bai San komai ba,nace akwai ma zobe da agogonka suna wajena Amma na barshi gidan Attine watarana Zan dakko na nuna ma wlh Allah kaine,Kuma wlh Ni matarka ce da igiyarka a kaina uku.
Kowa abin ya daure Masa kai.

Ni kuwa na dage nace gashi gashi komai na gane kaine,kune baku Sani ba Amma wlh yayi Ciwon hauka lokacin da ba Wanda zai iya rabarsa Ni na sanshi na soshi na aureshi na zauna dashi,Nasha wahala wajen iyayena akansa Amma na jure sabo da sonsa da nake wlh badan kudi na soshi ba,lokacin da na soshi ko mahaifiyarsa nasan baza ta rabeshi ba a lokacin Ni kuwa na yarda na soshi....Gau......naji an zuba min mari Ni kike cewa Mahaukaci? Yaushe nayi Ciwon hauka Dan ubanki kika Kuma fada sai na yankaki,kinji na rantse Miki ba Ni bane yar iska ki nemi mijinki mahaukaci, banyi Shuru ba Ina kuka nace wlh kaine,Kuma da kasan ko Ni wace a wajenka wlh baza ka soma daga min ko yatsa ba bare ka mareni,Kuma Kaine Nan Mahaukaci da Aliyu Hydar Sulaiman da Kai aka daura min Aure,mamaki ya kashe su tunaninsu hada sunan kawai nayi sabo da naji sunansu yanzu Zan cucesu.

Dariya suka dinga sheka min Ana ganina mahaukaciya har Nanee,kitchen Danbature Wanda suke cewa Ice Naga ya Shiga ya dauko kwandon tace taliya yace ki tsaya yanzu zamu gane tana da hankali ko a'a?

Kwandon ya Mika min yace ungo na karba yace ebo min ruwa a ciki na gani Wai ta haka zai gane haukata Babba ce ko karama Murmushi sosai na kalleshi sonsa ya Kara ninka na baya nace lokacin da muke soyewa muna Shan love da Kai kana Mahaukaci ai Ni ban ma Haka ba,marina yayi sosai me zanci dake zakice munsha uban love Dan uwarki.

Murmushi nayi nace ku sani Yan gidan Nan wlh Ina da auren Aliyu Hydar Sulaiman Kuma har kwanciyar aure munyi sau daya Banda romancing din juna da muke tun Yana kazaminsa mahaukaci lokacin Bai iya komai na duniya ba.
Dariya aka Kara dauka harda ihu Ice duk tsanar Mata da yayi baya kula kowa yau gashi ance har kwanciyar aure yayi Wai da ita Yar aiki, idonsa jajur yace Ni Virgin ne Dan kan ubanki, nace wlh karya ne ba virgin bane Kai an taba yi ye wullu..plate din tangaran ya dauko zai kwada min, na sheka da gudu Bayan Nanee nace daga fadan gaskiya ta Bayan Nanee ya damko ni na bige plate din ya Fadi ya fashe Ina ihu nabi ta saman kujera ya biyo ni,sabo da tsokana nace Ina gudu da Haki,sau nawa Ina maka wanka tas, kullum sai na maka wanka kana cewa My love Nan Bai fita ba a wanke can,ihun dariya Yan dakin suka Sa,naja Cilla harda tsalle Dan dariya,Nanee tace tunda bakya ji ke dashi ta haura sama tana Naga abin naki tsokana ce.

Har ya kamo rigata na koma bayan Dr who Wanda ke dariya ganin ba Babba a Palon Ina haki nace kasan lokacin gajeren wando ma Ni nake sa maka,Mika daya ya damko Ni ba Wasa sai da na Sha Mari yafi biyar fuskata ta kumbura,ya sameni da wayar charger jikinsa na rawa babu Wanda ya ceceni ya Zane fes sai da ya farfasa min jiki, Ina ta kuka a hakan ma saida da Dr who ya karbeni da kyar.

Yace wlh in kina Wasa ki daina kaf gidan Nan tsoronsa akeyi baya Wasa da kowa zuciyace dashi zai iya halakaki ba ruwansa,yanzu da kike gani ba hucewa yayi ba ki kiyayi haduwarki dashi anjima ko gobe.
Nanee ce ta gasa min jiki tasa aka kaini asibiti duk inda Naga wani ko wata Yan gidan sai su kwashe min da dariya,tsoron Dan Bature ya kamani bama naso ko a hanya na ganshi Amma sabo da sonsa yasa nake labewa na dinga lekensa,abincina ma tunda yasan nice ya daina ci a part din Asiya Nanee,da kyar ta bashi hakuri ta lallabashi ya dawo Yana Dan karba yaci.
Nanee tace karki Kuma zuwa inda yake wlh dukan da zai Miki sai yafi na baya,Haka ban Kuma Bari mun hadu ba tsoronsa nake ji kamar malaikan daukan Rai.

Har na koma makaranta ban ganshi ba,yau Tuesday Bayan na Gama aikina na shirya cikin Riga da skert na lace takalmi da jakata iri daya da mayafin duka peach color lace din blue and peach nayi kyau Amma banyi wata kwalliyar kirki ba,Nanee na sanarwa tace naje driver ya kaini,ganin Yan gidan Basu da mutunci nace a taxi zanje,ta bani kudi tace kin huta jawo min magana,karki manta 12pm Dole kizo kiwa Dana abinci,nace ba damuwa na tafi.

Na makara 8am nake da lecture Amma Yanzu har 8 din tayi,da gudu gudu sauri sauri na fito Haka ta compound na fito, Ice ya fito cikin daukan wanka yayi kyau iya kyau sanye cikin kana Nan Kaya kyau dai ba a fada Yana kamshi,Ina ganinsa tsoro ya kamani na koma na labe Dan kar ya ganni Ashe ya ganni ya tsaya jikin wata dalleliyar motarsa yaki tafiya Nima na gaji gashi Zan makara,na fito Ina lallabawa Zan fice yacewa wani Soja ya dauko Masa Ni,sai ji nayi an sabani a kafada,kuka kawai na fashe dashi Raina ya baci da aurena Kato ya daukeni,nace wlh Ina da aure Bazan yafe ba cin zarafin aurena da akayi,a gabansa aka dire Ni na zube a kasa jikina sai rawa yake nace da aurena wlh kasa za a ci min zarafi,yace oh yanzu ma Zaki ce Ni mijinki ne? Da sauri tsoro yasa nace A'a karya nake Kai ba Mijina bane,kayi hakuri ka yafe min, fuska ba Rahma ya kalleni shekeke yace to a gaban kowa Zaki tonawa kanki asiri kamar yanda kika yi wancen lokacin,kaina a kasa hawayen so Yana zuba nace na yarda Amma don Allah ka Bari na dawo daga makaranta da yamma,mamaki yayi yasan babu Yar aikin dake zuwa makaranta sai yanzu yaji yasan Islamiyar Saturday Sunday ta gidan kawai sukeyi.

Kina Yar aiki har wani schl kike zuwa? Nace ae Mana University ma kuwa Yar jamia ce ni level 2 nake Health education, Minister Ijeoma na taba aiki a gidanta itace take biya min kudin Niclos University me tsada sabo da kyan halina take biya min,Kai ya jinjina naso na bashi dariya harda yabon kaina Wai sabo da kyan halinta ya furta a ransa,sai da ya Gama ji yace to ubanwa ya tambayeki Dalla bace min a gani kafin Raina ya baci na halakaki.

Jikina na rawa na mike da sauri na fice daga gidan Ina godewa Allah Bai min komai ba,da gudu gudu na nake tafiya ina so na Isa titi na hau mota,rantsatsiyar motarsa na gani tana slow a titi driver na jansa ya kame a baya Yana Danna waya,Driver dinsa ya ba Umarni yace tafi ka kwashe min yarinyar can da mota,Driver yayo kaina sosai da mota,na kauce ya bini again na kwashe da gudu ya biyo Ni zai takeni da mota Naga wata waya an zagaye wani garden da ita na Kama wayar na daka tsalle na haure na rufta ciki wayar ta yankeni a kafata sosai jini na fita,ban sani ba a ciki Ashe kusa da miciji Kato na fada ya kafta min Sara a hannuna.
Da gudu na Kara yo tsalle na fito waje ban tsaya ta wani yankan waya ba,ihu na saka kawai nabi titi Ina miciji ya cijeni a kaini asibiti,shi kuwa mugun yayi tafiyar sa,taxi na tare na fada da turanci na fada wa Driver me taxi miciji ya cijeni ya kaini asibiti kawai.

Nan take nacewa Driver sunana Fadila,a gidan Sulaiman Araba Lagos nake aiki,Ina da Aunty na Attine can Ojeota layin Babatunde 14no house, na rubuta Masa number ta Attine data Nanee nace ko da zan mutu ka Kira wannan Number.
Chapter 17 · 0% Book details