← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 50

Sashe 26

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya zare hannunsa a nawa ya mike Ina bacci ban sani ba ya Shiga toilet Yana daga hannun da aka cire bullet da kyar, wanka yayi tare da brush ya Dade kafin ya fito,na farka daga bacci Naga bawan Allah har ya shirya cikin wani Uniform na Hospital sabo an kawo Masa,Sallah yake ramawa,Bayan ya Gama Already an kawo Masa abinci iri iri. Hannunsa da kyar yake motsawa,Wani likita ne yazo da sauri Yana ta fada ya za ayi Ina kallo na Bari yayi Abu da hannun? Idan na sake motsin hannunsa yayi yawa wlh hannun zai lalace aikin da suka yi Masa da naura zai lalace,ko cokali Kar na Bari ya dauka da kansa sai Nan da 3wks.

Nurces ya Kira suka taimaka Masa Bayan an gyara bed din tare da canja komai na bed din zuwa sabo,kwantar dashi sukayi sannan suka bani Magunguna da yanda Zan dinga bashi,sai abinci sukace na fara bashi da Hannuna a baki.
Duk da nasan muna da aure Amma shi Sam Bai sani ba,Kuma Kar ya kalleni wacce ban San darajar aure na ba, muryarsa naji a hankali yace ki bani abinci pls,wannan Dan iskan Mijin naki kike tunani wannan kawai ki shareshi kiyi auren Gaiba,Baki na turo nace ai baiyi Shekara uku da bacewa ba bare nayi auren.
To Ni bani abinci naci ba abinda ya dameni tunda shi ya gudu ina ruwan wani,nasan shine Mijin nawa kawai na dauki abinci na Shiga ciyar dashi a hankali,Ina bashi Yana ta kallo na.

Na ebo a spoon yaki bude bakin,nace ka bude bakin Mana sai ya datse hakoransa spoon din nasa na daki hakoran kadan Ina dariya Allah baka da kirki sai wahala kake bani,da tuni an Gama cinyewa Amma kakiya, sai da ya Gama ci sannan na maida komai na ajiye,ke kinci abincin ne? Ya tambayeni,Kai na girgiza kici Mana sai wata cutar ta kamaki,abinda Raina ke so Johanna ta sake kawo min naci abina,nayi wanka,a toilet na shirya nayi komai na fito Ras Dani da kwalliyata, anan Zaki sa wata doguwar Riga ke ba a Saudiya kike ba?.
Ae tunda ba fita zanyi ba Kuma ga Heater a Nan ko Ina ba sanyi me zansa ?Baki ya tabe yace Wai ke me aure wa ya sani ma ko nine Mijin naki kike ta wahalar da kanki kwakwalwarki Bata ganewa,Dariya ce ta cika min ciki, na danne nace tun yaushe na gane Mijina ko Kama Ashe baku yi ba, tsaki yaja yace Maganar farko da ita sarki yake Amfani da me yasa kika ce nine,ko dai kece me tabin hankalin?

Murmushi nayi kawai nace kasan kayi Ciwon ne?kasan garinmu? Ka tuna wani Abu? Yace to sai Lallai na tuna? da waye yace kice nine mijinki kawai dama Ni kike so da yawa Haka shi yasa kika kasa Jin dadin duniya, fuska na Bata cike da Shagwaba nace ba Kaine ba nace yanzu na gane gaskiya.
Zanyi bincike ne yarinya,to idan ka binciko gidanku zasu yarda da Ni har su Bari mu zauna tare sannan zaka iya Kai yarda da auren? Ina ruwanki Kuma wannan iya kaci naji idan kinmin to na yarda idan Baki min ba na Baki red card.

Murmushi nayi kawai ya gyara kwanciyarsa sosai Yana wani Jin farin ciki a ransa yace kika Ce har wanka kike min, Baki na bude nace bafa Kai ba Mijina Danbature,Ae to naji bani labarin me Dame kikeyi da shi na aure? Sirrin Mijin nawa Zan fada maka? Babu kyau,tsaki yaja tare da duba saman Drower dake kusa dashi ya cillo min wani English novel yace karanta min Ina ji.

Wayata ce tayi Kara Naga Ayman, dagawa nayi tare da sallama nace Ina yini ya aiki,yace lfy Lau ya me jiki,nace Alhmdllh, Danbature yaji Ina waya da Namiji kawai Nan take ya daure fuska ya canja gaba daya,sai da yaji nace Ya Ayman gashi ma tashi fa tuni,da kansa yayi wanka, brush,Sallah,yaci abinci Bari na bashi wayar.
Sai lokacin ya Ware fuska ya karbi waya suka Shiga Hira sosai Ina jinsu suna ta dariya,Ayman ne yace Man wannan yarinyar taka fa ta takura min Meena pls talk to her, Uhm..oh Meena Wai dama tana kiranka? Ae Mana, hankalina ne ya tashi kishi ya kamani, kamar na fashe da kuka Haka nake Jin zuciyata,Ashe Yana da Budurwa Meena, Ayman yace kasan tana Masifar sonka idan baza ka aure ta ba, to ka daina kulata online, satar kallona Ice yayi sannan yace Kai ba ruwanka Malam Zan nemeka later.
Yana datse Kiran na mike kamar Zan fashe na fisge wayata a Hannunsa nayi waje fuuuuu a fusace.
Rasa Dalilin fushina yayi kawai yasha maganinsa ya kwanta bacci ya kwashe shi.
Ina can wajen masallaci Ina goge hawayena kadan yayin da turawa ke zirga zirga abinsu.
Zaga Hospital din nayi part part sannan na fita daga asibitin na Dan kalli gari a iya kusa da Hospital din sannan na koma ciki na Samu Yana baccinsa hankali kwance.
Tunani nakeyi Taya za ayi ya ganeni Ina da aurensa idan bazai so ni ba ya sakeni kawai na huta da masifar dake damuna.

Anty Maryam Kiran wayar Aliyu take ba yankewa Amma Sam Bata Shiga,ta rude har frnds dinsa data sani duk ta neme su Basu sani ba,Ni kuwa Nanee na Kira na sanarwa cewar ba Yanzu Zan dawo ba ta Kara hakuri,tace ya Naga number waje? Gabana ya Fadi nace yayana ne Gomnati ta fitar dashi waje ayi Masa magani shine aka ce Ni zanyi jinyarsa sabo da Ina Jin turanci, Nanee ta tausaya Masa kwarai tace kiyi Masa sannu Allah ya bashi lfy nace Ameen.

Murna nayi sosai sannan na Kira Nanee nace Aliyu ka canja murya a matsayin yayana dake jinya a turai ka tsara min Nanee Kar ta kureni, Nanee tana daga waya nace Ga Yayan nawa marar lafiya ku gaisa,Aliyu ya karba ya canja murya wata iri suka gaisa tayi Masa sannu ya amsa sannan ya Miko min wayar na kashe,muka tuntsire da dariya nace wannan Muryar kamar ta Mugyambo Dan India.

Nanee Kam da Aliyu kuwa Bata damu ba sabo da tasan Halinsa idan yayi tafiya ba kowa yake sanarwa ba sannan idan ya tafi wani waje baya fadawa kowa Sam.
Attine ma na kirata nace mun tafi Garin su Nanee.na tsarata itama ta hau.
Aliyu kuwa Daddy ya Kira suka gaisa tare da Hira sannan yace yaje wani Business ne turai,zuwa nayi Yana bacci na dauke wayar na boyeta yanda bazai sake ganinsa bare Anty tace ya dawo ta tsafe shi.

Karimatu ce tsaye tana Kai kawo a palonta,Shehu niga me Maganar Mata Yana zaune Yana kallonta,Baki ya tabe yace Kya yi Kya Gama Haka kawai ki tashi kanki tsaye,Ni Kinga nayi Nan.
Karimatu tunani take a ranta tace to Dan iskan yaron Nan wacce kasar ya tafi shegen yaro kamar me aljanu Wanda suke fada Masa za a Masa wani Abu.
Ni kaina Fadila wayata ma kasheta nayi na boye ba Wanda zai Kira ya sameni dama layikan ba yi zasuyi ba,Amma sabo da tsaro sai sim sabo da Ayman ya Sa min a sabuwar waya dashi muke Amfani muna karyarmu iri iri..
Anty Maryam ta karbi Number ta wurin Nanee irin Wai zata Kira taji ayi tracking ina nake bugun duniya taji duf duf.

Danbaturena Hankalinsa kwance yake baccinsa,Amma abin ya bani tsoro bacci yaki karewa na tasheshi yaki tashi sai bacci yakeyi,Doctor na kira na sanar Masa zai Kai 12hrs yana bacci,da kansu suka duba shi,su kansu abin ya Basu tsoro,ba shiri suka sakashi cikin Wata na'ura,Ni Ina waje zuciyata cike da tsoro, cikin na'ura ya farka a firgice Yana Kiran sunana Fadila.
Bayan an fito dashi sun dawo dashi dakin da muke da,kallon room din yayi sosai yaci gaba da Kiran sunana,Nace ka ganni Nan gani,a hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan yace na tunaki Fadilan kauye,na tuna lokacin danayi ciwo Wanda kwakwalwata Bata iya tuna komai sai Abu kadan kadan wlh da gaske na tuna komai baya lokacin.

Amma abin mamaki mahaukacin gaske idan ya warke baya iya tunawa Amma gashi Ni na San komai,Na tuna ma sanda Yan uwanki suka min duka,lokacin da kike bani abinci,sanda kika fito Ana ruwa taimakona na tuna.
Farin ciki ji nake kamar na sheka lahira Dan murna Danbature ya ganeni ya gane komai tabbas, a fili Kuma sai na canja fuska nayi galala Ina kallonsa,yace Mene ne? Nace to Ni ai ban Sanka ba yaushe wasu yayyena suka dukeka,na baka abinci yaushe? Wanne kauye?,Ni ai ba a kauye nake ba,ban taba rayuwa a kauye ba Ni ba sam.

Kece Nan wlh Fadila Ni Zaki rainawa hankali nine fa Danbaturenki fa,ki tuna Mana gidan da rayuwarmu lokacin kina Sona kina Jin tausayina kika taimakeni kika so ni lokacin da Babu Wanda zai iya saurarata,na tuna tun sanda na bar gida da lokacin da nayi ta garari har nazo kauyenku Fadila Sai na Baki lbr pls? Hmm nifa Malam ban Sanka ba na fada ma gizo nayi maka ba Ni bace,Mikewa tsaye yayi a fusace ransa ya baci ya Yana fada min gaskiyarsa Ina karyata shi,kece Nan Fadila ya fada da karaji,nine Wanda kike so,kike kuka a kaina yanzu na gane I'm all urs,Ina Sam na nuna ban sanshi ba,nace nifa matar wani ce ba Kai ba.
Masifa ya Shiga yi iri iri nidai nace ba shi bane,Toilet ya Shiga ya barni a Nan a fusace.
Wanka da brush ya sake kana ya daura alwala ya fito ko kallona baiyi ba ya fara Sallarsa.
Chapter 26 · 0% Book details