← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 50

Sashe 2

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salman dai Hannuna yaja Ni Kuma na daura faranti gyada ta a kaina na bishi muka fita tare, har bakin titi ya rakani muna hirarmu ya tsaya wajen masu soya doya da kwai tare da egg in to egg ya siya min na dari biyu harda lemon kwalba mirinda da ruwa pure water guda biyu ya bani a Leda sai ga Mahmood Dan Kawu Salisu suka rakani har schl sannan suka tafi zasuyi Shirin zuwa filin ball dake kauyen.

Naje schl Ina tunanin rayuwata ko karatun yanzu na daina fahimta burina na siyar da gyadar dana zo da ita schl Kar na koma gida Naci duka wajen Hajiyarmu.
Haka na dinga zaga class dake makarantun kauye ne na Gomnati ba damuwa akayi da ilmin ba Babu ruwansu.

Ajin Yara na Shiga lokacin anyi break Ina so su siye min gyada ta,na fara musu wayo kasancewarsu Yan primary, wani bench na Yara na Samu duk sun fito da kudinsu zasu fita break na zauna saman desk na washe musu Baki nace Yan Yara Yara gyada me sihiri Ina tafi dama sun San wakar sai ko suka fara Baki daya ajin Ana tafi Ina bawa Yara guda biyu,suna ci nace duk Wanda ya siyi gyadar Nan zan bashi alawa me dadi,Nan Yara suka dinga turuwar siyan gyada da alawata a jaka Ina Basu daya daya,suna siya,kafin kace me sai ga wasu yaran ma na wani ajin muna rera waka,watarana ma idan na faki idon yaro kawai sai na kwace kudinsa na bashi gyada ta kudinsa Dole ya hakura yaci,Dan da Nan na siyar da gyada tas.

Wurin Magrib muka tashi daga schl sai gida,Ina dawowa ranar Girkin Hajiyar mu ne Haka tace yawwa maza je ki karasa min girkin can,Haka ba hutu na Karasa na Gama tuwon shinkafa miyar Danyar kubewa da kifinta dake gidanmu ba laifi muna cin me kyau,Kuma gidan mu ba na kasa bane na bulon siminti ne ko Ina a shafe sumul yasha fenti.

Ina gamawa zanyi wanka kenan na huta Anty ta Miko min katon botiki tace tuzuruwa ebo min ruwa a tuka tuka na waje,tsakanin uwa da danta sai Allah Hajiyarmu karaf a kunnenta fuuuuu sai gata ta fito ta kwace bokitin a Hannuna tayi ball dashi Nan take ya fashe,sai ga Abbu ya shigo daga masallaci,ganin Anty Amarya aka yiwa laifi ya fara masifa kamar zai cire bakinsa sannan ya kalleni tare da cewa zo ki tafi makarantar dare Dan ubanki mene amfaninki,ya kawo min duka Hajiyarmu ta Kare ya sameta a hannu, Hajiya ta kwalla ihu da uban karfi Wanda ya dawo da hankalin makwafta gidanmu,hannu aka ta Dora tana an tsaneni an tsani yarana,sai ka kasheni ka huta,azzalumi tunaninku ban son yarana,Anty tuni Sumi Sumi ta koma dakinta tayi luf tabar Hajiyarmu da babatu mutane suka cika gidan Ana kallon Hajiyarmu a Masifaffiya marar ilmi Ana ganin ita ce ke zaluntar Anty sai zaginta akeyi ita kuma tana ta faman hayaki da masifa.

Kunya tasa gaba dayanmu muka bar gidan sai dare wurin 10pm muka fara dawowa mu kullum gidanmu ba zaman lfy.
Da Sassafe Abbu yace na fito ya aikeni na siyo Masa petrol,Salman yace tana mace Abbu ka bani Ni na siyo ko Musa duk ga Yara sai Fadila zaka aika,Abbu wata Harara ya watsawa salman Wanda yasa Salman yin shuru ba shiri, ita nayi niyyar aike idan ta gaji ta fito da miji tayi aure., Kudin kawai na karba da jarka na tafi naje na dawo sannan nayi Shirin schl.

Abin takaici an fara registration na waec da Neco Amma da na sanarwa Abbu sai yace karatun ya mace bashi da Amfani a duniya Fadila nasan baza ki taba ci gaba a rayuwa ba,baza ki wuce kauyen Nan ba ko aure zakiyi to mene amfanin biya Miki makudan kudi haka,Dana biyawa mace taci gaba da karatu gwara na zubar da kudin,mene amfanin karatun boko wajen ya mace, Hawaye na fara ,sanyi,iska etc Dana Sha a banza bazan karbi certificate ba,ko bazan ci gaba ba ai na karbi Certificate a Hannuna.
Da kuka na fito daga dakin Abbu,Hajiyarmu tasan me ya faru Baki ta tabe duk ke kika jawa kanki da kinyi aure ai da kin huta, Ina Hawaye tare da rakubewa a jikin bangon dakina kamar almajira nace Hajiyarmu Wai komai ba Allah ne yake tsarawa Dan Adam ba Amma kamar baku San hakan ba,ai aure lokaci ne komai dadewa idan da Rai zanyi, rufe mana Baki ai Baki niyya ba komai sai da niyya yake tabbata kiyi niyya ki gani idan bakiyi ba ehe cewar Anty tsokana,Mahmood ne ya shigo gidan wurin Mahmood ya Iskeni Ina kuka,Kanwata me akayi miki? Nace Abbu ne yace bazai biya min Waec ba,Kuma naje wajen kawun Salisu da Kawu Usman sunce baza suyi asarar kudi ba Wai aure ne kadai idan zanyi zasu kashe min kudi Amma boko ai zunubi zasu kwasa ma, dariya Mahmood yayi Dan an biya boko mace tayi shine za a kwashi zunubi, lallashina yayi sannan yace Zamu biya Miki Ni da Salman dasu Musa ki daina kuka,Nan take farin ciki ya mamayeni.

Washe gari kuwa da safe Salman da Mahmood suka je suka biya min Waec da Neco, zo kuga murna Ina ta gode musu, Salman Yana dariya yace ki Bari yarinya Allah yasa muyi kudi Zaki ji dadi,nace Allah yayana?yace sosai ma,to Allah ya hore suka ce Ameen sannan suka tafi daga schl din.

Koda Abbu yaji cewar an biya min kudin jarabawa sai ya dinga fada,da sauri ya shugo yace Ina Fadila,nasan halinsa da gudu na fito nasan halinsa yanzu na Sha Mari,yace naji kinje kin Sa an biya Miki jarabawa ko? Wato Ni ban Isa ba,kin shahara to wlh sai dai ayi asarar kudin Amma Baki Isa kin zana jarabawa ba,ni Zaki tozarta,to zanga me iko dake tsakanin Salman Dani,daga yau na soke zuwa makarantar taki har Islamiyya, Wai ke sai kin ci da biro ko? Ai naji me kike cewa a garin sai kinci da biro,Rokon Abbu na fara Ina kuka,Abbu yace Abu daya zakiyi na kyaleki ki zana jarabawa,da sauri nace me zanyi Abbu? Aure ya bani amsa na gaji da gorin da ake min gari,da maganganu da ake Akan zuriyata,wlh kika sake sunana ya baci wlh kinji na rantse sai na koreki daga Gidana,Anty zaraf ta leko tace wlh kuwa yo yarinya ta Gama balaga a gida,ace kamar Fadila ta fara haila a gida,ga nonuwa kamar me shayarwa Allah yasa ma ba maza bane suka jawosu ta karfi sai wukil ta koma daki, Hajiyarmu wacce ke wanke wanke a bakin rijiya ta mike ta fara surfawa Anty masifa iri iri,Abbu ya zazzageta Wai Bata da hakuri ai fada Anty tayi min.

Haka Abbu ya fice fuuu,Salman Yana dawowa yaga yanda idona ya kumbura sabo da kukan Dana ci,me ya sameki Fadila,labari na bashi yaji haushin Abbu Amma sai ya min Nasiha yace nayi biyayya Allah Yana kallo.

Washe gari Ina kwance a dakina Ina tunani Ina hawayen dan ban San Ina yi ba,ganin kuka bazai Kare ba kawai nayi Alwala nayi Nafeela tare da Kai kuka na wajen Allah,karshe Nace Allah ka bani Mijin aure ko wanne iri ne Allah ko Mahaukaci ne zan aureshi haka.

Anan nake Jan hankalin Yan uwa Da yawa Ana samu idan mutum Allah yasa Bai yi aure da wuri ba ko mace ko Namiji sai dangi da mutane su takura Masa,Ana gulma Ana aibata wasu ko ace ma fasikanci sukeyi,a garin haka sai mutum yaje ya zabowa kansa wahala ya aura,zaka ji da yawa hakan na faruwa Mata suna Allah ka bani Miji ko wanne irine aura zanyi Haka sabo da halin da suke Shiga wajen iyaye,Yan uwa,kawaye da mutan gari.
Ana nunawa mutum shine yaki yi Ana mantawa da Allah.

Bayan wata daya Cikin Yan uwanmu wata ta haihu yau Suna shiryawa nayi naci kwalliya ta kamar Yar birni dama gani da uban kyau kamar asace Ni,Hajiyarmu ce ta takura min ita baza taje ba sai Ni na wakilceta Kuma na zaga danginta Dana Abbu, Haka na fito na iske samarin gidanmu tare dasu Mahmood a majalisarsu suna ta tsokanata nayi kyau daddawar daki yau ta fito,dariya na danyi na wuce na tafi,Ina sallama a gidan mutane damkam Ana ta cin abinci tun kafin na Shiga aka fara gulmata Ana kus kus, Abin haushin dangina Yan uwa dasu ake zagina,tunda na Shiga wasu da gayya suke min habaici,wasu Kuma su fake da Wasa,da kyar nayi 10mnt na bar gidan, na fara zaga dangin Abbu duk inda na Shiga sai na fito Ina goge guntun Hawaye,Haka dangin Hajiyarmu ba hadin Kai Sam.

Gidan kakannina na wajen uwa ma suka sani a daki ta inda suke Shiga ba tanan suke fita ba,kakannina Yafendo da Baffalo sune naje na karshe,Yafendo tana gani na tace oh yau kece a garin,gashi Nan duk kin tsufa a gida,yanzu Yar Nan baza kiwa kanki fada ba? Wlh Nan da wata Uku idan Baki fito da miji ba to ko da ubanwa daura Miki za ayi.nan suka Karaci surutunsu na taso na bar musu gidan Yafendo tace Yar bantan uba me kafa kamar tabarya.

Bayan wata daya Ina wannan Hali da yamma na fita tallan Goro na dawo Ina kan hanyata ta komawa gida katsam naga mutane damkam a kusa da gidanmu Yara da manya ka rantse masallacin idi ne Mata da maza har da masu leke ta cikin gida Mata saman katanga, Wani Almajiri na tambaya me ake kallo me ya ta faru,Almajiri ya washe jajayen hakoransa yace Bature ne yazo Amma kamar mahaukacine fa an kasa ganewa Yana da hankali ko babu, Baki ganshi ba Dan gayu Dan birni Baki ganshi ba je ki gani.

Jin ance bature ne nace Nima baza a barni a baya ba,Haka na kutsa cikin mutanen har na Shiga inda baturen yake, sai da na kusa Suma sabo da cikar zatinsa da haibarsa ban taba ganin me kyau Haka ba,ai sai na ganni na dawo baka a kansa,kyau kuwa kamar shi yayiwa kansa sai ka lalace wajen kallon wannan bawan Allah sai wani kamshi yakeyi,Shadda ce fara Kar a jikinsa me tsadar gaske tana sheki,sai dai ta danyi dirty kadan,Kuma gefenta ya Dan yage kamar ma kusa ce ta yaga wajen bana mutuwa bane.
Chapter 2 · 0% Book details